Shin Allah zai ƙyale ’yan Adam su ci gaba da mallakar juna kuma su halaka juna? A’a. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, Allah zai ɗau mataki don ya kawo ƙarshen dukan mugunta da kuma nuna ƙarfi da ake yi a wannan zamanin. Mahaliccin mutum da kuma duniya yana so ka san cewa zai ɗauki mataki nan ba da daɗewa ba. Ta yaya yake bayyana wannan batun?

Ka yi la’akari da wannan kwatancin: Idan kana so ka yi tafiya a mota kuma ba ka san hanya ba, babu shakka, za ka iya bincika Intane da taswirori da kuma wasu littattafai don ka san hanyar da za ka bi. Yayin da kake tafiya kuma ka soma ganin kwatancin da ke cikin taswirar, za ka soma gaba gaɗi domin ka san cewa ka kusan kai inda za ka. Hakazalika, Allah ya ba mu Kalmarsa wadda ta bayyana abubuwa na musamman da za su faru a faɗin duniya. Yayin da muke ganin yadda waɗannan abubuwan suke faruwa, muna daɗa gaba gaɗi domin mun san cewa ƙarshen duniya ya kusa.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa abubuwa za su taɓarɓare sosai a duniya kuma hakan zai ci gaba har ƙarshen ya zo. A wannan lokacin, abubuwan da ba su taɓa faruwa ba a duniya za su auku. Ka yi la’akari da wasu cikin waɗannan alamun da aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki.

1. TASHE-TASHEN HANKULA A KO’INA Annabcin da ke littafin Matta sura 24 ya lissafta abubuwan da za su faru a duniya. Waɗannan aukuwar za su zama alamar cikar “zamani” kuma su ne za su sa “ƙarshen ya zo.” (Ayoyi na 3, 14, LMT) Waɗannan alamun sun haɗa da yaƙe-yaƙe da ƙarancin abinci da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam da yaɗuwar mugunta da rashin ƙauna da kuma yaudara daga malaman addinai. (Ayoyi na 6-26) Babu shakka, ba a yau waɗannan abubuwan suka soma faruwa ba, amma yayin da ƙarshen yake kusatowa, waɗannan abubuwan za su faru a kusan lokaci ɗaya. Za su kuma biyo bayan alamu uku da ke gaba.

2. ƊABI’UN MUTANE Littafi Mai Tsarki ya ce ɗabi’ar mutane za ta lalace sosai a “kwanaki na ƙarshe.” Ayar ta ce: “Mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, mafiya son annishuwa da Allah.” (2 Timotawus 3:1-4) Ko da yake ba a yau ’yan Adam suka soma rashin kunya ba, amma a kwanaki na ƙarshe ne irin wannan halin zai yi tsanani sosai har a kira shi “miyagun zamanu.” Ka lura cewa mutane suna da irin wannan mummunar halin kuwa?

3. ANA ƁATA DUNIYA Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai “halaka waɗanda ke” ɓata duniya. (Ru’ya ta Yohanna 11:18) A waɗanne hanyoyi ne ’yan Adam za su ɓata duniya? Ga kuma yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta zamanin Nuhu, ya ce: “Duniya kuwa ta ɓāci a gaban Allah, duniya kuma ta cika da zalunci. Allah ya duba duniya, ga ta kuwa ɓatacciya ce.” Sai Allah ya ce game da wannan lalatacen zamanin: “Zan halaka su.” (Farawa 6:11-13) Shin ka lura cewa duniya ta cika da mugunta yanzu? Ƙari ga haka, ’yan Adam sun kai wani lokaci na musamman a tarihi wato, suna da makaman da za su iya halaka dukan mutane a duniya. Ana kuma ɓata duniya a wata hanya. ’Yan Adam suna gurɓata iskar da muke shaƙa da teku kuma suna ɓata jeji da kuma mazaunin dabbobi.

