Sunan wani fim mai ban tsoro da aka yi kwanan nan shi ne Antichrist (Magabcin Kristi).

Wani rukunin mawaƙa sun kira wani sabon albam ɗinsu Antichrist Superstar (Tauraron Magabtan Kristi).

Wani ɗan ilimin falsafa a ƙarni na 19 mai suna Friedrich Nietzsche ya kira wani littafin da ya rubuta Antichrist (Magabcin Kristi).

A zamanin dā, sarakuna suna yawan kiran abokan hamayyarsu da wannan sunan.

Wani Sarkin ƙasar Jamus mai suna Martin Luther, ya kira fafaroma magabcin Kristi.

TUN da an daɗe ana kiran shugabanni da fina-finai da wannan sunan, ya dace a yi waɗannan tambayoyin: Wane ne magabcin Kristi? Shin wannan sunan ya shafe mu ne a yau? Hakika, wurin da zai fi dacewa mu soma bincikenmu game da magabcin Kristi shi ne a cikin Littafi Mai Tsarki domin a cikinsa ne sunan ya bayyana sau biyar.

AN FALLASA MAGABCIN KRISTI

Yohanna ne kaɗai marubucin Littafi Mai Tsarki da ya yi amfani da wannan furucin. Yaya ya kwatanta wannan magabcin Kristi? Ka lura da abin da Yohanna ya faɗa a littafi na farko da ya rubuta. Ya ce: ‘’Ya’ya ƙanƙanana, sa’a ta ƙarshe ke nan: kamar yadda kuka ji magabcin Kristi yana zuwa, ko yanzu magabtan Kristi da yawa sun taso; saboda wannan mun sani sa’a ta ƙarshe ke nan. Sun fita daga cikinmu, amma ba na cikinmu ba ne . . . Wane ne maƙaryaci sai wanda yana mūsun Yesu shi ne Kristi? Magabcin Kristi ke nan, shi wanda yake mūsun Uban da Ɗan.’—1 Yohanna 2:18, 19, 22.

Manzo Yohanna ya fahimci cewa magabtan Kristi su ne dukan waɗanda suke yaɗa ƙarya da gangan game da Yesu Kristi da kuma koyarwarsa

Mene ne ka koya daga wannan furucin? Yohanna ya ambata “magabtan Kristi,” kuma hakan ya nuna cewa magabcin Kristi ba mutum ɗaya ba, amma rukunin mutane ne. Waɗannan mutanen suna yaɗa ƙarya, ba su yarda cewa Yesu shi ne Kristi ko Almasihu ba kuma ba sa so mutane su san bambanci tsakanin Allah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Magabtan Kristi suna da’awa cewa su Kristi ne ko wakilinsa, amma tun da sun “fita daga cikinmu,” sun bijire daga koyarwar gaskiya ta Littafi Mai Tsarki. Bugu da ƙari, da akwai wannan rukunin a lokacin da Yohanna ya rubuta wasiƙarsa, wato a “sa’a ta ƙarshe,” wataƙila a ƙarshen zamanin manzannin Yesu.

Mene ne kuma Yohanna ya rubuta game da wannan magabcin Kristi? Sa’ad da yake magana game da annabawan ƙarya, ya ce: “Kowane ruhu wanda ya shaida Yesu Kristi ya zo cikin jiki na Allah ne: kowane ruhu wanda ba ya shaida Yesu ba, ba na Allah ba ne: ruhun magabcin Kristi ke nan, wanda kun ji labari yana zuwa; ko yanzu yana nan duniya.” (1 Yohanna 4:2, 3) Yohanna ya sake maimaita wannan batun a wasiƙa ta biyu da ya rubuta: “Masu-ruɗin mutane da yawa sun fita zuwa cikin duniya, wato waɗanda ba su shaida Yesu Kristi ya zo cikin jiki ba. Mai-ruɗewa ke nan da magabcin Kristi.” (2 Yohanna 7) Hakika, Yohanna ya fahimci cewa magabtan Kristi su ne dukan mutanen da ke yaɗa ƙarya game da Yesu Kristi da kuma koyarwarsa.

