JEHOBAH ALLAH mai karimci ne. (Yaƙ. 1:17) Taurari da ke ko’ina a sararin sama da itatuwa da tsire-tsire da Allah ya halitta a duniya sun nuna cewa shi mai karimci ne.—Zab. 65:12, 13; 147:7, 8; 148:3, 4.

Marubucin zabura ya nuna godiya ga Jehobah wanda ya halicci kome kuma ya rera waƙa don ya ɗaukaka shi. Ka karanta Zabura ta 104 don kai ma ka ga yadda Jehobah ya cancanci ɗaukaka. Marubucin zabura ya ce: “Zan raira [waƙa] ga Ubangiji muddar raina. Zan raira yabo ga Allahna muddar akwai ni.” (Zab. 104:33) Babu shakka, kai ma kana da wannan burin.

BABU MAI KARIMCI KAMAR JEHOBAH

Jehobah yana so mu yi koyi da shi a nuna karimci. Ƙari ga haka, ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata mu kasance masu bayarwa sa’ad da ya ja-goranci manzo Bulus da ruhu mai tsarki ya rubuta cewa: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu; su yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyyar bayarwa, masu son zumunta; suna ajiye wa kansu tushe mai kyau domin lokaci mai zuwa, da za su ruski rai wanda yake hakikanin rai.”—1 Tim. 6:17-19.

Sa’ad da manzo Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu zuwa ga ikilisiyar da ke Korinti, ya ƙarfafa ’yan’uwa su kasance da kyakkyawar anniya sa’ad da suke bayarwa. Bulus ya ce: “Kowane mutum ya aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Kor. 9:7) Bayan haka, Bulus ya ambaci waɗanda suke amfana daga halin bayarwa. Na ɗaya, masu karɓa don Allah yana biyan bukatun su ta hakan. Na biyu Allah yana yi wa masu bayarwa albarkar don karimcinsu.—2 Kor. 9:11-14.

Sa’ad da Bulus yake kammala sura 8 da 9 na wannan wasiƙarsa, ya ambaci dalilin da ya nuna cewa Allah shi ne babban mai karimci. Ya ce: “Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban magana.” (2 Kor. 9:15) Kyautar da Jehobah yake bayarwa ya haɗa da dukan alherin da ya nuna ga bayinsa ta wurin Yesu Kristi. Darajar wannan kyautar ta wuce misali.

Ta yaya za mu nuna godiya don dukan abubuwan da Jehobah da Ɗansa suka yi mana da kuma waɗanda za su yi a nan gaba? Hanya ɗaya ita ce ta ba da lokacinmu da kuzarinmu da kuma wasu dukiyarmu don a sami ci gaba a yin wa’azin bishara da kuma wasu ayyuka na ƙungiyar Jehobah, ko da gudummawar da za mu iya yi kaɗan ko da yawa.—1 Laba. 22:14; 29:3-5; Luk. 21:1-4.