Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 TARIHI

Abin da Tsara Bakwai na Iyalinmu Suka Gāda

Abin da Tsara Bakwai na Iyalinmu Suka Gāda

Mutane suna yawan cewa na yi kama da babana. Halina da idanuna da kuma fara’ata duk sun yi kama da na shi. Har ila da akwai wani abin da iyalinmu ta gāda daga wurinsa, wato bautar Jehobah. Bari in ba da labarin.

Yadda na koyi wasu abubuwa da muka gāda daga wurin ubana

A ranar 20 ga Janairu, 1815, ne aka haifi kakana Thomas1 * Williams a birnin Horncastle, a ƙasar Ingila. Mahaifiyarsa ta rasu shekaru biyu bayan haihuwarsa, saboda haka, mahaifinsu mai suna John Williams ne ya raine su da sauran ’yan’uwansa uku. Mahaifinsu ya koya wa Thomas aikin kafinta, amma Thomas ya so wata sana’a dabam.

A lokacin, ana ƙarfafa mutane a ƙasar Ingila su koma coci. Wani mai bishara mai suna John Wesley ya fita daga cocin nan Church of England (Cocin Ingila) kuma ya kafa cocin Society of Methodists. Wannan rukunin suna ƙarfafa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma wa’azi. Koyarwar Wesley ta bazu da sauri kamar wutar daji kuma iyalin Williams sun karɓi koyarwar hannu bibbiyu. Thomas ya soma yaɗa koyarwar Wesley kuma ya koma Kudancin Fasifik a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje. A watan Yuli na shekara ta 1840, shi da amaryarsa Mary,2 sun ƙaura zuwa tsibirin * Lakeba a ƙasar Fiji a wani dutse da masu cin naman mutane suke zama.

ZAMA DA MASU CIN NAMAN MUTUNE

Thomas da matarsa sun sha wuya sosai a shekarun farko da suka yi a ƙasar Fiji. Sun yi aiki na sa’o’i da yawa duk da yanayin ƙauyen da kuma zafin rana. Sun fuskanci abubuwa masu ban tsoro da yawa, kamar yaƙi da kisan gwauraye da yara da kuma masu cin naman mutane. Ƙari ga haka, mutanen garin ba sa jin wa’azin da suke yi. Mary da ɗanta na fari sun kusan mutuwa saboda ciwo mai tsanani da suka yi. A shekara ta 1843, Thomas ya rubuta: “Na yi sanyin gwiwa kuma na kasala ba kaɗan ba. . . .” Duk da haka, shi da matarsa sun jimre kuma bangaskiyarsu ga Jehobah Allah ce ta taimake su.

Daga baya, sai Thomas ya yi amfani da sana’arsa ta kafinta don ya gina irin salon gida Turawa a ƙasar Fiji. Wannan shi ne gida na farko a ƙasar Fiji da ke da irin wannan fasalin. Akwai wurin da iska zai riƙa shigowa cikin ɗaki a ƙasan ginin da kuma wasu abubuwa masu kyau da ya ja hankalin mutanen garin. Kafin a gama gina gidan, sai Mary ta haifi ɗanta na biyu mai suna Thomas Whitton3 Williams, wanda ya zama kakana.

A shekara ta 1843, Thomas babba ya taimaka wajen fassara Lingilar Yohanna zuwa harshen Fiji, kuma wannan ba ƙaramin aiki ba ne. * Amma yana da baiwar sanin tarihin mutane don shi mai lura ne sosai. Sai ya rubuta tarihin a littafinsa mai suna Fiji and the Fijians (1858), kuma wannan tarihi ne  na musamman na rayuwar mutanen Fiji a ƙarni na 19.

Thomas ya yi aiki tuƙuru a cikin shekaru 13 da yake ƙasar Fiji kuma hakan ya sa ya soma ciwo, sai shi da iyalinsa suka ƙaura zuwa Ostareliya. Thomas ya rasu a birnin Ballarat, Victoria, a shekara ta 1891 bayan da ya jima yana hidima a matsayin limami.