“MASU-ƘARYAN ANNABCI” DA KUMA “MUTUMIN ZUNUBI”

Yesu ya yi gargaɗi cewa annabawan ƙarya za su zo da ‘fatar tumaki amma daga ciki kerketai ne masu-hauka’

Shekaru da yawa kafin Yohanna ya yi magana game da waɗannan mayaudaran, Yesu Kristi  ya shawarci mabiyansa. Ya ce: “Ku yi hankali da masu-ƙaryan annabci, masu-zuwa wurinku da fatar tumaki, amma daga ciki kerketai ne masu-hauka.” (Matta 7:15) Manzo Bulus ma ya gargaɗi Kiristoci a Tasalonika, ya ce: “Kada ku bari kowane mutum ya ruɗe ku ta ko ƙaƙa: gama wannan rana [ranar Jehobah] ba za ta zo ba sai riddan ta fara zuwa, mutumin zunubi kuma ya bayyanu, ɗan halaka.”—2 Tasalonikawa 2:3.

Saboda haka, a ƙarni na farko, annabawan ƙarya da kuma ’yan ridda sun riga sun bazu a ko’ina, suna neman su gurɓata ikilisiyar Kirista. Dukan mutanen da ke yaɗa ƙarya game da Yesu Kristi da kuma koyarwarsa suna cikin mutanen da Yohanna ya kira “magabcin Kristi.” Manzo Bulus ya faɗi ra’ayin Jehobah game da wannan magabcin sa’ad da ya kira shi “ɗan halaka.”

KA YI HANKALI DA MAGABTAN KRISTI A YAU

Yau kuma fa? Har a yau, mutane da ƙungiyoyin magabtan Kristi suna hamayya da Kristi da kuma koyarwarsa. Suna yaɗa ƙarya kuma suna yaudarar mutane da gangan domin kada su san Uban, wato Jehobah Allah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Ya kamata mu yi hattara da irin waɗannan ƙaryace-ƙaryacen. Bari mu tattauna biyu cikinsu.

’Yan coci sun yi shekaru da yawa suna yaɗa koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, suna da’awa cewa Uban da kuma Ɗan ɗaya ne. Magabcin Kristi ya hana mutane sanin Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mutane su yi koyi da Yesu Kristi kuma su kusaci Allah, amma magabtan Kristi sun hana mutanen kirki yin hakan.—1 Korintiyawa 11:1; Yaƙub 4:8.

’Yan coci sun kuma saka hannu a wannan ɗimaucewar ta wajen sa a yi amfani da juyin Littafi Mai Tsarki da babu sunan Allah , wato Jehobah a ciki. Sun yi hakan duk da cewa sunan Allah ya bayyana wajen sau 7,000 a asalin rubutu na Littafi Mai Tsarki. Mene ne sakamakon haka? Sun daɗa ɓoye sunan Allah na gaskiya.

A wani ɓangare kuma, sanin sunan Allah, wato Jehobah, ya taimaka wa bayin Allah da yawa su kusace shi. Abin da ya faru da wani mai suna Richard ke nan, wanda ya tuna tattaunawar da ya yi da wasu Shaidun Jehobah biyu. Ya ce: “Sun nuna min a cikin Littafi Mai Tsarki cewa sunan Allah, Jehobah ne. Sanin cewa Allah yana da suna ya burge ni sosai, domin abu ne da ban taɓa ji ba.” Tun daga lokacin, Richard ya yi canje-canje a rayuwarsa don halinsa ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ya riƙa faranta wa Jehobah rai. Ya daɗa cewa: “Sanin sunan Allah ya taimaka mini in ƙulla dangantaka da shi.”

Magabtan Kristi sun kwashi shekaru da yawa suna ɓad da mutane a ibadance. Amma yin nazarin Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu san ko wane ne wannan magabcin Kristi kuma mun sami ’yanci daga ƙaryace-ƙaryacen addinai.—Yohanna 17:17.