“Ubangiji yana kiyayar da baƙi.”​—ZAB. 146:9.

WAƘOƘI: 84, 73

1, 2. (a) Waɗanne matsaloli ne wasu ’yan’uwanmu suke fuskanta? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

WANI ɗan’uwa mai suna Lije ya ce: “Muna wurin babban taronmu sa’ad da aka fara yaƙin basasa a ƙasar Burundi. Mun ga mutane suna ta gudu kuma ana ta harbi. Sai iyayenmu da mu yara sha ɗaya muka gudu, amma ba mu kwashi kaya da yawa ba. Wasu cikinmu sun yi gudun kilomita 1,600 kuma suka isa sansanin ’yan gudun hijira a Malawi. Amma sauranmu, kowa ya yi ta gabansa.”

2 A faɗin duniya, akwai ’yan gudun hijira fiye da miliyan 65 da suka bar gidajensu sanadiyyar yaƙi da tsanantawa kuma ba a taɓa yin irin wannan adadin ba a tarihin duniya. * A cikin su kuma akwai Shaidun Jehobah da yawa. Kuma sun yi asarar kusan dukan dukiyarsu, ban da haka ma, da yawa daga cikinsu ’yan’uwansu sun rasu. Waɗanne matsaloli ne wasu kuma suka fuskanta? Ta yaya za mu taimaka ma waɗannan ’yan’uwan su “bauta wa” Jehobah da farin ciki? (Zab. 100:⁠2) Ta yaya za mu yi ma ’yan gudun hijira wa’azi don su soma bauta wa Jehobah?

 YADDA ’YAN GUDUN HIJIRA SUKE RAYUWA

3. Ta yaya Yesu da almajiransa da yawa suka zama ’yan gudun hijira?

3 A lokacin da Yesu yake ƙarami, shi da iyayensa sun gudu sun je Masar bayan da mala’ikan Jehobah ya gaya musu cewa Sarki Hiridus yana son ya kashe Yesu. Sun zama baƙi a wurin har sai da Hiridus ya mutu. (Mat. 2:​13, 14, 19-21) Bayan wasu shekaru, almajiran Yesu ma sun warwatse zuwa “lardin Yahudiya da na Samariya” don tsanani. (A. M. 8:​1, Littafi Mai Tsarki) Kuma Yesu ya riga ya annabta cewa wasu cikin mabiyansa za su bar gidajensu saboda tsanantawa. Ya ce: “In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba.” (Mat. 10:23) Gudun hijira bai da sauƙi ko kaɗan.

4, 5. Waɗanne matsaloli ne ’yan gudun hijira suke fuskanta (a) sa’ad da suke gudu? (b) sa’ad da suke zama a sansani?

4 ’Yan gudun hijira za su iya fuskantar matsala sa’ad da suke gudu ko kuma sa’ad da suke zama a sansani. Ƙanen Lije mai suna Gad, ya ce: “A lokacin shekarana 12, kuma mun yi tafiyar makonni muna ta ganin gawawwaki a kan hanya. Da ƙafafuwa na suka kumbura don tafiyar, sai na gaya wa ’yan gidanmu ba zan iya tafiyar kuma ba. Sai mahaifina ya taimaka min, bai bar ’yan tawayen su ɗauke ni ba. A kowace rana muna addu’a ga Jehobah kuma mun dogara gare shi don a wasu lokuta mangwaro kawai da muka samu a hanya shi ne abincinmu.”​—Filib. 4:​12, 13.

5 Yawancin ’yan iyalin Lije sun yi shekaru a sansanin Majalisar Ɗinkin Duniya. Duk da haka, sun fuskanci matsaloli da yawa. Ɗan’uwa Lije da yake hidimar mai kula da da’ira yanzu, ya ce: “Yawancin mutanen ba su da aikin yi. Don haka, sai su riƙa gulma da shaye-shaye da caca da sata da kuma halin rashin da’a.” ’Yan’uwa suna bukata su shagala da ayyukan ibada idan suna son su guji irin waɗannan halayen. (Ibran. 6:​11, 12; 10:​24, 25) Wasu sun soma hidimar majagaba don su riƙa ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Kamar yadda Jehobah ya taimaka wa Isra’ilawa kuma bai bar su har abada a jeji ba. Su ma ba su damu ainun ba domin sun san cewa ba za su zauna a sansanin har abada ba.​—2 Kor. 4:18.

NUNA WA ’YAN GUDUN HIJIRA ƘAUNA

6, 7. (a) Ta yaya “ƙaunar” da muke wa Allah za ta sa mu taimaka wa ’yan’uwa da suke shan wahala? (b) Ka ba da misali.

6 “Ƙaunar” da muke wa Allah ne take sa mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu sa’ad da suke shan wahala. (Karanta 1 Yohanna 3:​17, 18.) A lokacin da yunwa ta addabi Kiristoci na ƙarni na farko a Yahudiya, ikilisiyar ta shirya yadda za a taimaka musu. (A. M. 11:​28, 29) Manzo Bulus da Bitrus ma sun ƙarfafa Kiristoci su riƙa taimaka wa juna. (Rom. 12:13; 1 Bit. 4:⁠9) Da yake an ƙarfafa Kiristoci su riƙa taimaka wa ’yan’uwa baƙi, to, zai yi kyau mu riƙa taimaka wa ’yan’uwanmu ’yan gudun hijira ko kuma waɗanda ake tsananta musu, ko ba haka ba?​—Karanta Misalai 3:27. *

7 Kwanan nan, Shaidun Jehobah da yawa da suka ƙunshi maza da mata da yara sun gudu don yaƙi da kuma tsanantawa da ake musu a gabashin Yukiren. Abin baƙin ciki shi ne, an kashe wasu cikinsu. Amma ’yan’uwanmu sun taimaka wa yawancinsu kuma suka kai su gidajensu a wani wuri a Yukiren. Wasu ’yan’uwanmu da ke ƙasar Rasha kuma suka kai wasunsu zuwa gidajensu don su zauna da su. A waɗannan ƙasashe biyu da suka je, ba sa saka hannu a siyasa don su “ba na duniya ba ne,” kuma sun ci gaba da “wa’azin kalmar” da ƙwazo.​—Yoh. 15:19; A. M. 8:4.

 KU TAIMAKA WA ’YAN GUDUN HIJIRA SU ƘARFAFA BANGASKIYARSU

8, 9. (a) Waɗanne irin matsaloli ne ’yan gudun hijira suke fuskanta a ƙasashen da suka je? (b) Me ya sa suke bukatar taimakonmu?

8 Wasu mutane sun ƙaura zuwa wasu garuruwa, wasu da yawa kuma sun ƙaura zuwa wasu ƙasashe dabam don yaƙi ko tsanani. Ko da yake gwamnati za ta iya tanadar ma ’yan gudun hijirar abinci da tufafi da wurin kwana amma wataƙila ’yan gudun hijirar ba su san irin abincin da ake ci a wurin ba. Kuma waɗanda suka fito daga wuraren da ake zafi ba za su iya sanin tufafin da ya kamata su saka ba a wurin da ake sanyi. Idan kuma sun fito daga ƙauye ne, zai yi musu wuya su yi amfani da kayan zamani.

9 Wasu ƙasashe suna da wasu ƙungiyoyin da suke taimaka wa ’yan gudun hijira don su iya rayuwa a wurin da suka sami kansu. Amma za a bukaci masu gudun hijira su nemi abin da za su yi don su kula da kansu bayan wasu watanni. Canjin yanayin bai da sauƙi ko kaɗan. Koyan abubuwa da yawa a lokaci ɗaya, kamar koyon wani yare da dokoki da hali da yin abu a kan lokaci da biyan haraji da neman kuɗin magani ko wuta da zuwa makaranta da yin renon yara ba sauƙi! Shin za ka iya taimaka wa ’yan’uwa da suke cikin irin wannan yanayin?​—⁠Filib. 2:​3, 4.

10. Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyar ’yan gudun hijira da suka zo wurinmu? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

10 Ƙari ga haka, a wasu lokuta hukuma takan yi wasu abubuwan da zai sa ya yi wa ’yan’uwanmu wuya su nemi wurin da ikilisiya take. Wasu ƙungiyoyi sun gaya wa ’yan’uwanmu cewa idan ba su karɓi aikin da zai sa su riƙa fasa taro ba, gwamnati ba za ta taimaka musu ko kāre su ba. Da yake wasu ’yan’uwanmu sun ji tsoro, sai suka karɓi aikin. Don haka, zai dace mu nemi ’yan’uwanmu da zarar mun ji labari sun iso wurin da muke da zama. Za su yi farin cikin sanin cewa mun damu da su. Idan muka yi hakan, za mu taimaka musu su ƙarfafa bangaskiyarsu sosai.​—Mis. 12:25; 17:17.

TAIMAKA WA ’YAN GUDUN HIJIRA

11. (a) Mene ne ’yan gudun hijirar suke bukata da farko? (b) Ta yaya ’yan gudun hijirar za su riƙa nuna godiya?

11 Da farko, muna bukata mu taimaka wa ’yan’uwanmu da abinci da tufafi da kuma wasu abubuwan biyan bukata. * Yin wasu abubuwa kamar ba wa ɗan’uwa taye zai sa shi farin ciki sosai. Kuma idan ’yan gudun hijirar suna godiya don taimakon da ake musu, hakan zai sa ’yan’uwan da suke ba su kyautar farin ciki. Duk da haka, bai kamata ’yan gudun hijirar su daina yin aiki suna dogara ga ’yan’uwansu kawai ba, don yin hakan zai sa su zub da mutuncinsu. (2 Tas. 3:​7-10) Amma zai dace a riƙa taimaka musu.

Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwanmu da suka yi gudun hijira? (Ka duba sakin layi na 11-13)

12, 13. (a) Ta yaya za mu taimaki ’yan gudun hijira? (b) Ka ba da misali.

12 Ba ma bukatar kuɗi da yawa kafin mu taimaka wa ’yan gudun hijira, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne lokaci da kuma nuna mun damu da su. Za mu iya koya musu yadda za su shiga motar haya da yadda za su sayi abinci mai kyau amma mai araha. Ban da haka ma, za mu iya taimaka musu wajen samun wasu abubuwa kamar keken ɗinki da abin yanka ciyawa don su yi aiki kuma su sami abin biyan bukata. Ƙari ga haka, za mu iya taimaka musu su saka ƙwazo a yin abubuwa a ikilisiyarsu. Idan zai yiwu, ka riƙa kai su taro. Ban da haka ma,  ka koya musu yadda za su yi wa’azi a yankinsu kuma ka riƙa fita wa’azi tare da su.

13 Da wasu matasa ’yan gudun hijira suka ƙaura zuwa wata ikilisiya, sai dattawan suka koya musu yadda za su yi tuƙi da amfani da kwamfuta da yadda za su rubuta wasiƙar neman aiki da kuma yadda za su tsara ayyukansu don su bauta wa Jehobah da kyau. (Gal. 6:10) Ba da daɗewa ba, sai su huɗun suka soma hidimar majagaba. Taimakon da dattawa suka yi musu da ƙoƙarin da su huɗun suka yi don su zama masu ibada sosai ya taimaka musu su sami ci gaba maimakon yin baƙin ciki don yanayinsu sanadiyyar duniyar Shaiɗan.

14. (a) Waɗanne jarabobi ne ’yan gudun hijira suke bukatar su guje wa? (b) Ka ba da misali.

14 Kamar yadda Kiristoci suke yi, ’yan gudun hijira ma suna bukata su guji jarabobi da kuma neman dukiya ruwa a jallo don hakan zai iya ɓata dangantakarsu da Jehobah. * Lije da aka ambata ɗazu da ’yan’uwansa sun faɗi darasin da mahaifinsu ya koya musu da suke gudu. Sun ce: “Da sannu-sannu mahaifinmu ya zubar da sauran kayan da muka kwashe kuma ya riƙe jakar, sai da fara’a ya ce: ‘Kun ga, ba ma bukatar waɗannan abubuwan!’ ”​—Karanta 1 Timotawus 6:⁠8.

ABU MAI MUHIMMANCI DA ’YAN GUDUN HIJIRA SUKE BUKATA

15, 16. Ta yaya za mu taimaka wa ’yan gudun hijira su (a) ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah? (b) su san cewa mun fahimci yadda suke ji?

15 ’yan gudun hijira suna bukatar kulawa da abin da zai sa su ƙarfafa imaninsu ba abin biyan bukata kawai ba. (Mat. 4:⁠4) Dattawa za su iya taimaka musu ta wurin kawo musu littattafai a yarensu da nuna musu ’yan’uwan da suke yarensu. ’Yan gudun hijira da yawa sun rabu da iyalinsu da garuruwansu da kuma ikilisiyoyinsu. Don haka, suna bukatar taimakon ’yan’uwa. Me ya sa? Hakan zai tabbatar musu cewa Jehobah yana ƙaunarsu da kuma tausaya musu. Idan ba haka ba, za su iya neman taimako daga danginsu da abokansu da ba Shaidu ba da suka fito daga wuri ɗaya. (1 Kor. 15:33) Idan muka sa suka ji daɗin hidimar da suke yi a ikilisiya, to muna aiki tare da Jehobah wajen ‘kiyayar da baƙi’ ke nan.​—Zab. 146:⁠9.

 16 Wasu ’yan gudun hijira ba za su sami zarafin komawa ƙasarsu ba idan waɗanda suke tsananta musu har ila suna nan. Haka ma ya faru da Yesu da iyayensa, ba su sami zarafin komawa ba. Lije ya ce: “Iyayen da suka ga yadda aka yi lalata da yaransu ƙarfi da yaji da kuma waɗanda aka kashe yaransu ba za su iya komawa wuraren da hakan ya faru ba.” Saboda haka, ’yan’uwa za su iya taimaka wa irin waɗannan mutanen ta wajen zama “masu-juyayi” da ƙauna da taushin zuciya da kuma tawali’u. (1 Bit. 3:⁠8) Wasu ’yan gudun hijira sun sha wahala sosai kuma hakan ya sa suna jin kunyar faɗan irin wahalar da suka sha, musamman a gaban yaransu. Saboda haka, zai dace ka yi tambayar nan, ‘Da a ce ni ne wannan abin ya faru da ni, yaya zan so a bi da ni?’​—Mat. 7:12.

YADDA DA ZA A YI WA ’YAN GUDUN HIJIRA WA’AZI

17. Ta yaya wa’azin da muke yi yake wartsake zuciyar ’yan gudun hijira?

17 ’Yan gudun hijira da yawa sun fito ne daga ƙasashen da ake sa wa aikinmu ido. Muna yaba ma ’yan’uwa masu ƙwazo da suke taimaka ma waɗannan mutanen. Saboda dubban ’yan gudun hijira da ba su taɓa jin wa’azin ‘Mulkin’ Allah ba, yanzu suna yin hakan. (Mat. 13:​19, 23) Ƙari ga haka, “masu-nauyin kaya” suna samun wartsakewa a lokacin da suka halarci taronmu kuma su ce: “Hakika Allah yana wurinku.”​—Mat. 11:​28-30; 1 Kor. 14:25.

18, 19. Ta yaya za mu kasance da basira sa’ad da muke yi ma ’yan gudun hijira wa’azi?