1Thomas Williams, mai yada wa’azin addinin Wesley (1815-1891)2Mary Williams (1816-1890)3Thomas Whitton Williams (1841-1902)4Phoebe Williams (1850-1926)Majami’ar Mulki, Donnybrook, Ostareliya, 19475Arthur Bakewell Williams (1875-1959) A Indiya6Florence Williams (1911-2003)7Arthur Lindsay Williams (1904-1984)A Tsibirin Salaman8Ronald Williams (1935 har yau)9Geoffrey Williams (1962 har yau)101112Kevin Williams (1986 har yau-)

“ZINARIYA” A YAMMA

A shekara ta 1883 ne Thomas Whitton Williams da matarsa Phoebe, (4) suka ƙaura zuwa birnin Perth, a Yammacin Ostareliya. Ɗansu na biyu mai suna Arthur Bakewell (5) Williams, wanda shi ne kakana, yana ɗan shekara 9 ne a lokacin.

Sa’ad da Arthur yake da shekara 22, sai ya tafi neman arziki a wani birni mai suna Kalgoorlie inda ake tona zinariya wajen mil 370, wato kilomita 600 gabas da birnin Perth. A wurin ne ya karanta wasu littattafan da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka wallafa wato Shaidun Jehobah a yau. Sai ya ce a riƙa aika masa Zion’s Watch Tower, wato Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona. Sa’ad da Arthur ya ji daɗin abin da ya karanta, sai ya soma gaya wa wasu abin da yake koya, yana gudanar da taro don nazarin Littafi Mai Tsarki. Da haka ne aka soma ayyukan Shaidun Jehobah a yammacin ƙasar Ostareliya da yanzu ya bunƙasa.

Arthur ya gaya wa danginsa abin da yake koya. Mahaifinsa ya amince da abin da yake koya daga wurin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki amma ya rasu jim kaɗan bayan haka. Daga baya, mahaifiyarsa Phoebe, da ƙannensa Violet da Mary sun zama Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Violet ta soma hidimar majagaba. Arthur ya ce ita ce “majagaba mafi ƙwazo da aka taɓa samu a Yammacin Ostareliya.” Wataƙila abin da Arthur ya faɗa ba daidai ba ne, duk da haka, ƙwazon Violet ya shafi tsara na gaba sosai.

Daga baya, Arthur ya yi aure kuma ya ƙaura zuwa birnin Donnybrook, da ke kudu maso yammacin Ostareliya. A wurin an ba shi suna “Old Mad 1914!” (Tsohon Mahaukacin 1914) don yadda yake wa’azin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da wannan shekarar. * An daina tsokanarsa sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na Ɗaya. Arthur ya saka littattafanmu a tagar shagonsa inda mutane za su riƙa gani kuma a koyaushe yana yi wa kwastomominsa wa’azi. Ya saka alama a tagarsa cewa zai ba da fam 100 ga duk mutumin da zai iya nuna masa koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma, babu mutumin da ya taɓa yin hakan. Arthur ya tsani wannan koyarwar sosai don ba ta cikin Littafi Mai Tsarki.

An yi amfani da gidan Williams don nazarin Littafi Mai Tsarki na rukuni da kuma taron ikilisiya a birnin Donnybrook. Daga baya, Arthur ya gina Majami’ar Mulki wato inda ake yin taro a birnin, kuma wannan ne ɗaya cikin sabbin wuraren taro da aka gina a Yammacin Ostareliya. Har ma lokacin da ya kai shekaru saba’in da wani abu, yakan saka kwat da taye, sai ya  hau tsohon dokinsa mai suna Doll zuwa wa’azi a wurare masu nisa a birnin Donnybrook.

Arthur shiru-shiru ne kuma yana da hankali sosai, ƙari ga haka, shi mai ƙwazo ne kuma hakan ya shafi yaransa maza biyu da mata biyar. ’Yarsa mai suna Florence6 ta yi hidima a ƙasar Indiya a matsayin mai wa’azi ƙasashen waje. Ɗansa mai suna Lindsay (7) da Thomas sun daɗe suna hidima a matsayin dattawan ikilisiya kamar mahaifinsu.

