Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Janairu 2015

Ƙauna ta Gaskiya Za Ta Yiwu Kuwa?

Ƙauna ta Gaskiya Za Ta Yiwu Kuwa?

“[Ƙaunar] harshen wuta ne, harshen wuta mai-tsanani na Ubangiji.”W. WAƘ. 8:6.

1, 2. Su wa za su amfana daga bincika littafin Waƙar Waƙoƙi, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

WANI dattijo da ya gama ba da jawabin aure ya lura da yadda amaryar da angon suke kallon juna da kuma yadda suka riƙe juna. Sai ya amince cewa suna matuƙar son juna. Yayin da ma’auratan suke rawa a wurin da ake bikin, sai ya soma tunani ko soyayyarsu za ta dawwama. Wata tambaya da ta zo zuciyarsa ita ce, shin waɗannan ma’aurata za su ci gaba da son juna ne, ko kuma ƙaunarsu za ta riƙa raguwa da sannu-sannu da shigewar lokacin? Idan mata da miji suna son juna da gaske, za su ji daɗin aurensu. Da yake ma’aurata da yawa suna rabuwa da juna, ba abin mamaki ba ne mu yi tunani ko ƙauna ta gaskiya za ta yiwu.

2 A zamanin Sarki Sulemanu ta Isra’ila ta dā, ma’aurata da yawa ba sa ƙaunar juna da gaske. Sulemanu ya yi magana game da halin mutanen zamaninsa, ya ce: “Namiji guda cikin dubu na samu; amma mace guda ban samu ba cikin waɗannan duka. Duba! Wannan kaɗai na iske: Allah ya yi mutum kafaffe sosai; amma suna ta biɗe-biɗe da yawa.” (M. Wa. 7:26-29) Da yake mata daga al’ummai  da suke bauta wa Ba’al suna zama tsakaninsu, Isra’ilawa maza da mata da yawa ba su da ɗabi’u masu kyau. Amma, shekaru 20 kafin wannan lokacin, Sarki Sulemanu ya rubuta wata waƙa da ta nuna cewa soyayya tsakanin ta mace da namiji za ta iya dawwama. Ya kuma kwatanta ƙauna ta gaskiya da kuma yadda za a nuna ta. Ma’aurata da waɗanda ba su yi aure ba da suke bauta wa Jehobah za su koyi abubuwa da yawa game da soyayya ta wurin bincika wannan littafin Waƙar Waƙoƙi.

ƘAUNA TA GASKIYA ZA TA YIWU

3. Me ya sa soyayya ta gaskiya tsakanin tamace da namiji za ta yiwu?

3 Karanta Waƙar Waƙoƙi 8:6. Furucin nan ‘harshen wuta na Ubangiji’ da aka kwatanta ƙauna da shi yana da ma’ana sosai. Ƙauna ta gaskiya ita ce “harshen wuta . . . na Ubangiji” da yake Jehobah shi ne tushen ƙaunar. Ya halicce mu a cikin kamaninsa, wato a yadda za mu iya ƙaunar mutane. (Far. 1:26, 27) Sa’ad da Allah ya ba wa Adamu matarsa, wato Hauwa’u, Adamu ya yi farin ciki sosai kuma ya bayyana hakan. Babu shakka, Hauwa’u ita ma ta kusaci Adamu sosai domin daga cikinsa “aka ciro ta.” (Far. 2:21-23) Tun da yake Jehobah ya halicci ’yan Adam yadda za su so juna, zai yiwu soyayya da ke tsakanin namiji da tamace ta dawwama.

4, 5. Ka ɗan ba da labarin da ke littafin Waƙar Waƙoƙi.

4 Hakika, soyayya tsakanin namiji da tamace za ta iya dawwama amma akwai wasu abubuwa da ya kamata mu sani ban da haka. An kwatanta wasu cikin waɗannan a cikin littafin Waƙar Waƙoƙi. Waƙar wani labarin soyayya ce game da wata budurwa daga garin Shunem da saurayinta makiyayi. Budurwar tana kula da gonar inabi kusa da inda Sulemanu da sojojinsa suka ya da zango. Kuma Sulemanu yana bala’in sonta don ita kyakkyawa ce. Amma tun farko, a bayyane yake cewa tana soyayya da wani saurayi makiyayi. Yayin da Sulemanu yake ƙoƙari ya rinjaye ta, yarinyar kuma ta furta sarai cewa tana son ta kasance da saurayinta. (W. Waƙ. 1:4-14) Saurayin ya shiga cikin sansanin, sai suka bayyana yadda suke son juna.—W. Waƙ. 1:15-17.

5 Da Sulemanu ya koma Urushalima tare da wannan budurwar, sai makiyayin ma ya bi ta. (W. Waƙ. 4:1-5, 8, 9) Duk ƙoƙarin da Sulemanu ya yi don budurwar ta so shi ya ci tura. (W. Waƙ. 6:4-7; 7:1-10) Da ganin haka, sai sarkin ya bar ta ta koma gida. A ƙarshen waƙar, an ce budurwar tana son saurayinta ya “yi wasa kamar ’yar barewa” kuma ya zo da gudu ya same ta.—W. Waƙ. 8:14.

6. Me ya sa zai kasance da wuya a gane sunayen waɗanda aka ambata furucinsu a wannan labarin?

6 Waƙar Waƙoƙi waƙa ce mai daɗi, shi ya sa aka ƙira shi “Waƙar waƙoƙi.” Amma a cikin waƙarsa, Sulemanu bai ambaci sunayen mutane a lokacin da suke magana ba. (W. Waƙ. 1:1) Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce, “tsarin labarin da kuma sunayen waɗanda aka ambata furucinsu a labarin ba su ne ke da muhimmanci a waƙar ba.” Ya so mutane su ji daɗin waƙar maimakon mai da hankali ga mutanen da suka yi waƙar. Ko da yake waƙar ba ta ambaci sunayen waɗanda  suka yi ba, za a iya gane su ta furucinsu.

“ƘAUNARKA TA FI GABAN RUWAN ANAB”

7, 8. Mene ne za mu iya faɗa game da furucin soyayya da ke littafin Waƙar Waƙoƙi? Ka ba da misalai.

7 A cikin Waƙar Waƙoƙi, an rubuta yadda budurwa da saurayinta suka yi ta bayyana yadda suke ‘ƙaunar’ juna. Ko da yake furucinsu na ƙauna ya nuna abin da ya faru shekaru 3,000 da suka shige kuma al’adarsu ta bambanta da namu, duk da haka, waƙar tana da ma’ana sosai kuma za mu iya fahimtar yanayin. Alal misali, makiyayin ya kwatanta idanun budurwar da ‘na kurciya.’ (W. Waƙ. 1:15) Ita kuma ta ce idanunsa suna nan kamar kurciyoyi. (Karanta Waƙar Waƙoƙi 5:12.) Ta kwatanta ƙwayar idonsa da kurciya da take wanka da madara.

8 Ba dukan furucin ƙauna da aka yi a cikin waƙar ne yake magana game da kyaun siffa ba. Ka yi la’akari da abin da makiyayin ya faɗa game da furucin budurwar. (Karanta Waƙar Waƙoƙi 4:7, 11.) Leɓunanta suna zuba kamar saƙar “zuma.” Me ya sa? Don saƙar zuma ta fi zumar da ta sha iska daɗi. ‘Zuma da nono suna ƙarƙashin harshenta’ hakan yana nufin cewa furucinta yana da daɗin ji kamar zuma da madara. Makiyayin ya ce wa budurwar: “Kyakkyawa ce ke sosai . . . babu aibi a cikinki.” Sa’ad da ya faɗi hakan, ba kyan siffa kaɗai yake nufi ba.

9. (a) Mece ce soyayya da ke tsakanin mace da miji ta ƙunsa? (b) Me ya sa yake da muhimmancin ma’aurata su riƙa faɗa cewa suna ƙaunar juna?

