Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Oktoba 2015

Ku Rika “Girmama Irin Wadannan Mutane”

Ku Rika “Girmama Irin Wadannan Mutane”

A SHEKARA ta 1992, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta naɗa ƙwararrun dattawa don sun taimaka wa kwamitoci dabam-dabam na hukumar don su cim ma ayyukansu. * An zaɓi waɗannan masu taimako ne daga “waɗansu tumaki” kuma suna taimaka wa Hukumar sosai. (Yoh. 10:16) Suna halartar taron mako-mako na kwamiti da suke yi wa hidima. Aikin su shi ne ba da shawarwari da kuma wasu labaran da ake bukata. Hukumar ce take yanke shawara sa’an nan masu taimako su aiwatar da waɗannan shawarwarin da kuma duk wani aikin da aka ba su. Masu taimakon suna bin membobin hukumar zuwa manyan taro na musamman da na ƙasashe. Ƙari ga haka, ana iya aika su ofisoshin Shaidun Jehobah a ƙasashe dabam-dabam don su yi hidima a matsayinsu na wakilan hedkwatar Shaidun Jehobah.

Ɗaya daga cikin masu taimakon da ya yi hidima a wannan matsayin tun da aka kafa wannan tsarin ya ce: “Idan na kula da aikin da aka danƙa mini, hakan yana ba wa hukumar dama ta mai da hankali sosai ga ayyukanta.” Wani ɗan’uwa da ya yi sama da shekara 20 yana hidima a matsayinsa na mataimaki ya ce: “Wannan gatan ya fi duk wani abin da na zata.”

Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta danƙa wa waɗannan masu taimako ayyuka da yawa kuma suna godiya saboda hidima mai kyau da waɗannan ’yan’uwa masu ƙwazo suke yi. Bari mu riƙa “girmama irin waɗannan mutane.”Filib. 2:29.

^ sakin layi na 2 Za ka sami taƙaitaccen bayani game da ayyukan da kwamitoci shida na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suke yi a shafi na 131 na littafin Mulkin Allah Yana Sarauta!