AFUL MAI SUNA SWEET LADY

Arthur Lindsay Williams, wato kakan-kakana sanannen mutum ne kuma mutane suna ƙaunar sa don halinsa mai kyau. Yana ba da lokacinsa don ya taimaka wa mutane kuma yana daraja su. Ƙari ga haka, ya ƙware a tsare itatuwa kuma a cikin shekaru sha biyu ya zama tauraro a gasa 18 na tsare itatuwa da aka yi.

Amma Arthur bai yi mamaki ba sa’ad da ɗansa Ronald, ɗan shekara biyu8 (kakana), ya je tsaran itacen aful da ke kusa da gidansu. Da mahaifiyarsa ta ga haka, sai ta ɗaure itacen kuma daga baya, itacen ya ba da ’ya’yan masu zaƙi sosai. Sun ba wa itacen suna Lady Williams apple kuma an yi amfani da sabon itacen a matsayin iri. Ƙari ga haka, wannan itacen aful ne aka fi sani a duniya yanzu.

Daga baya, Ronald da nake kiransa Gramp ya yi wasu ayyuka masu muhimmanci sosai. Shi da matarsa sun ba da kai a yin ayyukan gine-gine a ƙasar Ostareliya da kuma Tsibirin Solomon. Yanzu ya kusan shekaru 80, duk da haka, yana hidima a matsayin dattijo a ikilisiya kuma yana taimaka wajen gina da kuma gyare-gyaren Majami’un Mulki a Yammacin Ostareliya.

YADDA NA DARAJA GĀDONA

Da yake iyayena Geoffrey (9) da Janice (10) Williams suna bin misalin kakanninmu, sun yi aiki tuƙuru don su raine ni da ’yar’uwata, Katharine don mu daraja ƙa’idodin Jehobah. Na bi gurbinsu sa’ad da na kai shekara 13. Sa’ad da na halarci wani babban taro, sai wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, mai suna John E. Barr, ya ƙarfafa matasan da suka halarci taron cewa: “Kada ku yi banza da abu mai muhimmanci da kuka samu, wato damar sanin Jehobah da kuma yin ƙaunarsa.” A wannan daren ne na yi baftisma. Na soma hidimar majagaba bayan shekara biyu.

A yau, (12) ina jin daɗin yin wa’azi da matata, Chloe, (11) a birnin Tom Price, da ake haƙa ma’adinai a arewa matso yammacin Ostareliya. Muna aiki na ɗan lokaci don samun abin biyan bukatarmu. Iyayena da ’yar’uwata Katharine da mijinta Andrew, suna hidima a birnin Port Hedland, da ke da nisan mil 260, wato kilomita 420 daga arewacin ƙasar. Ni da mahaifina muna hidima a matsayin dattawa a cikin ikilisiya.

Kakana Thomas Williams wanda shi ne farko a cikin tsara bakwai da suka shige ya tsai da shawarar bauta wa Jehobah Allah. Wannan misali mai kyau na bangaskiya da ibada ya zama gādo da aka bar mana. Ina farin ciki sosai don na gāji bautar Jehobah.

^ sakin layi na 5 Kowace lamba tana nuna mutanen da suke hotunan da ke shafi na 10 da 11.

^ sakin layi na 6 A dā ana kiran wurin Tsibirin Lakemba, kuma yana kusa da gabashin Fiji inda wata ƙabila da ake kira Lau suke da zama.

^ sakin layi na 10 John Hunt mai wa’azi a ƙasashen waje ne ya fassara yawancin littattafan da ke Sabon Alkawari na yaren Fiji, wanda aka wallafa a shekara ta 1847. Fassarar na da kyau don ya yi amfani da sunan Allah, “Jiova,” a littafin Markus 12:36 da Luka 20:42 da kuma Ayyukan Manzanni 2:34.

^ sakin layi na 16 Ka duba ratayen nan mai jigo “1914— Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki” a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa kuma za ka iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha.