Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Satumba 2015

Lamirinka Yana Yi Maka Ja-gora da Kyau Kuwa?

Lamirinka Yana Yi Maka Ja-gora da Kyau Kuwa?

‘Matuƙar dokar ƙauna ce mai-fitowa daga zuciya mai-tsabta da lamiri mai-nagarta da bangaskiya.’ —1 TIM. 1:5.

WAƘOƘI: 57, 48

1, 2. Wane ne ya ba mu lamiri, kuma me ya sa za mu nuna godiya cewa muna da baiwar?

JEHOBAH ALLAH ya halicci ’yan Adam da ’yancin yin abin da suke so. Ƙari haka, ya halicce mu da lamiri, wato abin da zai sa mu san nagarta da kuma mugunta. Idan muka yi amfani da lamirinmu a hanyar da ta dace, zai taimaka mana mu yi nagarta kuma mu guji yin mugunta. Baiwar lamiri ta nuna cewa Allah yana ƙaunarmu kuma yana son ’yan Adam su riƙa yin abin da ya dace.

2 Wasu mutane a yau suna yin nagarta kuma suna ƙin mugunta ko da yake ba su san ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. (Karanta Romawa 2:14, 15.) Lamiri yana hana mutane da yawa yin ayyukan mugunta. Da a ce ba wanda yake da lamiri, da yanayin duniya ya yi muni fiye da yadda yake. Hakika, za mu riƙa yin mugunta sosai. Muna godiya cewa Allah ya halicce ’yan Adam da lamiri!

3. Ta yaya kasancewa da lamiri mai kyau zai amfani ’yan’uwa a ikilisiya?

3 Yawancin mutane ba sa tunanin horar da lamirinsu, amma bayin Jehobah suna son su horar da lamirinsu. Suna son lamirinsu  ya jitu da ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah game da nagarta da mugunta. Halin ’yan’uwa da suka horar da lamirinsu da kyau yana sa ’yan’uwa su riƙa yin abin da ya dace. Idan muna so mu horar da kuma bi ja-gorar lamirinmu, wajibi ne mu ɗauki wasu matakai. Muna bukata mu so ƙa’idodin Allah kuma mu kasance da bangaskiya cewa za su amfane mu. Manzo Bulus ya ce: ‘Matuƙar dokar ƙauna ce mai-fitowa daga zuciya mai-tsabta da lamiri mai-nagarta da bangaskiya marar-riya.’ (1 Tim. 1:5) Yayin da muka horar da lamirinmu kuma muka bi ja-gorarsa, za mu ƙara ƙaunar Jehobah da kuma ƙarfafa bangaskiyarmu. Yadda muke amfani da lamirinmu zai nuna ko mun ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah da kuma da abin da yake cikin zuciyarmu. Zai kuma nuna ko muna so mu faranta wa Jehobah rai ko a’a. Hakika, lamirinmu yana nuna irin halin da muke da shi.

4. Ta yaya za mu horar da lamirinmu?

4 Amma ta yaya za mu horar da lamirinmu? Ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da bimbini a kan abin da muka karanta da kuma bin abin da muka koya. Saboda haka, ba sanin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kawai ba. Ya kamata nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa mu san Jehobah da halayensa da abubuwan da ke faranta masa rai ko ɓata masa rai. Lamirinmu zai sa mu yi abubuwan da suka jitu da ƙa’idodin Jehobah Allah. Hakan zai motsa mu mu riƙa yin koyi da Jehobah.

5. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

5 Amma, ya kamata mu tambayi kanmu: Ta yaya lamiri mai kyau zai taimaka mana sa’ad da muke son mu tsai da shawarwari? Ta yaya za mu daraja lamirin ’yan’uwa? Ta yaya lamirinmu zai motsa mu mu yi ayyukan nagarta? Don mu sami amsar waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna hanyoyi uku da lamirinmu zai iya taimaka mana: (1) jinya, (2) nishaɗi, da (3) sa’ad da muke wa’azi.

KA KASANCE DA SANIN YAKAMATA

6. Wane batu mai muhimmanci ne ’yan’uwa suke yawan tambayoyi a kai?

6 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu guji ayyuka masu lahani kuma mu riƙa nuna sanin yakamata a batun ci da sha. (Mis. 23:20; 2 Kor. 7:1) Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu ɗauki matakai don kāre lafiyarmu sa’ad da muke rashin lafiya da kuma sa’ad da muka tsufa. A wasu ƙasashe ana amfani da maganin turawa da na gargajiya. ’Yan’uwa sukan rubuta wasiƙu a kai a kai zuwa ofisoshin Shaidun Jehobah don su sami ƙarin bayani a batun jinya. Da yawa sukan yi wannan tambayar, “Shin ya dace bawan Jehobah ya amince da irin wannan jinyar?”

7. Waɗanne shawarwari ne muke yi game da jinya?

7 Ba a ba wa ’yan’uwa da ke ofisoshin Shaidun Jehobah ko kuma dattawa izinin tsai shawara wa ’yan’uwa a batun jinya ba, ko da ya nemi shawara daga wurinsu. (Gal. 6:5) Suna iya bayyana masa umurnin Jehobah don su taimaka masa ya tsai da shawara mai kyau. Alal misali, ya kamata Kirista ya tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya ce a guji cin “jini.” (A. M. 15:29) Hakan zai sa ya guji jinyar da ta ƙunshi ƙarin jin ko kuma ɗaya daga cikin waɗannan sassan. Sanin wannan yana iya shafan lamirin Kirista sa’ad da yake tsai da shawara a kan maganin da aka sarrafa daga waɗannan sassa huɗu na jini. * Amma, wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta iya  taimaka mana mu tsai da shawara mai kyau a batun jinya?

8. Ta yaya Filibiyawa 4:5 za ta taimaka mana a batun jinya?

8 Littafin Misalai 14:15 ta ce: “Marar-wayo yana gaskanta kowace magana: Amma mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.” Wasu cututtuka ba su da magani. Saboda haka, muna bukatar mu mai da hankali sosai game da magunguna da ake nuna cewa suna da inganci amma babu tabbacin da ya nuna hakan. An hure Bulus ya rubuta cewa: “Ku bari jimrewarku [“sanin yakamata,” New World Translation] ta sanu ga dukan mutane.” (Filib. 4:5) Kasancewa da sanin yakamata zai taimaka mana mu mai da hankali ga bautar Jehobah maimakon damuwa ainun game da kiwon lafiyarmu. Za mu zama masu son kai idan muka sa kiwon lafiya kan gaba fiye da kome a rayuwarmu. (Filib. 2:4) Bautarmu ga Jehobah ta fi muhimmanci saboda haka ya kamata mu kasance da sanin yakamata a batun jinya.—Karanta Filibiyawa 1:10.

9. Ta yaya Romawa 14:13, 19 suka shafi shawarwarinmu a batun jinya, kuma ta yaya za mu iya sa haɗin kanmu cikin haɗari?

9 Kirista mai sanin yakamata ba ya cusa wa mutane ra’ayinsa. A wata ƙasar Turai, wasu ma’aurata suna ƙarfafa mutane su riƙa shan wasu irin magunguna kuma su bi wani tsarin cin abinci. Sun lallashi wasu ’yan’uwa su yi amfani da magungunan, amma wasu ba su yarda ba. Da shigewar lokaci, magungunan ba su taimaka ba kamar yadda aka zata ba, kuma hakan ya ɓata wa ’yan’uwa da yawa rai. Ma’auratan suna da damar zaɓa wa kansu ko za su bi wani tsarin cin abinci da kuma shan wasu magunguna. Amma bai dace su sa ’yan’uwa su kasance da rashin haɗin kai saboda kiwon lafiya ba. A Roma ta dā, Kiristoci suna da ra’ayi dabam-dabam game da cin wani irin abinci da kuma yin wasu bukukuwa. Wace shawara ce Bulus ya ba su? Ya ce: “Wani yana aza wata rana ta fi wata rana girma: wani kuwa yana aza dukansu ɗaya ne. Bari kowane mutum ya kasance a cikin hankalinsa.” Yana da muhimmanci mu guji yin abin da zai sa ’yan’uwa sanyin gwiwa a bautarsu ga Jehobah.—Karanta Romawa 14:5, 13, 15, 19, 20.

10. Me ya sa ya kamata mu riƙa daraja shawarwarin wasu? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)

10 Idan ba mu fahimci dalilin da ya sa wani ɗan’uwa ya tsai da wasu shawarwari ba, bai dace mu kushe shi ko kuma tilasta masa ya canja ra’ayinsa ba. Wataƙila lamirinsa “raunana” ne kuma yana bukata ya ƙara horar da lamirinsa, ko kuma ɗan’uwan yana yawan damuwa ko fushi a kan abin da bai taka kara ya ƙarya ba saboda lamirinsa. (1 Kor. 8:11, 12) A wani ɓangaren kuma, wataƙila ya kamata mu bincika kanmu ko mu ne ke bukatar horar da lamirinmu don mu ƙara fahimtar  ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. A batun jinya, ya kamata kowannenmu ya kasance a shirye ya tsai da shawara da kansa kuma ya rungumi sakamakon da hakan zai kawo.

KA RIƘA YIN NISHAƊIN DA YA DACE

11, 12. Sa’ad da muke zaɓan nishaɗi, wane gargaɗin Littafi Mai Tsarki ne ya kamata mu tuna?

11 Jehobah ya halicci ’yan Adam a hanyar da za su iya jin daɗin nishaɗi kuma su amfana. Sulemanu ya rubuta cewa da akwai “lokacin dariya” da “lokacin rawa.” (M. Wa. 3:4) Amma, ba dukan nishaɗi ne suke da amfani ba kuma ba duka ba ne suke wartsakarwa ba. Ƙari ga haka, bai dace mu riƙa yawan yin nishaɗi ba ko kuma a kowane lokaci ba. Ta yaya lamirinmu zai taimaka mana mu ji daɗin nishaɗi mai kyau kuma mu amfana?

12 Littafi Mai Tsarki ya ba mu gargaɗi a kan wasu halayen “ayyukan jiki.” Waɗannan halayen sun ƙunshi “fasikanci, da aikin lalata, da fajirci, da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya, da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu.” Bulus ya rubuta cewa “masu yin irin waɗannan abubuwa ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.” (Gal. 5:19-21, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, muna iya tambayar kanmu: ‘Shin lamirina yana sa na ƙin yin wasanni da ke hadassa gasa da ƙishin ƙasa ko kuma mugunta? Zuciyata tana yi mini horo sa’ad da nake son na ƙalli fim da ke ɗauke da batsa ko lalata ko maye ko kuma sihiri?’

13. Ta yaya ƙa’idodin da ke cikin 1 Timotawus 4:8 da Misalai 13:20 za su taimaka mana sa’ad da muke zaɓan nishaɗi?

13 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka mana mu horar da lamirinmu game da nishaɗi. 1 Timotawus 4:8 ta ce: “Wasa jiki tana da amfaninta kaɗan.” Mutane da yawa suna ganin cewa motsa jiki a kai a kai yana wartsake su kuma yana sa su kasance da koshin lafiya. Amma, idan muna son mu motsa jiki, shin ya kamata mu yi hakan da kowa ne? Misalai 13:20 ta ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” Hakika, hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci mu bi ja-gorar lamiri da aka horar bisa Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi.

