Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 KA KUSACI ALLAH

“Ka Bayyana Su ga Jarirai”

“Ka Bayyana Su ga Jarirai”

Kana son ka san gaskiya game da Allah, wato, ko wane ne shi, abin da yake so da wanda ba ya so da kuma nufinsa? A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah Allah ya bayyana kome game da kansa. Amma ba kowa ba ne zai iya karanta Littafi Mai Tsarki kuma ya fahimci gaskiyar da ke ciki. Me ya sa? Domin fahimtar gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki gata ne daga Allah kuma ba kowa ba ne yake samun wannan gatan. Bari mu tattauna abin da Yesu ya ce game da hakan.—Ka karanta Matta 11:25.

Wannan ayar ta soma da cewa: “A cikin lokacin nan Yesu ya amsa, ya ce.” Saboda haka, wataƙila Yesu yana so ya yi magana ne a kan abin da ya faru. Bai daɗe ba da Yesu ya tsawata wa mazauna wasu birane uku a Galilee, waɗanda suka ƙi gaskata da shi duk da cewa ya yi mu’ujizai a biranensu. (Matta 11:20-24) Wataƙila, za ka iya tambaya, ‘Yaya za a yi wani ya shaida ayyukan al’ajabi da Yesu ya yi kuma ya ƙi gaskata da shi?’ Mutanen nan sun ƙi gaskata da Yesu ne saboda taurin kai.—Matta 13:10-15.

Yesu ya san cewa idan mutum yana son ya fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, yana bukatar abubuwa guda biyu: taimakon Allah da kuma sahihiyar zuciya. Yesu ya ce: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” Ka ga abin da ya sa za a iya ce fahimtar gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki gata ne, ko ba haka ba? Jehobah yana da iko ya bayyana gaskiya ko kuma ya ɓoye ta ga wanda ya ga dama don shi ne “Ubangijin sama da ƙasa.” Amma Allah ya ba wa kowa zarafin fahimtar gaskiyar domin shi ba mai tara ba ne. To, me ya sa yake bayyana gaskiyar ga wasu amma ga wasu kuma sai ya ɓoye?

Jehobah ba ya son masu girman kai amma yana ƙaunar masu tawali’u. (Yaƙub 4:6) Yakan ɓoye gaskiya ga “masu-hikima” na duniya, wato, waɗanda girman kai yake sa su tunanin cewa ba sa bukatar taimakonsa. (1 Korintiyawa 1:19-21) Amma yana bayyana gaskiyar ga “jarirai,” wato, mutane masu sahihiyar zuciya da suke da tawali’u kamar yara ƙanana. (Matta 18:1-4; 1 Korintiyawa 1:26-28) Yesu, Ɗan Allah, ya ga mutanen da suka nuna girman kai da kuma waɗanda suka kasance da tawali’u. Shugabannin addinai masu ilimi da yawa da suke da fahariya ba su fahimci koyarwar Yesu ba, amma masu kama kifi da ke da tawali’u sun fahimci koyarwarsa. (Matta 4:18-22; 23:1-5; Ayyukan Manzanni 4:13) Duk da haka, akwai masu arziki da kuma ilimi da suka nuna tawali’u kuma suka zama almajiran Yesu.—Luka 19:1, 2, 8; Ayyukan Manzanni 22:1-3.

Bari mu sake yin tambayar da muka yi a farkon talifin nan: Kana son ka san gaskiya game da Allah? Idan amsarka e ce, za ka yi farin cikin sanin cewa Allah ba ya ƙaunar waɗanda suke ɗaukan kansu masu hikima a al’amuran duniya. Akasin haka, yana barin masu tawali’u su sami iliminsa, wato, waɗanda masu hikimar duniyar nan sukan raina. Idan ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki cikin tawali’u, za ka iya zama ɗaya daga cikin waɗanda Jehobah yake ba su wannan babban gata na sanin gaskiya game da shi. Sanin wannan gaskiyar zai sa rayuwarka ta ƙara kasancewa da ma’ana a yanzu kuma zai iya kai ga samun “hakikanin rai,” wato, rai na har abada a cikin sabuwar duniya na adalci da Allah ya yi alkawarinsa wanda zai zo ba da daɗewa ba. *—1 Timotawus 6:12, 19; 2 Bitrus 3:13.

Karatun Littafi Mai Tsarki

Matta 1-21

^ sakin layi na 7 Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka ka koyi gaskiya game da Allah da kuma nufinsa. Suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta ta wajen amfani da littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?