Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Yuni 2015

Kristi Shi Ne Ikon Allah

Kristi Shi Ne Ikon Allah

Kristi ikon Allah.”1 KOR. 1:24.

1. Me ya sa Bulus ya ce “Kristi ikon Allah” ne?

JEHOBAH ya yi amfani da Yesu don ya nuna ikonsa a hanyoyi masu ban al’ajabi. Labaran Linjila guda huɗu sun ba da bayanai game da wasu mu’ujizai da Kristi ya yi da suka ƙarfafa bangaskiyarmu. Ban da waɗannan, wataƙila ya yi wasu mu’ujizai da yawa. (Mat. 9:35; Luk. 9:11) Hakika, Allah ya ba Yesu iko sosai, shi ya sa manzo Bulus ya ce game da shi: “Kristi ikon Allah.” (1 Kor. 1:24) Duk da haka, ta yaya mu’ujizojin Yesu za su iya shafan mu?

2. Mene ne za mu iya koya daga mu’ujizojin da Yesu ya yi?

2 Manzo Bitrus ya ce Yesu ya yi mu’ujizai ko kuma “al’ajibai.” (A. M. 2:22) Ayyuka masu ban al’ajabi da Yesu ya yi a duniya suna nuna abin da zai yi a sarautarsa na shekara dubu. A lokacin, zai yi mu’ujizai da suka fi waɗanda ya yi sa’ad da yake duniya! Mu’ujizojin da ya yi sun sa mun fahimci halinsa da kuma na Ubansa. Bari mu tattauna wasu cikin mu’ujizojin da Yesu ya yi kuma mu ga yadda za su iya shafanmu a yanzu da kuma a nan gaba.

 DARASI DA ZA MU KOYA DAGA WATA MU’UJIZA GAME DA KARIMCI

3. (a) Ka kwatanta yanayin da ya sa Yesu ya yi mu’ujiza ta farko. (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai karimci ne a Kana?

3 Yesu ya yi mu’ujizarsa ta farko a wani bikin aure da aka yi a Kana na Galili. Wataƙila yawan mutane da suka zo bikin ya fi abin da aka zata, saboda haka ruwan inabin ya kasa. Maryamu, mahaifiyar Yesu tana cikin waɗanda suka zo bikin. Babu shakka, ta yi shekaru da yawa tana bimbini a kan dukan alkawura da aka yi game da ɗanta, wanda mala’ika ya gaya mata cewa za a ce da shi “Ɗan Maɗaukaki.” (Luk. 1:30-32; 2:52) Shin ta gaskata cewa yana da ikon yin mu’ujiza ne? A bayyane yake cewa Maryamu da Yesu sun ji tausayin ma’auratan kuma ba sa son su sha kunya. Yesu ya san cewa nuna karimci farilla ce, saboda haka, ya mai da wajen lita 380 na ruwa zuwa “ruwan anab mai-kyau.” (Karanta Yohanna 2:3, 6-11.) Shin wajibi ne Yesu ya yi wannan mu’ujizar? A’a. Ya yi hakan don yana ƙaunar mutane, kuma ta yin karimci, yana koyi da Ubansa na sama.

4, 5. (a) Wane darasi ne muka koya daga mu’ujiza ta farko da Yesu ya yi? (b) Mene ne mu’ujiza da aka yi a Kana ya koya mana game da nan gaba?

4 Wannan mu’ujiza da Yesu ya yi ya sa dukan mutanen sun sami isashen ruwan inabi. Wane darasi ne muka koya daga wannan mu’ujiza? Da yake Yesu ya yi wannan mu’ujiza mai ban al’ajabi da yardan rai kuma hakan ya tabbatar mana cewa shi da Ubansa sun damu da yadda mutane suke ji. Yesu da Ubansa ba masu maƙo ba ne. Hakan ya nuna cewa Jehobah zai yi amfani da ikonsa sosai a sabuwar duniya don ya yi tanadin abinci mai yawa ga “dukan al’ummai.”—Karanta Ishaya 25:6.