14. Ta yaya wasu iyaye suka taimaka wa ’yarsu ta bi ƙa’idar da ke cikin Romawa 14:2-4?

14 Christian da Daniela suna da yara biyu. Christian ya ce: “Mun tattauna batun nishaɗi sa’ad da muke Ibada ta Iyali da yamma. Mun yarda cewa wasu nishaɗi suna da kyau amma wasu ba su da kyau. Shin su wane ne abokan kirki? Ɗaya cikin yaranmu ta ce a lokacin hutu a makarantarsu, wasu Shaidu matasa suna yin abubuwa da take gani ba su dace ba. Tana ji kamar ta yi abubuwa da suke yi. Mun tattauna da ita cewa kowannenmu yana da lamiri, kuma ya kamata mu bar lamirinmu ya yi mana ja-gora a dukan abubuwan da muke yi da kuma wanda muke yin hakan da shi.”—Karanta Romawa 14:2-4.

Lamirinka zai taimaka maka ka guji abubuwan da ba su da kyau (Ka duba sakin layi na 14)

15. Ta yaya bincika Matta 6:33 zai taimaka maka sa’ad da kake shirin yin nishaɗi?

15 Wani batu kuma shi ne lokacin da muke yin nishaɗi. Shin kana saka ayyuka na ibada kamar halartan taro da wa’azi da nazarin Littafi Mai Tsarki a kan gaba a rayuwarka? Ko kuma nishaɗi ne ka fi so? Mene ne ya fi muhimmanci a gare ka? Yesu ya ce: “Ku fara biɗan  mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.” (Mat. 6:33) Sa’ad da kake tsai da shawara a yadda za ka yi amfani da lokacinka, shin lamirinka yana taimaka maka ka saka abubuwan da suka fi muhimmanci kan gaba?

LAMIRI MAI KYAU YANA SA MU YI ABUBUWAN DA SUKA DACE

16. Ta yaya lamirinmu yake ƙarfafa mu mu yi wa’azi?

16 Lamiri mai kyau yana yi mana gargaɗi da kuma motsa mu mu yi abubuwan da suka dace. Wani aiki mai muhimmanci shi ne yin wa’azi gida gida da kuma duk lokacin da ka sami zarafin yin wa’azi. Lamirin Bulus ya motsa shi ya yi hakan. Ya ce: “Ya zama mani dole; kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba!” (1 Kor. 9:16) Idan muka yi koyi da shi, za mu kasance da lamiri mai kyau da sanin cewa muna yin abin da ya dace. Kuma ta wajen yin wa’azin bishara, muna taimaka wa mutane su yi amfani da lamirinsu wajen yin abin da ya dace. Bulus ya ce: “Bisa ga bayyanawar gaskiya muna koɗa kanmu ga lamirin kowane mutum a gaban Allah.”—2 Kor. 4:2.

17. Ta yaya wata matashiya ta bi abin da lamirinta ya gaya mata?

17 Sa’ad da Jacqueline take ’yar shakara 16, ta yi nazarin halittu a makaranta. Aka bayyana musu koyarwar juyin halitta. Ta ce: “Lamirina ya hana ni saka baki a tattaunawa a cikin aji kamar yadda na saba yi. Ban zan iya goyon bayan koyarwar juyin halitta ba. Na je wajen malamin kuma na bayyana masa ra’ayina. Abin mamaki, malamin ya nuna sanin yakamata kuma ya ba ni damar yin magana ga dukan ’yan ajin a kan batun halitta.” Jacqueline ta yi farin ciki cewa ta bi lamirinta da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Shin lamirinka yana motsa ka ka yi abin da ya dace?

18. Me ya sa ya kamata mu kasance da lamiri mai kyau?

18 Maƙasudinmu shi ne mu yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodi da mizanan Jehobah. Kuma lamirinmu zai taimaka mana mu cim ma wannan maƙasudin. Za mu horar da lamirinmu, idan muna nazarin Kalmar Allah a kai a kai da yin bimbini a kan abin da muka karanta kuma muka yi ƙoƙarin bin abin da muka koya. Hakan zai sa lamirinmu ya zama kyauta mai tamani da zai riƙa yi mana ja-gora a rayuwa!

^ sakin layi na 7 Ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” shafuffuka na 215-218.