MUTANE da yawa su san cewa Yesu yana da manzanni 12. Amma wataƙila ba sun san cewa wasu mata sun zama almajiransa ba. Ɗaya daga cikin su ita ce Yuwanna.—Mat. 27:55; Luk. 8:3.

Mene ne Yuwanna ta yi a lokacin da Yesu ya yi hidima a duniya, kuma me za mu iya koya daga misalin da ta kafa?

WACE CE YUWANNA?

Yuwanna ita ce “matar Kuza wakilin Hirudus.” Wataƙila Kuza ma’aikaci mai kula da harkokin cikin gidan Hirudus Antibas ne. Yuwanna tana ɗaya daga cikin mata da yawa da Yesu ya warƙar da su daga cututtukansu. Yuwanna da wasu mata, sun yi tafiya tare da Yesu da manzaninsa.—Luk. 8:1-3.

Malaman Yahudawa sun koyar cewa bai kamata mata su yi tarayya da mazan da ba danginsu ba, balle ma su yi tafiya da su. Ƙari ga haka, sun koyar cewa bai kamata mazan Yahudawa su yi magana da mata sosai ba. Yesu bai ɗaukaka waɗannan al’adun ba, kuma ya bar Yuwanna da sauran matan su yi tafiya da shi.

Yuwanna ba ta damu da tsegumin da mutane za su yi mata don tana bin Yesu da manzaninsa ba. Wajibi ne duk waɗanda suke son su bi shi su shirya don yin hakan. Game da waɗannan mabiyansa, Yesu ya ce: “Waɗanda suna jin maganar Allah, suna aikatawa, su ne uwata da ’yan’uwana.” (Luk. 8:19-21; 18:28-30) Sanin cewa Yesu ya damu da waɗanda suka yi sadaukarwa don su bi shi abin ƙarfafa ne, ko ba haka ba?

TA YI HIDIMA DA DUKIYARTA

Yuwanna da wasu mata sun yi wa Yesu hidima da “dukiyarsu.” (Luk. 8:3) Wani masani ya ce: “Ba wai Luka yana gaya mana cewa waɗannan matan sun dafa musu abinci ko wanke kwanuka ko kuma gyara musu kaya ba. Wataƙila sun yi waɗannan abubuwan, amma Luka bai ce hakan ba.” Mai yiwuwa sun yi amfani da kuɗinsu da dukiyarsu don su taimaka wa abokan tafiyarsu.

Yesu da manzanninsa ba su yi wata sana’a a lokacin da suke wa’azi ba. Saboda haka, wataƙila ba su da isashen kuɗin sayan abinci da kuma biyan bukatunsu. Mai yiwuwa, sun kai mutane 20. Ko da yake mutane sun nuna wa Yesu da manzaninsa karimci, ba su dogara da abin da aka ba su ba,  shi ya sa suke tafiya da jakar kuɗi. (Yoh. 12:6; 13:28, 29) Kuma wataƙila Yuwanna da sauran matan sun ba da gudummawa don biyan bukatunsu.

Waɗansu sun ce matan Yahudawa ba su da dukiya. Amma, wasu littattafai da aka rubuta a lokacin sun nuna cewa mace tana iya samun dukiya ta hanyoyi dabam-dabam: (1) ta gādo daga wurin mahaifinta idan bai haifi ’ya’ya maza ba, (2) ta kyautar dukiyar, (3) ta diyya da ake ba wa mace sa’ad da aka kashe aure, (4) ta mallakar dukiyar mijinta da ya rasu ko kuma (5) ta sana’ar kanta.

Babu shakka, mabiyan Yesu sun yi iya ƙoƙarinsu don su ba da gudummawa. Kuma wataƙila wasu a cikin mabiyansa mata ne masu wadata. Wasu suna ganin cewa Yuwanna tana da kuɗi domin ita matar ma’aikacin Hirudus ne. Yana iya yiwuwa cewa ita ce ta saya taguwa mai tsada da Yesu yake saka wa. Wata masaniya ta ce “matan masu kama kifi ba za su iya sayan wannan kayan ba.”—Yoh. 19:23, 24.

Littafi Mai Tsarki bai ambata cewa Yuwanna ta ba da gudummawar kuɗi ba. Amma ta yi iya ƙoƙarinta, kuma hakan ya koya mana darasi. Mu ne za mu yanke shawara game da yawan gudummawar da za mu ba da don faɗaɗa ayyukan Mulki. Amma Allah ya fi so mu yi hakan da farin ciki.—Mat. 6:33; Mar. 14:8; 2 Kor. 9:7.

YUWANNA TA KASANCE DA AMINCI GA YESU

A bayyane yake cewa Yuwanna ta kasance a wurin da aka kashe Yesu. Ta kasance cikin waɗanda suka bi shi suna masa hidima “sa’anda yana cikin Galili; da waɗansu mata kuma waɗanda suka zo Urushalima tare da shi.” (Mar. 15:41) Lokacin da aka cire gawar Yesu don a binne, “mata kuwa waɗanda suka fito daga Galili tare da shi, suka bi baya, suka duba kabarin, da yadda aka ajiye jikinsa. Suka komo, suka shirya kayan kanshi da man kanshi.” Luka ya ce waɗannan matan wato “Maryamu Magdaliya da Yuwanna da Maryamu Uwar Yaƙub” sun koma bayan assabaci kuma sun ga mala’ikun da suka gaya musu cewa an ta da Yesu daga mutuwa.—Luk. 23:55–24:10.

Yuwanna da sauran mata sun yi iya ƙoƙarinsu don su yi wa Ubangijinsu hidima

Wataƙila Yuwanna, tare da uwar Yesu da kuma ’yan’uwansa suna cikin almajiran da suka taru a Urushalima a ranar Fentakos na shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu. (A. M. 1:12-14) Da yake Luka ne kaɗai ya ambaci sunan Yuwanna, wasu suna gani cewa ita ce ta yi wa Luka bayani game da Hirudus Antibas don tana da masaniya game da abubuwan da ke faruwa a fadar.—Luk. 8:3; 9:7-9; 23:8-12; 24:10.

Labarin Yuwanna yana cike da darussa masu muhimmanci. Ta yi iya ƙoƙarinta don ta yi wa Yesu hidima. Idan gudummawar da ta bayar ta taimaka wa Yesu da kuma almajiransa su yi tafiye-tafiye don wa’azi, hakan ya sa ta farin ciki tabbas. Ta yi wa Yesu hidima kuma ta kasance da aminci duk da wahalar da shi da almajiransa suka fuskanta. Ya dace ’yan’uwa mata su yi koyi da halinta.