5 Ba da daɗewa ba za a biya dukan bukatunmu, kamar su abinci da gida mai kyau. Kowa zai sami abin da yake so. Bari tunanin waɗannan abubuwa masu kyau da Jehobah zai yi mana tanadinsu a Aljanna a duniya ya riƙa sa mu farin ciki.

Muna yin koyi da Yesu ta wajen nuna karimci sa’ad da muka ba da lokaci don taimaka wa mutane (Ka duba sakin layi na 6)

6. Yesu ya yi mu’ujiza don ya amfani wa, kuma yaya za mu yi koyi da shi?

6 Kristi ya ƙi yin amfani da ikonsa na yin mu’ujiza don biyan bukatunsa sa’ad da Iblis ya gaya masa ya mai da duwatsu zuwa gurasa. (Mat. 4:2-4) Amma ya yi amfani da ikonsa don ya biya bukatun wasu. Ta yaya za mu yi koyi da halin Yesu na karimci? Ya ƙarfafa bayin Allah su riƙa ‘bayarwa.’ (Luk. 6:38) Shin za mu nuna karimci ta wajen gayyatar wasu zuwa gidanmu don cin abinci tare kuma mu ƙarfafa juna? Shin bayan taro za mu iya ba da kanmu don taimaka wa wani da jawabinsa? Alal misali, za mu iya sauraronsa yayin da yake shirya yadda zai ba da jawabin. Yaya za mu taimaka wa  wasu su ƙware a yin wa’azi? Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa mutane kuma muka ƙarfafa dangantakarsu da Allah, muna nuna karimci kamar Yesu.

‘DUKANSU SUKA CI SUKA ƘOSHI’

7. Wane yanayi ne zai kasance muddin muna cikin wannan mugun zamani?

7 An daɗe ana fama da talauci. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa na dā cewa ba za a taɓa rasa talakawa a ƙasar ba. (K. Sha. 15:11) Bayan shekaru da yawa, Yesu ya ce: “Kuna da fakirai kullum tare da ku.” (Mat. 26:11) Shin Yesu yana nufin cewa talakawa ba za su taɓa ƙarewa a duniya ba ne? A’a, yana nufin cewa muddin muna cikin wannan mugun zamani, za a ci gaba da samun talakawa. Amma, muna farin cikin sanin cewa mu’ujizojin da Yesu ya yi suna nuna abubuwa masu kyau da za mu more a Mulkinsa, sa’ad da kowa zai sami isashen abinci.

8, 9. (a) Me ya sa Yesu ya ciyar da dubban mutane? (b) Mene ne ya burge ka game da wannan mu’ujizar?

8 Marubucin zabura ya ce game da Jehobah: “Kana buɗe hannunka, kana biya wa kowane mai-rai muradinsa.” (Zab. 145:16) Da yake “Kristi ikon Allah” ne, ya yi koyi da Ubansa sa’ad da yake duniya ta wajen biyan bukatun mabiyansa a kai a kai. Bai yi hakan kawai don ya nuna cewa yana da iko ba, amma don ya damu da mutane. Bari mu tattauna Matta 14:14-21. (Karanta.) Almajiran Yesu sun zo su tattauna da shi don wataƙila suna jin yunwa kuma sun damu cewa mutane da suka biyo shi da ƙafa daga birane sun gaji saboda haka su ma suna jin yunwa. (Mat. 14:13) Mene ne zai yi?

9 Yesu ya yi amfani da gurasa guda biyar da kifi biyu don ya ciyar da maza 5,000 da mata da kuma yara! Yadda Yesu ya yi amfani da ikonsa na yin mu’ujiza don ya kula da dukan iyalai har da yara yana ƙarfafa mu, ko ba haka ba? Mutanen “suka ci, suka ƙoshi.” Hakan ya nuna cewa Yesu ya yi musu tanadin isashen abinci kuma hakan ya ba su ƙarfin yin doguwar tafiya sa’ad da suke komawa gidajensu. (Luk. 9:10-17) Bayan haka, abincin da ya rage ya cika kwanduna goma sha biyu!

