Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 Tarihi

Bari Tsibirai da Yawa Su Yi Murna

Bari Tsibirai da Yawa Su Yi Murna

Ba zan taɓa mantawa da ranar nan ba. Ina tare da ’yan’uwa da yawa daga ɓangarori dabam-dabam na duniya kuma muna jira a daƙin da membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suke taro. Muna so mu yi wata gabatarwa ga Kwamitin Rubuce-Rubuce. ’Yan makonni da suka wuce, mun bincika matsaloli da mafassara suke fuskanta, kuma yanzu muna son mu ba da shawarwari a kan yadda za a magance su. Me ya sa wannan taron da muka yi a ranar 22 ga Mayu, 2000, yake da muhimmanci sosai? Kafin in ba ka labari, bari in yi maka wani bayani game da kaina.

An yi mini baftisma a Queensland, na yi hidimar majagaba a Tasmaniya, kuma na yi hidima a tsibiran Tuvalu da Samoa da kuma Fiji

AN HAIFE ni a jihar Queensland da ke ƙasar Ostareliya, a shekara ta 1955. Jim kaɗan bayan haka, Shaidun Jehobah suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mahaifiyata Estelle. An yi mata baftisma a shekara ta 1956 kuma mahaifina Ron ya soma bauta wa Jehobah shekaru 13 bayan hakan. An yi mini baftisma a garin St. George na jihar Queensland a shekara ta 1968.

Tun ina yaro, ina son yin karatu da kuma koyon yare. Sa’ad da muke tafiye-tafiye, iyayena ba sa jin daɗi cewa ina karatu yayin da nake zaune a bayan mota maimakon in riƙa kallon wurare. Son yin karatu ya taimaka mini sosai a makaranta. Sa’ad da nake makarantar sakandare a birnin Glenorchy da ke jihar Tasmaniya na ci lambobin yabo da dama.

A wannan lokacin, ina bukatar in tsai da shawara mai muhimmanci. Na ci sukolashif na zuwa jami’a. Duk da son karatu da nake yi, mahaifiyata ta taimaka mini in ƙaunaci Jehobah fiye da. (1 Kor. 3:18, 19) Sa’ad da na gama makarantar sakandare ina ɗan shekara 15, sai na soma hidimar majagaba a watan Janairu, a shekara ta 1971, da izinin iyayena.

 A shekaru takwas da suka biyo baya, na yi hidimar majagaba a jihar Tasmaniya kuma na auri wata kyakkyawar yarinya ’yar Tasmaniya mai suna Jenny Alcock a lokacin, muka yi shekara huɗu muna hidimar majagaba na musamman a yankunan da babu masu shela a garuruwan Smilthton da Queenstown.

HIDIMA A TSIBIRAN FASIFIK

A shekara ta 1978 ne lokaci na farko da ni da matata muka halarci taron ƙasashe a Port Moresby, babban birnin ƙasar Papua New Guinea. A wannan taron wani ɗan’uwa mai wa’azi a ƙasar waje ya ba da jawabi a yaren Hiri Motu. Ban gane kome da ya faɗa ba, amma jawabinsa ya motsa ni kuma na soma sha’war yin wa’azi a ƙasar waje, da koyon wasu harsuna don in ba da jawabai kamar yadda ya yi. Yanzu, na sami zarafin cim ma burina na koyan yaruka a hidimata ga Jehobah.

Sa’ad da muka koma Ostareliya, wani abin mamaki ya faru da mu. An gayyace mu mu je hidima a ƙasashen Funafuti da Tuvalu wadda a dā ake kira tsibirin Ellice. Mun isa wurin a watan Janairu a shekara ta 1979, kuma a lokacin masu shela da suka yi baftisma guda uku ne kaɗai a ƙasar Tuvalu.

Ni da matata Jenny a Tuvalu

Koyon yaren Tuvalu ba shi da sauƙi. “Sabon Alkawari” ne kawai littafin da suke da shi a yaren. Da yake, babu ƙamus a yaren kuma babu inda ake koyarwa, sai muka soma koyon sababbin kalmomi guda 10 zuwa 20 a kowace rana. Ba da daɗewa ba, muka gane cewa ba mu fahimci ainihin ma’anar yawancin kalmomin da muke koya ba. Alal misali, maimakon mu gaya wa mutane cewa tsafi ba shi da kyau, muna koya musu cewa su guji yin amfani da ma’auni da kuma sanduna! Amma wajibi ne mu koyi yaren don mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Saboda haka, ba mu karaya ba. Shekaru bayan haka, wani da muka taɓa yin nazari da shi a lokacin da muke koyon yaren ya ce mana: “Muna farin ciki cewa yanzu kun iya yarenmu. Da farko, ba ma fahimtarku!”

A wani ɓangaren kuma, akwai wasu abubuwa da suka faru da suka taimaka mana sosai a koyon sabon yaren. Da yake babu gidajen haya, mun zauna da wani iyalin Shaidun Jehobah a babban ƙauyen da ke yankin. Hakan ya sa ya zama dole mu yi yaren sa’ad da muka fita wa’azi da kuma a gida. Bayan mun yi wasu shekaru ba ma Turanci, sai muka iya yaren sosai.

Ba da daɗewa ba, mutane da yawa suka soma koya game da Jehobah. Amma da mene ne za mu  yi nazari da su? Ba mu da wani littafi da aka buga a yarensu. Ta yaya za su yi nazari da kansu? Sa’ad da suka soma zuwa taro, waɗanne waƙoƙi ne za su yi, waɗanne littattafai ne za su yi amfani da su? Ƙari ga haka, ta yaya za su yi shirin taro? Ta yaya za su sami ci-gaba har su yi baftisma? Hakika, waɗannan mutane masu tawali’u suna bukatar littattafanmu a yarensu! (1 Kor. 14:9) Mun yi fargaba cewa ba za a buga littattafanmu a yaren Tuvalu ba don masu faɗin yaren ba su kai 15,000 ba. Jehobah ya amsa waɗannan tambayoyin kuma hakan ya nuna cewa (1) Yana so a yaɗa Kalmarsa a “tsibirai masu-nisa,” (2) yana so mutane da duniya take ganin “masu talauci” ne su sami mafaka a sunansa.—Irm. 31:10; Zaf. 3:12.

MUN SOMA AIKIN FASSARA

A shekara ta 1980 ofishin Shaidun Jehobah da ke Fiji ya umurce mu mu yi aikin fassara, aikin da ba ma tsammanin za mu iya yi. (1 Kor. 1:28, 29) Da farko, mun sayi wata tsohuwar na’urar buga littattafai daga hannun gwamnati kuma muka soma buga littattafan da za mu yi amfani da su a taro. Har ma mun fassara littafin nan Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami da wannan na’urar. Ba zan manta da warin tawadar da kuma ƙoƙarin da muka yi a wannan yanayi mai zafi don mu buga waɗannan littattafai da hannunmu ba. A lokacin, babu wutar lantarki!

Yin fassara zuwa Tuvalu ba shi da sauƙi don babu littattafan bincike da yawa a yaren. Amma, a wani lokaci mukan sami taimako daga wuraren da ba mu yi tsammani ba. Wata safiya a rashin sani, na je wa’azi a gidan wani tsoho da ya taɓa aikin malanta kuma mutumin ba ya son sauraronmu. Ya gaya min cewa kada mu riƙa zuwa wa’azi a gidansa kuma sai ya ce: “Ina son in gaya maka wani abu. A fassararku, kuna yawan amfani da tsarin magana da ba a cika amfani da su a yaren Tuvalu.” Sai na tambayi wasu kuma suka ce haka ne. Saboda haka, sai muka yi gyare-gyare don mu kyautata fassararmu. Amma, na yi mamaki cewa Jehobah ya sa maƙiyinmu ya taimaka mana. Hakan ya nuna cewa yana karanta littattafanmu!

Kingdom News No. 30 a yaren Tuvalu

 Abin da muka soma bugawa a yaren Tuvalu don rarraba wa jama’a shi ne takardar gayyata zuwa taron Tuna Mutuwar Yesu. Bayan haka, sai muka buga Kingdom News No. 30, kuma aka fitar da shi a lokaci ɗaya da na Turancin. Mun yi farin ciki cewa an buga wa mutanen littattafai a yarensu! Da sannu-sannu, aka wallafa wasu ƙasidu da littattafai a yaren Tuvalu. A shekara ta 1983, an soma buga Hasumiyar Tsaro mai shafuffuka 24 da ake fitarwa kowane wata uku a ofishin Shaidun Jehobah na ƙasar Ostareliya. Hakan ya sa muna nazarin kimanin sakin layi bakwai kowane mako. Ta yaya waɗannan littattafan suka shafi mutanen? Da yake mutanen Tuvalu suna son karatu, sai mutane da yawa suka so littattafanmu sosai. Duk lokacin da muka fitar da wani littafi, sai a sanar a gidan rediyo na gwamnati. A wani lokaci ma yana zama a cikin kanun labaran! *

Muna soma fassarar a kan takarda. Daga baya, sai a buga da tafireta sau da sau kuma a aika zuwa ofishinmu da ke gurza littattafai a Ostareliya. Akwai lokacin da ofishin yake amfani da wasu ’yan’uwa mata biyu don shigar da fassarar da muka yi a cikin kwamfuta ko da yake ba sa yin yaren Tuvalu. Wannan tsarin shigar da fassarar sau biyu da kuma duba bambancin daga kwamfuta ya taimaka sosai wajen rage kurakurai. Bayan an tsara yadda littafin zai kasance, sai a gurza kuma a aika mana ta wasiƙa don mu duba kuma mu yi gyara. Sa’an nan mu sake aika zuwa ofishinmu don a buga.

Amma yanzu, abubuwa sun canja sosai! Yanzu mafassara suna shigar da rubutun kai tsaye a kwamfuta. A yawancin lokaci, ana shirya fassarar da aka gama gyararta a inda masu fassarar suke. Bayan haka, sai a aika fassarar ta intane zuwa ofisoshinmu da ke buga littattafai. Yanzu ba ma hanzarin zuwa gidan waya don mu aika fassararmu.

MUN SAMI ƘARIN AIKI

Da shigewar shekaru, ni da matata Jenny mun yi hidima a wurare dabam-dabam a tsibiran da ke Fasifik. An tura mu daga Tuvalu zuwa ofishinmu da ke Samoa a shekara ta 1985. Sa’ad da muka je wurin, mun taimaka wajen yin fassara zuwa yarukan Samoa da Tonga da kuma Tokelau. * Daga baya, a shekara ta 1996, aka tura mu zuwa ofishinmu da ke Fiji don mu taimaka da aikin fassara da ake yi zuwa yarukan Fiji da Kiribati da Nauru da Rotuma da kuma Tuvalu.

Yin amfani da littattafanmu a yaren Tuvalu wajen taimaka wa mutane

Himmar masu fassara littattafanmu tana burge ni a kowane lokaci. Aikin fassara yana da wuya kuma yana sa gajiya. Amma, waɗannan ’yan’uwan suna koyi da Jehobah wanda yake so a yi wa’azin bishara ga ‘kowace . . . ƙabila da harshe da al’umma.’ (R. Yoh. 14:6) Alal misali, sa’ad da ake shirin fassara Hasumiyar Tsaro ta farko zuwa yaren Tonga, na haɗu da dukan dattawan da ke Tonga kuma na tambaye su ko akwai wanda da za a horar da shi a aikin fassara. Wani dattijo da yake aikin makaniki ya ce zai bar aikinsa washe gari kuma ya soma fassara ba tare da ɓata lokaci ba. Abin da ya yi ke  nan. Hakan yana da ban ƙarfafa sosai don ɗan’uwan yana da iyali da yake ciyarwa. Amma Jehobah ya kula da shi da kuma iyalinsa, ya yi shekaru da yawa yana aikin fassara.

Waɗannan ’yan’uwan da suka ba da kai suna da ra’ayi ɗaya da mambobin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah waɗanda suke son a buga littattafanmu a dukan harsuna, har da waɗanda mutane kalilan ne suke yi. Alal misali, akwai lokacin da aka yi tambaya ko ya dace a riƙa buga littattafanmu a yaren Tuvalu. Amsar da Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta bayar ya ƙarfafa ni sosai, wasiƙar ta ce: “Ba mu ga abin da ya sa za ku daina fassara a yaren Tuvalu ba. Ko da yake, yankin Tuvalu bai da girma kamar yankunan wasu yaruka, mutanen suna bukatar su ji bishara a yarensu.”

Ana yin baftisma a tafki

A shekara ta 2003, an tura ni da matata Jenny daga Sashen Fassara da ke ofishinmu da ke ƙasar Fiji zuwa Sashen Taimakon Masu Fassara da ke Patterson a New York da ke Amirka. Abin nema ya samu! Mun kasance cikin rukunin da ke taimakawa don a fassara littattafanmu zuwa harsuna da yawa. Mun yi wajen shekara biyu muna zuwa ƙasashe dabam-dabam don mu horar da mafassara.

WASU MATAKAI MASU MUHIMMANCI

Yanzu barin in yi bayani game da gabatarwa da na ambata ɗazu. A shekara ta 2000, Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ga cewa ya dace a horar da masu fassara a faɗin duniya. Domin, zuwa wannan lokacin, yawancin masu fassara ba su sami isashen horo ba. Bayan mun yi gabatarwar ga Hukumar Rubuce-rubuce, sai Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta amince a koyar da dukan masu fassara a faɗin duniya. Wannan koyarwar ya ƙunshi yadda za su ƙara fahimtar Turanci da magance matsalolin da ke tasowa sa’ad da suke fassara da kuma yadda za su yi aiki tare a matsayin rukuni.

Mene ne sakamakon wannan koyarwar? Ta kyautata aikin fassara kuma ta sa ana fassara littattafanmu a harsuna da yawa fiye da dā. Sa’ad da muka je hidimarmu ta farko a ƙasar waje a shekara ta 1979, ana fassara mujallun Hasumiyar Tsaro a harsuna 82 ne kawai. Duk da haka, ana fitar da yawancin mujallun yaren ’yan watanni bayan na Turancin. Amma yanzu, ana fassara Hasumiyar Tsaro a harsuna fiye da 240, kuma ana wallafa yawancinsu a lokaci ɗaya da na Turancin. Bugu da ƙari, ana buga littattafanmu a harsuna fiye da 700. Shekarun baya, mun ɗauka cewa hakan ba zai yiwu ba.

A shekara ta 2004 Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun ɗauki wani mataki mai muhimmanci har ila, wato yadda za a hanzarta fassarar Littafi Mai Tsarki. ’Yan watanni bayan haka, sai aka ba wa fassara Littafi Mai Tsarki fifiko. Hakan ya sa an fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation zuwa harsuna da yawa. A shekara ta 2014, an buga New World Translation ko  kuma sashensa a cikin harsuna 128 kuma hakan ya haɗa da harsunan da ake yi a Kudancin Fasifik.

Fitar da New World Translation of the Christian Greek Scriptures a yaren Tuvalu

Abin da ba zan taɓa mantawa ba shi ne gatan halartan babban taro a Tuvalu a shekara ta 2011. An yi watanni ba a yi ruwan sama ba kuma hakan ya jefa ƙasar cikin wani mugun yanayi na rashin ruwa, hakan ya sa an kusan ɗage babban taron. Amma, ranar da muka zo, an yi ruwa sosai kamar da bakin ƙwarya da yamma, kuma mun yi taron. Na sami gatan fitar da New World Translation of the Christian Greek Scriptures a yaren Tuvalu ko da yake ’yan’uwa da ke yin yaren ba su da yawa, sun sami wannan kyauta mai tamani daga Jehobah. Bayan taron, an sake yin ruwan sama. Saboda haka, mutane sun ji daɗi saboda ƙarfafa daga taron da kuma ruwan sama da aka yi!

Ganawa da iyayena, Ron da Estelle, a wani babban taro a Townsville, Ostareliya, a 2014

Abin baƙin ciki shi ne, matata da muka yi sama da shekara 35 muna hidima tare, ba ta sami damar ganin wannan babbar ranar ba. Ta mutu a shekara ta 2009 bayan ta yi shekara goma tana fama da cutar kansa. A nan gaba, idan aka ta da ita daga mutuwa, za ta yi farin cikin jin cewa an fitar da Littafi Mai Tsarki a yaren Tuvalu.

Tun lokacin, Jehobah ya ba ni wata kyakkyawar mata mai suna Loraini Sikivou. Loraini da Jenny sun yi aiki tare a Bethel da ke ƙasar Fiji, kuma Loraini ta yi aikin fassara zuwa yaren Fiji. Jehobah ya sake ba ni mace mai ƙaunarsa kuma mai son yaruka kamar ni!

Ni da matata Loraini, yayin da muke wa’azi a Fiji

Idan na tuna da abubuwan da suka faru a cikin waɗannan shekarun, ina farin ciki cewa Ubanmu na sama, Jehobah ya ci-gaba da kula da dukan mutane ta wajen tanadar da littattafai a yarensu, har da yarukan da mutane kaɗan ne suke yi. (Zab. 49:1-3) Ina ganin yadda mutane suke farin ciki yayin da suka sami littattafanmu a yarensu ko kuma sa’ad da suke rera waƙa ga Jehobah a yaren da ke ratsa zuciyarsu. (A. M. 2:8, 11) Ba zan manta da abin da wani ɗan’uwa tsoho daga Tuvalu mai suna Saulo Teasi ya faɗa ba. Bayan ya rera waƙarmu a karo na farko a yarensu, ya ce: “Ka gaya wa Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah cewa waƙoƙin suna da daɗi a yaren Tuvalu fiye da na Turanci.”

Tun daga shekara ta 2005, an ba ni babban gatan yin hidima a matsayin memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Ko da yake yanzu ba na fassara, Jehobah ya ba ni damar yin aiki tare da masu taimaka wa mafassara a faɗin duniya. Abin farin ciki ne cewa Jehobah yana kula da dukan mutanensa, har da waɗanda ke tsibiran da ke tsakiyar Tekun Fasifik! Hakika, waɗannan kalaman marubucin zabura yana cika: “Ubangiji [ne] yake mulki; bari duniya ta yi farin ciki; bari taron tsibirai su yi murna.”—Zab. 97:1.

^ sakin layi na 18 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 2000, shafi na 32 a Turanci; da Awake ta 1 Agusta, 1988, shafi na 22; da kuma ta 22 ga Disamba, 2000, shafi na 9, don ka san yadda mutane suka ɗauki littattafanmu.

^ sakin layi na 22 Don samun ƙarin bayani game da aikin fassara a Samoa, ka duba littafin 2009 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 120-121, 123-124.