“A dā ni ɗan caca ne sosai. Na yi addu’a don in ci caca, amma ban taɓa yin nasara ba.”—Samuel, * daga ƙasar Kenya.

“Sa’ad da muke addu’a a makaranta, muna maimaita addu’ar da muka haddace ne.”—Teresa, daga ƙasar Filifin.

“Ina addu’a sa’ad da nake fuskantar matsaloli. Ina roƙo don a gafarta zunubaina kuma in zama Kirista na ƙwarai.”—Magdalene, daga ƙasar Gana.

Abin da Samuel da Teresa da kuma Magdalene suka ce ya nuna cewa akwai dalilai da yawa da ke sa mutane yin addu’a. Wasu dalilan sun dace, wasu kuma ba su dace ba. Wasu mutane suna yin addu’a da zuciya ɗaya, wasu kuma suna yi ne kawai amma, miliyoyin mutane sun san amfanin yin addu’a. Wasu suna yin hakan ne don su ci jarrabawa ko don kulob ɗinsu ya ci gāsa ko don Allah ya kāre iyalinsu ko kuma don wasu dalilai. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa har mutanen da ba su da addini ma suna yin addu’a a kai a kai.

Kana yin addu’a kuwa? Idan haka ne, me kake roƙa? Ko da kana yin addu’a ko a’a, za ka iya ce: ‘Yin addu’a yana da wani amfani kuwa? Akwai wani da ke jin addu’o’ina kuwa?’ Wani marubuci ya ce yin addu’a tana kamar “shan magani ne kawai.” Wasu likitoci ma suna da wannan ra’ayin, sun ce addu’a abu ne da mutum yake yi idan ba ya so ya sha magani. Shin waɗannan kalaman da aka yi a sama gaskiya ne?

Littafi Mai Tsarki bai ce addu’a abu ne da ake yi idan ba a son shan magani ba. Ya ce akwai mai jin addu’o’in da ake yi a hanyar da ta dace da kuma don dalilai masu kyau. Shin hakan gaskiya ne? Bari mu tattauna gaskiyar wannan batun.

^ sakin layi na 3 An canja wasu sunaye.