9 Aure ba yarjejeniya ba ce kawai tsakani mata da miji. Ƙauna tana da muhimmanci a auren Kirista. Amma wace irin ƙauna ce wannan? Ƙauna ce da ke bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? (1 Yoh. 4:8) Wannan yana magana ne game da ƙauna da ke tsakanin ’yan’uwa daga iyali ɗaya? Hakan ya ƙunshi dangantaka da ke tsakanin abokai na kud da kud? (Yoh. 11:3) Soyayya ce tsakanin mace da miji? (Mis. 5:15-20) Hakika, soyayya tsakanin mace da miji ya ƙunshi dukan waɗannan. Ana sanin waɗanda suke ƙaunar juna ta yadda suke tattaunawa da kuma yadda suke bi da juna. Bai kamata harkokin yau da kullum su sa ma’aurata su daina bayyana ƙaunarsu ga juna ba. Irin waɗannan furucin za su sa mata da miji su sami kwanciyar hankali kuma su ji daɗin aurensu. A wuraren da iyaye suke zaɓa wa yaransu waɗanda za su aura kuma mata da miji ba sa sanin halin juna kafin ranar auren, furta yadda suke ƙaunar juna zai taimaka musu su ji daɗin zaman aurensu.

10. Ta yaya ma’aurata za su amfana idan suka tuna da kalaman soyayya da suke yi wa juna?

10 Idan ma’aurata suka bayyana ƙaunarsu ga juna, za su amfana a wata hanya har ila. Sarki Sulemanu ya ce zai yi wa budurwa Bashulammiya “tubkar zinariya tare da ado na azurfa.” Ya yabe ta sosai, ya ce ita “kyakyawa ce kamar wata, garai kamar rana.” (W. Waƙ. 1:9-11; 6:10) Amma budurwar ta kasance da aminci ga saurayinta. Mene ne ya ƙarfafa ta a lokacin da ba sa tare? Ta gaya mana dalilin. (Karanta Waƙar Waƙoƙi 1:2, 3.) Ta tuna da kalaman ‘ƙauna’ da saurayinta ke mata. Waɗannan kalaman  sun fi mata “ruwan anab” da ke sa mutum farin ciki, kuma sunan saurayinta yana kwantar mana da hankali kamar “man ƙamshi” da aka shafa a kai. (Zab. 23:5; 104:15) Hakika, tuna da kalaman ƙauna da ma’aurata suke yi wa juna zai sa su ci gaba da ƙaunar juna. Yana da muhimmanci ma’aurata su riƙa bayyana ƙaunarsu ga juna ta furucinsu a koyaushe.

KADA KU SOMA SOYAYYA SAI LOKACI YA YI

11. Wane darasi ne Kiristoci marasa aure za su koya daga rantsuwar da budurwa Bashulammiya ta sa wasu su yi?

11 Kiristoci marasa aure za su iya koyan darussa daga littafin Waƙar Waƙoƙi, musamman waɗanda suke neman aure. Wannan budurwar ba ta so Sulemanu ba. Ta sa ’yan matan Urushalima ransuwa cewa: “Kada ku ta da ƙauna, kada ku farkar da ita sai ta yarda.” (W. Waƙ. 2:7; 3:5) Me ya sa? Domin bai kamata mu kama son kowane mutum da ya zo neman mu ba. Ya kamata duk wani Kirista da yake son yin aure ya kasance da haƙuri kuma ya jira wanda ko wadda zai so ta da gaske.

12. Me ya sa budurwa Bashulammiya ta so saurayinta?

12 Me ya sa Bashulammiya ta so saurayinta makiyayi? A gaskiya, yana da kyau kuma ya yi kama da “barewa”; hannayensa suna da ƙarfi kamar “finjalin zinariya”; ƙafafunsa suna da kyau kamar “umudan marble.” Ba wai kawai yana da kyau da kuma ƙarfi ba. Saurayinta yana “kamar itacen apple a cikin itatuwan jeji” kuma “a ciki ’ya’ya maza.” Kafin yarinya mai aminci ga Jehobah ta ji haka game da saurayi, babu shakka wannan mutum yana da dangantaka mai kyau da Jehobah.—W. Waƙ. 2:3, 9; 5:14, 15.

13. Me ya sa makiyayin ya so budurwarsa?

13 Ita Bashulammiyar kuma fa? Ko da yake ita kyakkyawa ce da ta ja hankalin sarki da a lokacin yake da “sarauniya guda sittin, da ƙwaraƙwarai tamanin, budurwai kuma gaban lissafi,” ta ɗauki kanta a matsayin “furen rose na filin jejin Sharon.” Yarinyar mai tawali’u ce sosai. Shi ya sa a wurin saurayin tana da daraja kuma ya kwatanta ta da “furen lily cikin ƙayayuwa.” Ƙari ga haka, tana da aminci ga Jehobah.—W. Waƙ. 2:1, 2; 6:8.

14. Mene ne Kiristoci marasa aure da ke neman aure za su iya koya daga labarin soyayya da ke Waƙar Waƙoƙi?

 14 An shawarci Kiristoci a cikin Littafi Mai Tsarki su yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Ya kamata wanda yake neman aure ya guji yin soyayya da waɗanda ba Shaidu ba amma ya auri amintacce mai bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, kasancewa da salama da kuma haɗin kai a ibadarmu yayin da muke fuskantar matsalolin yau da kullum zai sa mu ji daɗin aurenmu. Amma hakan yana bukatar bangaskiya da kuma dangantaka mai kyau da Jehobah. Waɗannan sune halayen da ake bukata a wurin saurayi ko budurwa da ake nema da aure. Kuma irin waɗannan halayen ne makiyayi da Bashulammiya suke da shi.

Ya kamata Kiristoci su guji yin soyayya da waɗanda ba Shaidu ba (Ka duba sakin layi na 14)

BUDURWATA TANA KAMAR “SHIMGAGGIYAR GONA”

15. Ta yaya Bashulammiya ta kafa misali mai kyau ga Kiristoci da ba su yi aure ba?

15 Karanta Waƙar Waƙoƙi 4:12. Me ya sa makiyayi ya kwatanta budurwarsa da yake ƙauna da “shimgaggiyar gona”? Mutane ba za su iya shiga lambu da aka shinge ba. Za a iya shiga ta kofa ne kawai. Bashulammiya tana kama da wannan lambun don saurayinta ne kaɗai take so. Da yake ta ƙi sarki, ta kasance kamar “bango” ba “ƙofa” da ke buɗe ba. (W. Waƙ. 8:8-10) Hakazalika, ya kamata mata da maza da ba su yi aure ba su ƙuduri niyyar yin soyayya da wanda za su aura kaɗai.

16. Mene ne ka koya game da neman aure a littafin Waƙar Waƙoƙi?

16 A lokacin da makiyayi ya ce Bashulammiya su je yawo da rana, ’yan’uwanta ba su yarda mata ta je ba. Maimakon haka, sun ba ta aikin da za ta yi a lambu. Me ya sa? Shin ba su yarda da ita ba ne? Suna ganin cewa za ta je ta yi wani abin da ba kyau ne? Babu shakka, suna kāre ta ne don kada ta faɗa a yanayin da zai zama mata jaraba. (W. Waƙ. 1:6; 2:10-15) Ga darasin da Kiristocin marasa aure za su koya: Lokacin da suke fita zance ya kamata su mai da hankali don su kasance da ɗabi’a mai kyau. Su guji zama a inda ba mutane. Ko da yake ba laifi ba ne a riƙa furucin soyayya, duk da haka, ya kamata su guji yanayin da zai sa su cikin jaraba.

17, 18. Ta yaya ka amfana daga binciken littafin Waƙar Waƙoƙi?

17 Lokacin da Kiristoci suka yi aure sukan so juna sosai. Da yake Jehobah yana son aure ya dawwama, yana da muhimmanci ma’aurata su yi aiki tuƙuru don su ci gaba da ƙaunar juna.—Mar. 10:6-9.

18 Idan kana neman abokin aure, ya kamata ka nemi wanda za ka so da gaske kuma ka yi ƙoƙari ka inganta auren don ya dawwama kamar yadda littafin Waƙar Waƙoƙi ya nuna. Ko da kana neman aure ne ko kuma ka riga ka yi aure, za ka iya moran ƙauna ta gaskiya kamar “harshen wuta na Ubangiji.”—W. Waƙ. 8:6.