“Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.”—1 BIT. 2:21.

1. Me ya sa yin koyi da Yesu zai sa mu kusaci Jehobah?

MUKAN so mu zama kamar mutanen da suke burge mu. A cikin duk mutanen da suka taɓa rayuwa a duniya, ba wanda ya cancanci mu yi koyi da shi kamar Yesu Kristi. Me ya sa? Shi da kansa ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yoh. 14:9) Yesu ya koyi halayen Ubansa sosai shi ya sa duk wanda ya lura da Yesu kamar yana ganin Ubansa. Saboda haka, idan muka yi koyi da Yesu, za mu kusaci Jehobah, Mai iko duka. Wannan babbar albarka ce ga waɗanda suka bi gurbin ɗan Allah!

2, 3. (a) Me ya sa Jehobah ya tanadar mana da tarihin Ɗansa, kuma mene ne Jehobah yake so mu yi? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma a na gaba?

2 Shin ta yaya za mu san halin Yesu? Abin farin ciki shi ne muna da hurarren tarihin Yesu. Jehobah ya tanadar mana da rubutaccen tarihin Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki don yana son mu san Ɗansa da kyau kuma mu yi koyi da shi. (Karanta 1 Bitrus 2:21.) A cikin Littafi Mai Tsarki an  kwatanta rayuwar Yesu da ‘sawu.’ Kamar dai Jehobah yana gaya mana mu bi sawu ko kuma gurbin Yesu. Yesu ya bar mana gurbi mai kyau ko da yake mu masu zunubi ne. Amma Jehobah bai ce lallai sai mun bi misalin Yesu sau-da-kafa ba. A maimakon haka, Ubanmu na sama yana so mu yi iya ƙoƙarinmu a bin misalin Ɗansa.

3 Bari mu tattauna wasu halayen Yesu. Za mu yi la’akari da tawali’unsa da kuma tausayinsa a wannan talifin, kuma a na gaba, za mu tattauna yadda ya kasance da ƙarfin zuciya da kuma basira. Za mu amsa tambayoyi uku a kan kowane hali: Mene ne ma’anar halin? Ta yaya Yesu ya nuna halin? Ta yaya za mu yi koyi da shi?

YESU MAI TAWALI’U NE

4. Mene ne tawali’u yake nufi?

4 Mene ne tawali’u? A wannan duniya da yawancin mutane suke girman kai, wasu za su ɗauka cewa tawali’u kasawa ne ko kuma rashin ƙarfin zuciya. Amma, a yawancin lokaci, ba haka ba ne. Nuna tawali’u na bukatar ƙarfin zuciya da gaba gaɗi. Tawali’u yana nufin “rashin fahariya da girman kai.” Idan muna so mu zama masu tawali’u muna bukata mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tawali’u yana nufin sanin yadda muka kasa a gaban Allah.” Idan mu masu tawali’u ne a gaban Allah, ba za mu riƙa ɗaukan kanmu da muhimmanci fiye da sauran mutane ba. (Rom. 12:3; Filib. 2:3) Kasancewa da tawali’u ba abu mai sauƙi ba ne ga ’yan Adam ajizai. Amma za mu iya zama masu tawali’u idan muka yi la’akari da matsayinmu a gaban Allah kuma muka bi misalin Ɗansa.

5, 6. (a) Wane ne Mika’ilu shugaban mala’ilu? (b) Ta yaya Mika’ilu ya nuna cewa shi mai tawali’u ne?

5 Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u? Ɗan Allah mai tawali’u ne tun yana sama a matsayin mala’ika mai iko da kuma sa’ad da ya zo duniya a matsayin ɗan Adam. Bari mu tattauna wasu misalai.

6 Halinsa. Yahuda, wani Marubucin Littafi Mai Tsarki ya rubuta wani misali game da rayuwar Yesu kafin ya zo duniya. (Karanta Yahuda 9.) A matsayin Mika’ilu shugaban mala’iku, Yesu ya yi jayyaya da kuma “gardama” da Iblis. Gardamar a kan “jikin Musa” ne. Ka tuna cewa sa’ad da Musa ya mutu, Jehobah ya binne gawar a wani wurin da ba a sani ba. (K. Sha. 34:5, 6) Wataƙila Shaiɗan yana so ya yi amfani da gawar Musa don ya sa mutane bautar ƙarya. Ko da mene ne aniyarsa, Mika’ilu ya yi tsayin daka da shi. Wani littafin bincike ya ce ana amfani da waɗannan kalaman “mahawara” da “gardama” a lokacin da “ake shari’a a kotu” kuma hakan yana iya nufin cewa “Mika’ilu ya ‘ƙalubalanci Shaiɗan’ game da gawar Musa.” Duk da haka, shugaban mala’iku ya san cewa ba shi da izinin zartar da hukunci. A maimakon haka, ya miƙa shari’ar ga Babban Alƙali, wato Jehobah. Ko da yake abin ya ɓata wa Mika’ilu rai, bai wuce gona da iri ba. Babu shakka, shi mai tawali’u ne!

7. Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u a furucinsa da kuma ayyukansa?

7 Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, furucinsa da ayyukansa sun nuna  cewa shi mai tawali’u ne da gaske. Furucinsa. Bai taɓa yin abu don mutane su ɗaukaka shi ba. A maimakon haka, ya miƙa dukan ɗaukaka ga Ubansa. (Mar. 10:17, 18; Yoh. 7:16) Bai taɓa raina almajiransa ko kuma yi wani abu da zai nuna cewa ya fi su ba. Akasin haka, ya ɗauke su da mutunci, ya yabe su don halaye masu kyau da suke da shi kuma ya nuna cewa ya amince da su. (Luk. 22:31, 32; Yoh. 1:47) Ayyukansa. Yesu ya yi rayuwa mai sauƙi kuma bai tara wa kansa abin duniya ba. (Mat. 8:20) Ya yi marmarin yin ayyukan da bayi suka saba yi. (Yoh. 13:3-15) Ya nuna cewa shi mai tawali’u ne da gaske a yadda ya yi biyayya. (Karanta Filibbiyawa 2:5-8.) Mutane masu fahariya ba sa son yin biyayya, amma Yesu ya ba da kansa ga yin nufin Allah kuma ya yi “biyayya har . . . mutuwa.” Hakika, Yesu, mutumi ne “mai-ƙasƙantar zuciya.”—Mat. 11:29.

KA ZAMA MAI TAWALI’U KAMAR YESU

8, 9. Ta yaya za mu nuna cewa mu masu tawali’u ne?

8 Ta yaya za mu nuna tawali’u kamar Yesu? A halinmu. Idan mu masu tawali’u ne, ba za mu wuce gona da iri a ikon da aka ba mu ba. Idan muka fahimci cewa ba mu da iko mu yanke hukunci a kan mutane, ba za mu yi saurin kushe su don laifuffukansu ba kuma ba za mu ɗauka cewa suna da mugun aniya ba. (Luk. 6:37; Yaƙ. 4:12) Tawali’u zai sa kada mu “cika yin adalci,” wato mu riƙa raina waɗanda ba su da baiwa ko kuma gatan da muke da su. (M. Wa. 7:16) Dattawa masu tawali’u ba sa ɗauka cewa sun fi sauran ’yan’uwansu masu bi. A maimakon haka, suna ɗaukan ‘wasu’ da mutunci kuma suna ganin kansu kamar bayi.—Filib. 2:3; Luk. 9:48.

9 Ka la’akari da  W. J. Thorn da ya yi hidima a matsayin mai kula mai ziyara daga shekara ta 1894. Bayan ya yi shekaru da yawa yana aikin, sai aka ce ya je aiki a wani gonar da ake kiwon kaji da ake kira Kingdom Farm a arewacin New York. Ya ce: “Duk lokacin da fahariya ta soma shiga zuciyata, nakan je gefe kuma in ce wa kaina: ‘Kai ɗan ƙwaro. Mene ne kake da shi da kake burga?’” (Karanta Ishaya 40:12-15.) Wannan halin mai tawali’u ne!

10. Ta yaya za mu nuna cewa mu masu tawali’u ne ta furucinmu da ayyukanmu?

10 Furucinmu. Idan mu masu tawali’u ne, yadda muke magana zai nuna hakan. (Luk. 6:45) Sa’ad da muke taɗi da wasu, ba za mu riƙa mai da hankali ga abubuwan da muka cim ma ba. (Mis. 27:2) A maimakon haka, za mu mai da hankali da halaye masu kyau na ’yan’uwanmu kuma mu yabe su don iyawarsu da kuma abubuwan da suka cim ma. (Mis. 15:23) Ayyukanmu. Kiristoci masu tawali’u ba sa neman suna a wannan zamanin. Sun fi so su yi rayuwa mai sauƙi, suna yin hakan don su sami damar bauta wa Jehobah da dukan ƙwazonsu ko da hakan yana nufin yin aikin da mutane ba sa ɗauka da muhimmanci. (1 Tim. 6:6, 8) Mafi muhimmanci, za mu iya nuna cewa mu masu tawali’u ne ta yin biyayya. Yin biyayya ga ‘waɗanda ke shugabanci,’ wato dattawa da bayi masu hidima da kuma bin umurnin ƙungiyar Jehobah yana  bukatar mu kasance da tawali’u.—Ibran. 13:17.

YESU MAI TAUSAYI NE

11. Mene ne tausayi?

11 Mene ne tausayi? Tausayi yana sa mutum ya nuna ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah da Yesu suna matuƙar tausayi da ƙauna. (Luk. 1:78; 2 Kor. 1:3; Filib. 1:8) Littafi Mai Tsarki ya ce mu zama masu tausayi, game da hakan wani littafin bincike ya yi bayani cewa: “Wannan umurnin ba wai yana nufin jin tausayin mabukata kawai ba, amma ya ƙunshi sanin yanayinsu da kuma ɗaukan mataki don inganta rayuwarsu.” Mutum mai tausayi yana saurin yin abin da ya dace don ya taimaka wa wasu.

12. Mene ne ya nuna cewa Yesu ya ji tausayin mutane, kuma mene ne tausayi ya motsa shi ya yi?

12 Ta yaya Yesu ya nuna tausayi? Ya ji tausayin mutane kuma ya ɗauki mataki. Sa’ad da ya ga abokiyarsa Maryamu da waɗanda ke tare da ita suna kuka don ɗan’uwanta Li’azaru ya mutu, Yesu “ya yi kuka” a fili. (Karanta Yohanna 11:32-35.) Bayan haka, tausayi ya motsa shi ya ta da Li’azaru daga matattu kamar yadda ya ta da ɗan wata gwauruwa. (Luk. 7:11-15; Yoh. 11:38-44) Ta wajen ɗaukan wannan matakin, mai yiwuwa Yesu ya ba wa Li’azaru begen zuwa sama. Kafin wannan lokacin, Yesu ‘ya yi juyayin’ wani taron mutane masu yawa da suka zo wajensa. Tausayi ya motsa shi kuma “ya fara koya masu abu da yawa.” (Mar. 6:34) Babu shakka, wanda ya bi koyarwar Yesu ya amfana sosai! Ka lura cewa tausayin da Yesu ya nuna ya motsa shi ya ɗauki mataki don ya taimaka wa mutane.—Mat. 15:32-38; 20:29-34; Mar. 1:40-42.

13. Ta yaya Yesu ya yi magana da tausayi? (Ka duba hoton da ke shafi na 5.)

13 Furucinsa da daɗin ji. Tausayi ya motsa Yesu ya yi furuci mai daɗi da zai ƙarfafa mutane, musamman matalauta. Manzo Matta ya ce wannan annabcin Ishaya ya cika a rayuwar Yesu: “Raunanan kara ba za ya karye shi ba, lagwani mai-hayaƙi ba za ya ɓice shi ba.” (Isha. 42:3; Mat. 12:20) Yesu ya yi magana a yadda zai ƙarfafa waɗanda suke kama da lagwanin da wutarsa ya kusan mutuwa, wato waɗanda suka raunana. Wa’azinsa ya sa “masu-karyayyen zuciya” su kasance da bege. (Isha. 61:1) Ya ce wa “masu-nauyin kaya” su zo gare shi kuma ya tabbatar musu cewa za su “sami hutawa.” (Mat. 11:28-30) Ya gaya wa mabiyansa cewa Allah yana jin tausayin kowane bawansa, har da “ƙanƙanana,” wato waɗanda mutanen duniya ba sa ganinsu da mutunci.—Mat. 18:12-14; Luk. 12:6, 7.

KA ZAMA MAI TAUSAYI KAMAR YESU

14. Ta yaya za mu nuna cewa muna jin tausayin mutane da gaske?

14 Ta yaya za mu zama masu tausayi kamar Yesu? Mu kasance masu tausayi. Nuna tausayi bai da sauƙi a wani lokaci, amma Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu yi ƙoƙari mu zama masu tausayi. “Tausayi” yana cikin sabon halin da aka ce Kiristoci su kasance da shi. (Karanta Kolosiyawa 3:9, 10, 12.) Ta yaya za ka iya nuna tausayi ga mutane? Ya kamata mu so mutane da zuciya ɗaya. (2 Kor. 6:11-13) Ka saurari mutum da kyau sa’ad da yake gaya maka damuwarsa. (Yaƙ. 1:19) Ka yi tunani kuma ka tambayi kanka: ‘Idan ni ne a yanayinsa, yaya zan ji? Yaya zan so a bi da ni?’—1 Bit. 3:8.

15. Ta yaya za mu iya taimaka wa waɗanda suke kama da lagwanin da wutarsa ya kusan mutuwa?

 15 Mu taimaka don tausayi. Tausayi ne yake motsa mu mu ɗauki mataki don mu inganta rayuwar mutane, musamman ma waɗanda suke kamar lagwanin da wutarsa ya kusan mutuwa. Ta yaya za mu taimaka musu? Littafin Romawa 12:15 ta ce: “Ku yi kuka tare da masu-kuka.” Waɗanda suke baƙin ciki suna bukatar ƙarfafa fiye da magani. Wata ’yar’uwa da ’yan’uwa suka ƙarfafa ta sa’ad da ta yi rashin ’yarta, ta ce: “Na sami ƙarfafa sa’ad da abokai suka zo suka yi kuka tare da ni.” Za mu kuma iya nuna tausayi ta wajen yin alheri. Ka san wata gwauruwa da ke bukata a yi mata gyara a gidanta? Shin akwai wani tsoho ko tsohuwa da ke bukatar taimako don zuwa taro ko wa’azi ko kuma zuwa wajen likita? Ko da wani ɗan alheri ne ka yi wa wani ɗan’uwa da ke da bukata, hakan zai inganta rayuwarsa sosai. (1 Yoh. 3:17, 18) Mafi muhimmanci, za mu iya nuna tausayi ta wajen yin wa’azi da ƙwazo sosai. Yin wa’azi shi ne hanya mafi kyau da za mu taimaka wa mutane masu son bauta wa Allah.

Shin ka damu da ’yan’uwanka masu bi da gaske? (Ka duba sakin layi na 15)

16. Mene ne za mu faɗa don mu ƙarfafa waɗanda suke baƙin ciki?

16 Mu yi magana mai daɗin ji. Idan muna tausayin mutane, za mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tas. 5:14) Mene ne za mu faɗa don mu ƙarfafa irin waɗannan masu baƙin ciki? Za mu iya ƙarfafa su ta wajen nuna cewa mun damu da su da gaske. Za mu iya yaba musu don mu taimaka musu su ga halayensu masu kyau. Za mu iya tuna musu cewa Jehobah ya jawo su zuwa wajen Ɗansa, saboda haka, suna da mutunci a gabansa. (Yoh. 6:44) Za mu iya tabbatar musu cewa Jehobah yana ƙaunar bayinsa “masu-karyayyar zuciya” ko kuma “ruhu mai-tuba.” (Zab. 34:18) Kalamanmu masu daɗin ji zai iya ƙarfafa masu baƙin ciki.—Mis. 16:24.

17, 18. (a) Yaya Jehobah yake so dattawa su bi da ’yan’uwa a cikin ikilisiya? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Dattawa, Jehobah ya umurce ku ku bi da ’yan’uwa cikin ƙauna. (A. M. 20:28, 29) Kada ku manta cewa ku ne ke da hakkin ciyar da, ƙarfafa da kuma wartsakar da tumakinsa. (Isha. 32:1, 2; 1 Bit. 5:2-4) Saboda haka, dattijo da ke da tausayi ba ya tilasta wa tumakin ta wajen kafa dokoki ko kuma ya sa su ji cewa laifi ne idan ba su yi wani abin ba, alhali abin ya fi ƙarfinsu. A maimakon haka, yana yunkurin sa su farin ciki kuma ya amince suna yi iya ƙoƙarinsu su bauta wa Jehobah don suna ƙaunar sa.—Mat. 22:37.

18 Yayin da muke la’akari da tawali’u da kuma tausayi da Yesu ya nuna, babu shakka hakan zai motsa mu mu ci gaba da bin gurbinsa. A talifi na gaba, za mu tattauna ƙarin halaye guda biyu na Yesu, wato ƙarfin zuciya da basira.