BABU aikin da ya kai wa’azin bishara muhimmanci a duniya yanzu. Babu shakka, a matsayinka na Mashaidin Jehobah, wannan hidimar tana da daraja sosai a gare ka. A wasu lokatai majagaba da masu shela suna fuskantar ƙalubale da zai iya sa su sanyin gwiwa a wa’azi.

Mene ne zai taimaka maka ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo?

Wasu masu shela ba sa yawan samun waɗanda za su tattauna da su sa’ad da suke wa’azi gida-gida. Hakika, ba a yawan samun yawancin mutane a gida. Idan ma aka sami mutane a gida, wasunsu ba sa son su saurari bishara. Akasin haka, yankin wasu masu shela yana da girma sosai kuma mutane suna sauraron wa’azi, amma masu shelan suna gani cewa ba za su iya yin wa’azi a dukan yankin ba. Ban da hakan, akwai wasu ’yan’uwa a ikilisiya sun yi shekaru da dama suna wa’azi kuma ba su zata cewa za su riƙa yin wa’azi har zuwa wannan lokacin ba. Saboda haka, sun yi sanyin gwiwa.

Bai kamata mu yi mamaki cewa dukan bayin Jehobah suna fuskantar ƙalubale da suke sa su sanyin gwiwa a wa’azi ba. Me ya sa? Don mun san cewa za mu fuskanci ƙalubale a yin wa’azin bishara da ke cetar da mutane a wannan duniyar da ‘Shaiɗan’ Iblis yake mulki.—1 Yoh. 5:19.

Ko da waɗanne irin matsaloli ne kake fuskanta a wa’azi, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimake ka ka shawo kansu. To, mene ne ya kamata ka yi don ka kasance da ƙwazo a wa’azi? Bari mu duba waɗannan shawarwarin da ke gaba.

KA TAIMAKA WA WAƊANDA BA SU ƘWARE SOSAI BA

Kowace shekara, dubban mutane suna yin baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Idan ba ka daɗe da yin baftisma ba, ’yan’uwa da suka daɗe suna wa’azi za su taimaka maka ka ƙware. Idan ka daɗe da yin baftisma, sababbi za su amfana sosai idan ka horar da su kuma za ka sami albarka.

 Yesu ya san cewa almajiransa suna bukatar ja-gora don su iya yin wa’azi da kyau, kuma ya nuna musu yadda za su yi aikin. (Luk. 8:1) A yau ma, ana bukatar koyar da wasu don su ƙware a yin wa’azi.

Bai kamata mu ɗauka cewa sababbin masu shela za su ƙware idan suna fita wa’azi kawai ba. Suna bukatar wanda zai horar da su cikin alheri da ƙauna. Waɗanne abubuwa ne za a iya koya wa mai shela da bai ƙware ba? Waɗannan abubuwan sun ƙunshi (1) shirya da kuma gwada yadda za a yi wa’azi, (2) yadda zai ci gaba da tattaunawa da masu gida ko wani mai wucewa, (3) yadda zai ba da littattafai, (4) yadda zai koma don ya ziyarci mutane da kuma, (5) yadda zai soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Idan wanda aka horar ya mai da hankali kuma ya yi koyi da wanda yake taimakonsa, wataƙila a sami amfani mai kyau. (Luk. 6:40) Sabon mai shela zai ji daɗi idan yana tare da wanda zai saurare shi kuma ya taimaka masa idan da bukata. Ƙari ga haka, mai shelan zai ji daɗi idan ana yaba masa kuma ana ba shi shawara don ya ƙware.—M. Wa. 4:9, 10.

KA RIƘA HIRA DA WANDA KUKE WA’AZI TARE

A wasu lokatai, ban da hirar da kake yi da abokin wa’azinka, ba ka jin daɗin wa’azi don babu mutane ko kuma ba sa son sauraro duk da cewa kana yunkurin yi musu wa’azi. Ka tuna cewa Yesu ya tura almajiransa wa’azi “biyu biyu.” (Luk. 10:1) Suna iya ƙarfafa juna yayin da suke wa’azi tare. Saboda haka, yin wa’azi tare da wani ɗan’uwa yana ba mu zarafin ƙarfafa ‘bangaskiyar juna.’—Rom. 1:12.

Waɗanne abubuwa ne za mu iya magana a kai? Akwai wani abu mai ban ƙarfafa da ya faru da kai ko abokin wa’azinka a kwanan nan? Shin ka koyi wani abu a nazari da kake ki ko kuma a nazari na iyali? Shin akwai wani abu da ka ji a taro da ya ƙarfafa ka? A wasu lokatai, abokin wa’azinka ba wanda ka saba yin wa’azi da shi ba. Ka san yadda ya zama Mashaidin Jehobah kuwa? Mene ne ya tabbatar masa cewa Jehobah ne yake yi wa wannan ƙungiyar ja-gora? Wane ayyuka ne ya yi? Za ka iya gaya masa wasu abubuwa game da hidimarka a bautar Jehobah. Ko da wane irin sakamako ne ka samu a wa’azi, kasancewa da abokin wa’azi zai ba wa kai da abokin wa’azinka damar ƙarfafa “juna.”—1 Tas. 5:11.

KADA KA FASA YIN NAZARI A KAI A KAI

Idan muna son mu ci gaba da ƙwazo a wa’azi, bai kamata mu fasa yin nazari a kai a kai ba. “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana wallafa  abubuwa da yawa a kan batutuwa dabam-dabam. (Mat. 24:45) Saboda haka, muna da batutuwa da dama da za mu iya yin nazarinsu don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Bari mu yi la’akari da wani batu da za mu iya yin nazarinsa: Me ya sa yin wa’azi yake da muhimmanci sosai? Akwatin da ke shafi na 16 ya ambata wasu dalilai.

Yin la’akari da waɗannan dalilan zai taimaka maka ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo. Za ka iya yin nazari don ka bincika ƙarin dalilan yin wa’azi da ƙwazo. Bayan haka, sai ka yi bimbini a kan dalilan da kuma nassosi da suka goyi bayan haka. Babu shakka, yin irin wannan binciken zai taimaka maka ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo.

KA RIƘA BIN SHAWARWARI

Ƙungiyar Jehobah tana tanadar mana da shawarwari kullum don mu inganta yadda muke yin wa’azi. Ban da wa’azi gida-gida, za mu iya yin wa’azi ta wasiƙu da ta tarho ko a titi ko kuma inda jama’a suke da yawa. Ƙari ga haka, za mu iya yin wa’azi inda muka sami zarafi da kuma a wuraren kasuwanci. Za mu iya tsara ayyukanmu don mu je wa’azi a yankunan da ba a yawan wa’azi.

Kana bin waɗannan shawarwarin kuwa? Shin kana ƙoƙari ka yi amfani da wasu cikinsu kuwa? ’Yan’uwa da yawa da suka yi hakan sun sami sakamako mai kyau. Bari mu bincika misalai uku.

Misali na farko ya ƙunshi wata shawara da aka bayar a wasu talifofin Hidimarmu ta Mulki a kan yadda za mu soma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan shawarwarin sun taimaka wa wata ’yar’uwa mai suna April ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da abokan aikinta guda uku. Ta yi farin ciki sa’ad da waɗannan abokan aikinta  guda uku suka amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma suka soma zuwa taro.

Misali na biyu ya shafi ba da mujallunmu. An ƙarfafa mu mu nemi mutanen da wataƙila za su so wasu talifofi da ke cikin mujallunmu. Wani mai kula da da’ira da yake ƙasar Amirka ya ce ya rarraba wata fitowar mujallar Awake! game da tayoyi ga wasu manajojin manyan shaguna da ake sayar da tayoyi a wani yanki. Shi da matarsa sun rarraba wata mujalla mai jigo: “Understanding Your Doctor” (Yadda Za Ka Fahimci Likitarka) a ofisoshin likitoci fiye da ɗari da ke da’irar. Ya ce: “Irin wannan ziyarar hanya ce mai kyau na gabatar da kanmu da kuma littattafanmu. Bayan da mutanen suka zama abokanmu, sai muka soma ziyararsu su a kai a kai.”

Misali na uku ya ƙunshi yin wa’azi ta tarho. Wata ’yar’uwa mai suna Judy ta rubuta wasiƙa zuwa babban hedkwatarmu don ta nuna godiya ga shawarar da aka bayar game da yin wa’azi ta tarho. Ta ba da rahoto cewa, mahaifiyarta mai shekara 86 da take ciwo tana wa’azi kullum ta tarho kuma tana farin ciki don nazarin Littafi Mai Tsarki da take gudanarwa da wata ’yar shekara 92.

Shawarwari da aka bayar a littattafanmu suna da amfani sosai. Zai dace ka yi amfani da su. Za su taimake ka ka ci gaba da farin ciki da ƙwazo a wa’azi.

KA KAFA MAƘASUDAI DA ZA KA IYA CIM MA

Ba yawan littattafai da muke bayarwa ko yawan waɗanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su ko kuma yawan mutanen da muka taimaka musu su zama Shaidun Jehobah ba ne zai nuna cewa muna yin nasara a hidimarmu. Alal misali, Nuhu ya yi nasara a wa’azi duk da cewa babu wanda ya saurare shi ban da matarsa da ’ya’yansa da kuma matansu. Abin da ya fi muhimmanci shi ne bauta wa Jehobah da aminci.—1 Kor. 4:2.

Masu shela da yawa sun gano cewa idan suna so su ci gaba da wa’azi da ƙwazo, suna bukata su kafa makasudai masu kyau da za su iya cim ma. Waɗanne irin makasudai ke nan? An ambaci wasu a akwatin da ke shafin nan.

Ka nemi hanyoyi da za ka inganta hidimarka da taimakon Jehobah. Idan ka cim ma makasudanka, za ka yi farin ciki kuma ka sami gamsuwa cewa kana iya ƙoƙarinka don ka yi wa’azin bishara.

Babu shakka, yin wa’azi yana da ƙalubale. Duk da haka, akwai wasu abubuwa da za ka iya yi da za su taimaka maka ka zama mai wa’azin Mulki da ƙwazo. Ka riƙa yin hira da abokin wa’azinka, ka ci gaba da yin nazari a kai a kai, ka bi shawarwarin bawa mai aminci kuma ka kafa makasudai da za ka iya cim ma. Gaba da kome, ka tuna cewa Jehobah ya ba ka babban gata na yin wa’azi a matsayin Mashaidin Jehobah. (Isha. 43:10) Za ka yi farin ciki sosai idan ka ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo.