Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DAGA TARIHINMU

“Muna Kara Kwazo da Kauna Fiye da Dā”

“Muna Kara Kwazo da Kauna Fiye da Dā”

KO DA yake ana zafi sosai, a ranar Jumma’a ga watan Satumba ta shekara ta 1922, mutane 8,000 sun taru a wani babban daƙin taro. Mai kujera ya sanar cewa mutane za su iya fita idan suna so, amma ba za a yarda su shigo ba.

An soma taron da sashen da ’yan’uwa suke rera waƙoƙi, bayan haka sai ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya hau kan dakalin magana. Yawancin mutane sun zauna suna jiran abin da zai faru. Amma kaɗan daga cikinsu suna ta zagayawa don irin zafin da ake yi. Sai mai jawabin ya ce musu su zauna don su saurari jawabin. Shin da aka fara jawabin mutane sun ga labulen da aka rataye a sama ne?

Ɗan’uwa Rutherford ya yi jawabi a kan jigon nan “Mulkin sama ya kusa.” Ya yi awa ɗaya da rabi yana ba da jawabi da babbar murya a kan yadda annabawa suka yi wa’azi da gaba gaɗi game da Mulkin Allah. Da ya kusan kammala jawabin, sai ya ce, “Kun gaskata cewa Sarki na daraja ya soma sarauta?” Sai waɗanda suka halarci taron suka amsa da babbar murya suka ce: “E!”

Bayan haka, sai Ɗan’uwa Rutherford ya ce da babbar murya: “Sai ku koma fili, ya ku ’ya’yan Allah maɗaukaki!” Ya kuma ce: “Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar sarkin da kuma Mulkin.”

A wannan lokacin ne aka daga labulen kuma jama’a suka ga jigon nan: “Ku Yi Shelar Sarkin da Kuma Mulkin.”

Ray Bopp da yake wurin a lokacin ya ce: “Jama’a sun yi mamaki ba kaɗan ba.” Anna Gardner ta kwatanta abin da ya faru ta ce: “Jama’a sun yi tafi sosai har daƙin ya girgiza.” Fred Twarosh ya ce: “Dukan jama’a sun tashi tsaye.” Evangelos Scouffas ma ya ce: “Kamar wani abu ne ya dāga mu duka daga kan kujerunmu kuma muka tashi tsaye muna kukan murna.”

Yawancin jama’a da suka halarci taron suna yin wa’azin Mulkin Allah. Duk da haka, jawabin ya ƙarfafa su ci gaba da yin hakan. Ethel Bennecoff ta ce Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koma gidajensu da aniyar “ci gaba da wa’azi da kuma ƙaunar mutane da ƙwazo.” Odessa Tuck da a lokacin take da shekara 18 ta koma gida da aniyar ba da amsar tambayar da Jehobah ya yi cewa ‘Wa zan aika?’ Ta ce: “Ban san inda zan yi wa’azi ko yadda zan yi shi ko kuma abin da zan faɗa ba. Amma abin da na sani shi ne na so in zama kamar Ishaya wanda ya ce: ‘Ga ni; ka aike ni.’” (Isha. 6:⁠8) Ralph Leffler ya ce: “A wannan ranar ne aka soma shelar Mulkin sosai da ake yi a ko’ina a duniya yanzu.”

Babu shakka, shi ya sa ba za a taɓa mantawa da taron nan da aka yi a shekara ta 1922 a Cedar Point, Ohio a tarihin Shaidun Jehobah ba. George Gangas  ya ce: “Wannan taron ya taimaka mini in ga muhimmancin halartan manyan taro.” Kuma tun daga lokacin, yana ganin bai taɓa fasa halartan manyan taro ba. Julia Wilcox ta ce: “A duk lokacin da aka ambaci taron Cedar Point a shekara ta 1922 a littattafanmu, ina farin ciki sosai. A kullum ina cewa, ‘Na gode wa Jehobah don yadda ya sa na halarci wannan babban taron da aka yi.’”

Wataƙila mu ma muna da wasu manyan taron da muka halarta da ya motsa zuciyarmu kuma ya sa muka kasance da ƙwazon yin wa’azi da kuma ƙaunar Allahnmu da kuma Sarkinsa. Idan muna yin tunani a kan taron a kullum, mu ma za mu iya cewa, “Mun gode wa Jehobah don yadda ya sa muka halarci wannan babban taron da aka yi.”