Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Kusantar Allah Ta Taimaka Min

Kusantar Allah Ta Taimaka Min

NA DAINA girma sa’ad da nake ’yar shekara tara. Hakan ya faru shekaru 34 da suka shige a ƙasar Kwaddebuwa kuma a yau, tsayina kafa uku ne kawai. A lokacin da iyayena suka gane cewa ban zan ƙara girma ba sai suka ƙarfafa ni in riƙa yin aiki sosai don kada na riƙa damuwa da fasalina. Sai na soma sayar da ’ya’yan itace a kofar gidanmu kuma ina tsabtace wurin. Hakan ya sa na sami abokan ciniki da yawa.

Hakika, kasancewa da ƙwazo bai canza komai ba. Ban ƙara tsayi ba kuma yin abubuwan masu sauƙi yana yi mini wuya kamar ɗaukan abu da ke saman kanta. Sai nake gani kamar an yi abubuwa don mutane da suka ninka ni a tsayi sau biyu. Na ji tausayin kaina amma abubuwa sun canja sa’ad da na kai ’yar shekara 14.

Wata rana wasu mata biyu sun sayi ’ya’yan itace a wajena. Su Shaidun Jehobah ne kuma suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ba da daɗawa ba, na fahimci cewa sanin Jehobah da kuma nufinsa ya fi muhimmanci fiye da yanayin da nake ciki kuma hakan ya taimaka mini sosai. Ayar da na fi so a cikin Littafi Mai Tsarki ita ce Zabura 73:28 wadda ta ce: “Amma ya yi mini kyau in kusaci Allah.”

Farat ɗaya, iyayena sun ƙaura zuwa ƙasar Burkina Faso kuma hakan ya sa rayuwata ta canja gaba ɗaya. Mutane sun saba gani na a unguwarmu ta dā a ƙasar Kwaddebuwa, amma a sabuwar unguwarmu, ni baƙuwa ce kuma wasu mutane ba su taɓa ganin mace irin na ba. Hakan ya sa suna yawan kallona. Saboda haka, na yi makonni ba na fita waje. Sa’ad da na tuna yadda kusantar Jehobah ya taimaka mini, sai na rubuta wasiƙa zuwa Ofishin Shaidun Jehobah kuma suka aika wata ’yar’uwa mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Nani don ta ziyarce ni. Tana zuwa wajena da sukuta kuma ta dace ta yi nazari da ni.

Hanyoyin zuwa unguwarmu suna da santsi sosai kuma da damina hanyar tana zama da caɓi. Nani ta sha faɗuwa daga sukutarta idan tana zuwa yin nazari da ni amma ba ta karaya ba. Sai ta ce tana so ta kai ni taro. Hakan yana nufin cewa zan jure da kallon da mutane za su yi mini. Ƙari ga haka, sukutar tana da wuyan tuƙawa kuma zama a baya zai ƙara mata nauyi. Amma duk da haka, na yarda na je taron kuma na tuna da sashe na biyu na ayar da  na fi so da ta ce: “Na mai da Ubangiji Yahweh mafakata.”

A wani lokaci ni da Nani mukan faɗi a cikin taɓo amma saboda muna son zuwa taro, hakan bai dame mu ba. A Majami’ar Mulki ’yan’uwa suna yi min murmushi, maimakon kallon da mutane suke min a waje. Na yi baftisma bayan watanni tara.

Sashe na uku ta ayar da na fi so ta ce: “Domin in labarta dukan ayyukanka.” Na san cewa wa’azi shi ne zai zama babban ƙalubale da zan fuskanta. Na tuna da rana ta farko da na fara fita wa’azi gida-gida. Yara da manya suna zuba min ido kuma suna bi kuma suna kwaikwayon yadda nake tafiya. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai amma na ci gaba da wa’azi domin na san cewa suna bukatar Aljanna kamar ni.

Na sayi sukuta mai taya uku don abubuwa su kasance mini da sauƙi. Idan muka kai tudu, abokiyar wa’azi ta takan tura ni kuma sa’ad da muke gangarowa, sai ta hau bayan sukutar. Ko da yake da farko yin wa’azi ya yi mini wuya amma na daga baya na soma jin daɗinsa sosai kuma hakan ya sa na soma hidimar majagaba na kullum a shekara ta 1998.

Na yi nazarin Littafi Mai Tsaki da mutane da yawa kuma huɗu daga cikin su sun yi baftisma. Ƙari ga haka, ƙanwata ta soma bauta wa Jehobah kuma hakan ya sa ni farin ciki sosai! Jin yadda wasu suke samun ci gaba a bautar Jehobah yana ƙarfafa ni sosai. Wata rana da nake fama da zazzaɓin cizon sauro, na sami wani saƙo daga ƙasar Kwaddubuwa game da wani ɗalibin jami’a a Burkina Faso da na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Amma, na gaya wa wani ɗan’uwa ya ci gaba da yin nazari da ɗalibin. Daga baya, ɗalibin ya ƙaura zuwa Kwaddubuwa. Na yi farin ciki da na ji cewa ya zama mai shelan da bai yi baftisma ba.

Shin ta yaya nake ciyar da kaina? Wata ƙungiya da ke tallafa wa naƙasassu sun ce za su koya min ɗinki. Amma, sa’ad da wata malama ta lura da yadda nake yin aiki da ƙwazo sai ta ce: “Ya kamata mu koya miki yadda ake yin sabulu.” Abin da suka yi ke nan. Ina yin sabulun wanki da na wanke-wanke. Sabulun da nake yi yana burge mutane kuma sukan gaya wasu game da shi. Sa’ad da aka sayi sabulun, ina kai wa har gidan mutane da sukutana mai taya uku.

Abin baƙin ciki shi ne a shekara ta 2004, ciwon baya ya sa na daina hidimar majagaba. Duk da haka, ina yin iya ƙoƙarina a wa’azin bishara.

Mutane sukan ce ni mai yawan murmushi ne. Hakika, ina da dalili mai kyau na yin farin ciki don kusantar Allah ta taimaka min.—Sarah Maiga ce ta ba da labarin.