10. A nan gaba, mene ne zai faru da talauci?

10 A yau, miliyoyin mutane ba sa samun biyan bukata don rashin adalci na gwamnati. Har wasu cikin ’yan’uwanmu ba sa samun isashen abinci su ci su “ƙoshi.” Amma, nan ba da daɗewa ba, ’yan Adam masu biyayya za su yi rayuwa a duniya da ba a cin hanci kuma babu talauci. Idan kana da ikon biyan bukatun ’yan Adam, shin ba za ka yi hakan ba? Allah maɗaukaki yana da iko da kuma niyyar yin hakan. Hakika, nan ba da daɗewa za a daina talauci!—Karanta Zabura 72:16.

11. Me ya ba ka tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba Kristi zai yi amfani da ikonsa don ya taimaka wa mutane a dukan duniya, mene ne sanin hakan yake motsa ka ka yi?

11 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi mu’ujizai a ƙaramin yanki ne kawai na shekara uku da rabi. (Mat. 15:24) A matsayinsa na Sarki mai ɗaukaka, zai yi sarauta har zuwa iyakar duniya. (Zab. 72:8) Mu’ujizojin da Yesu ya yi, ya sa mun kasance da tabbaci cewa zai yi amfani da ikonsa ya taimaka mana. Ko da yake ba za mu iya yin mu’ujizai ba, za mu iya gaya wa mutane game da alkawura masu kyau da Allah ya yi game da nan gaba. Da yake mu Shaidun Jehobah ne kuma muna da wannan masaniya game  da nan gaba, hakkinmu ne mu sanar da mutane. (Rom. 1:14, 15) Yin bimbini a kan waɗannan alkawura zai sa mu yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah.—Zab. 45:1; 49:3.

JEHOBAH DA YESU SUNA SARRAFA YANAYI

12. Me ya sa muka kasance da tabbaci cewa Yesu ya fahimci yanayi sosai?

12 Yesu Ɗan Allah makaɗaici yana tare da Jehobah a matsayinsa na “gwanin mai-aiki,” sa’ad da ya halicci duniya da dukan abubuwa da ke cikinta. (Mis. 8:22, 30, 31; Kol. 1:15-17) Saboda haka, Yesu ya fahimci yanayi sosai. Ya san yadda zai yi amfani da kuma sarrafa albarkatun duniya.

Mene ne yake burge ka game da yadda Yesu ya yi mu’ujizai? (Ka duba sakin layi na 13 da 14)

13, 14. Ka ba da misalin da ya nuna cewa Kristi yana da iko bisa yanayi.

13 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa shi ne “Ikon Allah” ta wajen sarrafa yanayi. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya dakatar da hadari mai iska da ya tsoratar da almajiransa. (Karanta Markus 4:37-39.) Wani masanin Littafi Mai Tsaki ya ce: “Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan tana nufin wata mahaukaciyar guguwa, ba iska kawai ba . . . amma babban hadari da iska da ruwa da ke ɓarna sosai.” Labarin Matta ya yi maganar wannan babban hadari.—Mat. 8:24.

14 Ka yi tunanin wannan yanayin: Kristi ya gaji tikis don aiki tuƙuru da ya yi a wa’azi, kuma ya soma barci a cikin kwalekwale sai ga igiyar ruwan yana bugun kwalekwalen kuma ruwa yana shiga ciki. Duk da wannan hayaniyar, Yesu ya ci gaba da barci don yana bukatar hutu. Almijiran sun tsorata, sai suka ta da Yesu daga barci suka ce masa za su “hallaka.” (Mat. 8:25) Da Yesu ya tashi sai ya tsawata wa iskar da kuma tekun ya ce: “Ka natsu, ka yi shiru,” sai iskar ta kwanta. (Mar. 4:39) Yesu ya ba iskar da kuma tekun umurni su yi shuru sai sun tsaya cak. Mene ne sakamakon? “Babbar natsuwa ta samu.” Hakika, Yesu yana da ikon sarrafa yanayi!

15. Ta yaya Allah Maɗaukakin Sarki ya nuna cewa shi mai sarrafa yanayi ne?

15 Jehobah ne ya ba Kristi wannan iko, saboda haka muna da tabbacin cewa Allah maɗaukaki zai iya sarrafa yanayi. Alal misali, kafin a yi Rigyawa Jehobah ya ce: “Sauran kwana bakwai, kāna zan sa a yi ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in.” (Far. 7:4) Hakazalika, Fitowa 14:21 ta ce: “Ubangiji kuma ya sa teku ya koma baya saboda iskan gabas mai-ƙarfi.” Ƙari ga haka, Yunana 1:4, ta ce: “Ubangiji ya aike da babban iska cikin teku, babban hadari kuwa ya tashi a teku, har jirgin yana bakin fashewa.” Sanin cewa Jehobah yana da iko bisa yanayi yana ƙarfafa mu. Hakika a sabuwar duniya Jehobah zai ci gaba da sarrafa yanayi a hanyar da ta dace.

16. Me ya sa sanin cewa Mahaliccinmu da Ɗansa na fari suna da ikon sarrafa yanayi yake ƙarfafa mu?

16 Yin tunanin irin ikon Mahaliccinmu da kuma Kristi, “gwanin mai-aiki” yana da ban ƙarfafa. Dukan mutane za su kasance da kwanciyar hankali sa’ad da Jehobah da Yesu suka soma nuna ikonsu bisa yanayin duniya a lokacin sarautar Kristi na shekara dubu. Ba za a ƙara yin bala’i da ke tsoratar da mutane ba. Ba za mu ji tsoron mahaukaciyar guguwa da tsunami da dutsen da ke aman wuta ko kuma girgizar ƙasa a sabuwar duniya ba. Za mu yi farin cikin yin tunanin lokacin da bala’i ba zai kashe ko kuma gurgunta kowa ba don “mazaunin  Allah [zai kasance] wurin mutane.” (R. Yoh. 21:3, 4) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ba Kristi ikon sarrafa yanayin mahalli a lokacin Sarautarsa na Shekara Dubu.

KA YI KOYI DA ALLAH DA KRISTI YANZU

17. A wace hanya ce za mu iya yin koyi da Allah da kuma Kristi a yanzu?

17 Hakika, ba za mu iya sa a daina bala’i ba kamar Jehobah da Yesu, amma Allah ya ba mu iko madaidaici. Ta yaya muke amfani da ikon? Hanya ɗaya ita ce ta bin ƙa’idar da ke Misalai 3:27. (Karanta.) Sa’ad da ’yan’uwanmu suka fuskanci mawuyacin hali, muna iya biyan bukatunsu kuma mu ƙarfafa dangantakarsu da Allah. (Mis. 17:17) Alal misali, muna iya taimaka musu bayan an yi wani bala’i. Wata gwauruwa da iska mai ƙarfin gaske ya ɓata gidanta ta ce: “Ina farin ciki matuƙa cewa ina cikin ƙungiyar Jehobah, ba don kawai an biya bukatuna ba amma don ƙarfafa da nake samu daga Kalmar Allah.” Wata ’yar’uwa marar aure da mahaukaciyar guguwa ta ɓata gidanta ta karaya kuma ta rikice, amma bayan da ’yan’uwa suka taimaka mata suka gina gidanta, sai ta ce: “Ina farin ciki matuƙa . . . Na gode maka Jehobah!” Muna farin ciki cewa muna cikin ƙungiyar da ’yan’uwa suke taimaka wa juna. Ƙari ga haka, muna godiya cewa Jehobah da Yesu Kristi suna kula da bayin Allah.

18. Mene ne ya burge ka game da dalilin da ya sa Yesu ya yi mu’ujizai?

18 A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ya nuna cewa shi ne “ikon Allah.” Amma bai yi amfani da ikonsa don ya burge wasu ko kuma ya amfani kansa ba. Maimakon haka, Yesu ya yi mu’ujizai domin yana ƙaunar mutane sosai. Za mu ƙara koya game da hakan a talifi na gaba.