18 Ya kamata waɗanda suke ma ’yan gudun hijira wa’azi su kasance da basira da kuma “hankali.” (Mat. 10:16; Mis. 22:⁠3) Ka saurare su sa’ad da suke magana, amma kada ka tattauna batun siyasa da su. Ka bi ja-gorar ofishin Shaidun Jehobah da kuma hukuma don kada ka sa kanka da wasu cikin hadari. Ka yi la’akari da addininsu da kuma al’adarsu. Alal misali, wasu mutane da suka fito daga wasu ƙasashe za su iya so mata su riƙa ado yadda ake yi a ƙasarsu. Saboda haka, sa’ad da kake musu wa’azi, zai dace ka yi adon da ba zai sa su ƙi jin wa’azin da muke yi ba.

19 Kamar yadda Basamariye ya taimaka ma wani a kwatancin da Yesu ya yi, mu ma za mu iya taimaka wa mutanen da suke shan wahala ko da ba Shaidu ba. (Luk. 10:​33-37) Hanya mai kyau da za mu iya yin hakan ita ce yi musu wa’azi. Wani dattijo da ya taimaka ma ’yan gudun hijira da yawa ya ce: “Yana da muhimmanci mu gaya musu cewa, mu Shaidun Jehobah ne kuma yadda za mu taimaka musu shi ne mu yi musu wa’azi, ba biyan bukatunsu ba. Idan ba haka ba, wasu za su riƙa halartan taro kawai don mu riƙa biyan bukatunsu.”

SAKAMAKO MAI KYAU

20, 21. (a) Wane sakamako za mu samu sa’ad da muka ƙaunaci baƙi? (b) Me za mu bincika a talifi na gaba?

20 Nuna wa “baƙi” ƙauna yana sa a sami sakamako mai kyau. Don tsanantawa, wata ’yar’uwa mai suna Alganesh ta gudu daga ƙasar Eritrea da yara shida sa’ad da mijinta ya rasu. Sun gudu sun bar wurin da suke kuma sun yi kwana takwas suna tafiya ta hamada har suka iso Sudan. Ta ce: “ ’Yan’uwan sun kula da mu sosai kamar danginsu. Suna ba mu abinci da tufafi da wurin kwana da kuma biya mana kuɗin mota.” Ƙari ga haka, “waɗanne ’yan addini ne za su iya kula da mutanen da ba su taɓa saninsu ba don kawai suna bauta wa Allah ɗaya? Sai Shaidun Jehobah!”​—Karanta Yohanna 13:⁠35.

21 To, yara da yawa da suka gudo tare da iyayensu da kuma wasu ’yan gudun hijiran fa? A talifi na gaba, za mu bincika yadda dukanmu za mu taimaka musu su bauta wa Jehobah da farin ciki.

^ sakin layi na 2 A wannan talifin, za mu yi amfani da furucin nan “ ’yan gudun hijira” don mu kwatanta waɗanda suka bar gidajensu suka je wasu garuruwa ko wasu ƙasashe sanadiyyar tashin hankali ko yaƙi ko kuwa bala’i. Rahoton wani Jakada na ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa idan aka ƙirga mutane 113, ɗaya daga cikinsu ɗan gudun hijira ne.

^ sakin layi na 6 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Kada Ku Daina Yi wa Baƙi Alheri” da ke shafuffuka na 8-12 na Hasumiyar Tsaro na Oktoba, 2016.

^ sakin layi na 11 Da zarar dattawa sun ji labari cewa ’yan gudun hijira sun shigo, zai dace su bi umurnin da ke littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, babi na 8 sakin layi na 30 a Turanci. Dattawa za su iya rubuta wasiƙa ga ofishin ƙasarsu ta dandalinmu na jw.org don su san game da ’yan gudun hijirar. Amma kafin su yi hakan, zai dace su yi masa tambayoyi da basira don su san ko Mashaidi ne da gaske.

^ sakin layi na 14 Ka duba talifofin nan “Ba Wanda Zai Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu” da kuma “Ka Kasance da Gaba Gaɗi Jehobah Ne Mai Taimakonka!” da ke shafuffuka na 17-26 a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2014.