Ka tambayi kanka, “Sama da shekaru ɗari da  suka shige, da zai yiwu ’yan Adam su halaka juna gaba ɗaya a duniya kuwa?’ A yanzu haka, ’yan Adam suna tattara manya-manyan makamai kuma suna ɓata mahalli da su sosai. Mutane suna samun ci gaba sosai a fagen fasaha amma ba su san illar da hakan yake jawowa ba ko kuma yadda za su magance hakan. Babu wani ɗan Adam da zai iya sanin ko kuma tsara yadda duniya za ta kasance nan gaba. Kafin mutane su gama halaka kansu, Allah zai halaka waɗanda suke ɓata duniya. Alkawarin da ya yi ke nan!

4. WA’AZI A DUKAN DUNIYA Wata alama kuma da za ta nuna cewa ƙarshen duniya ya kusa ita ce wani gagarumin aiki da aka annabta cewa za a yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Matta 24:14, LMT) Wannan wa’azin zai yi dabam da wanda yawancin addinai suka kwashi shekaru da yawa suna yi. Ainihin jigon wa’azin da za a yi a waɗannan kwanaki na ƙarshe shi ne, ‘bishara ta Mulki.’ Shin ka san wani addinin da ke yin wa’azi a kan wannan jigon kuwa? Ko da akwai wasu addinai da ke yin wa’azi a kan wannan jigon, shin sun yaɗa wannan bishara a “ko’ina a duniya domin shaida ga dukan al’ummai” kuwa?

Ana shelar bisharar Mulkin Allah a ɗarurruwan harsuna a faɗin duniya

Yanar gizon nan www.jw.org/ha tana nanata ‘bisharan nan ta Mulki.’ Ana wallafa littattafai da ke bayyana wannan saƙon cikin harsuna sama da 700 a wannan dandalin. Shin ka san wata hanya da mutane suke amfani da ita wajen yaɗa wannan bisharar Mulki ga iyakar duniya da ta kai wannan kuwa? Shekaru da yawa kafin a soma amfani da Intane, an san Shaidun Jehobah da yin ƙwazo sosai wajen yaɗa bishara ta Mulkin Allah. Tun a shekara ta 1939, kowane bangon mujallar Hasumiyar Tsaro tana ɗauke da jigon nan “Mai Shelar Mulkin Jehobah.” Wani littafi da ke magana a kan addinai ya ce “babu addinin da ke yaɗa bishara ga mutane kamar Shaidun Jehobah.” Wannan wa’azin da ake yi yana nanata cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai sa “ƙarshen ya zo.”

LOKACI MAI MUHIMMANCI A TARIHIN ’YAN ADAM

Shin ka lura cewa waɗannan alamu huɗu na Littafi Mai Tsarki da aka ambata a wannan talifin suna cika a zamaninmu? Sama da shekaru ɗari yanzu, wannan mujallar tana yi wa mutane bayani game da abubuwan da suke faruwa a duniya don ta tabbata musu cewa ƙarshen ya  yi kusa. Wasu ba su amince da hakan ba, suna da’awa cewa hakan ra’ayin mutane ne kawai. Ƙari ga haka, suna kuma da’awa cewa tun da sadarwa ta fi sauƙi yanzu kuma labari yana yaɗuwa da sauri, za a iya gani kamar abubuwa sun fi muni yanzu. Amma, a bayyane yake cewa muna rayuwa ne a lokaci na musamman a tarihin ’yan Adam.

Wasu ƙwararru sun ce mun kusa lokacin da za a yi gagaruman canje-canje a duniya. Alal misali, a shekara ta 2014, wasu masana sun gargaɗi Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a kan barazanar da ake wa rayuwar ’yan Adam a duniya. Waɗannan masana sun ce: “Binciken da aka yi ya sa mun kammala cewa yadda kan mutane ke daɗa wayewa tana ci gaba da sa rayuwar ’yan Adam cikin haɗari.” Mutane da yawa suna daɗa gaskata cewa muna rayuwa ne a lokaci na musamman a tarihin ’yan Adam. Mawallafan wannan mujallar da mutane da yawa da ke karanta ta sun tabbata cewa muna rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe kuma ƙarshen duniyar nan ta kusa. Amma maimakon jin tsoro don abin da zai faru a nan gaba, zai dace ka yi farin ciki don sakamakon da za a samu. Me ya sa ya kamata ka yi farin ciki? Domin za ka iya tsira wa ƙarshen wannan duniyar!