“Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.”​—MAT. 24:12.

WAƘOƘI: 60, 135

1, 2. (a) Su waye ne kalaman Yesu da ke Matta 24:12 ya shafa da farko? (b) Ta yaya littafin Ayyukan Manzanni ya nuna cewa wasu Kiristoci ba su bar ƙaunarsu ta yi sanyi ba? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

WANI abin da Yesu ya faɗa da zai nuna muna “cikar zamani” shi ne cewa “ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.” (Mat. 24:​3, 12) Wasu Yahudawa a ƙarni na farko da suke da’awa suna bauta wa Allah, sun bar ƙaunarsu ta yi sanyi.

2 Amma yawancin Kiristocin sun ci gaba da “koyarwa da yin wa’azi” game da Yesu da ƙaunar Allah da kuma juna. Ƙari ga haka, sun ƙaunaci marasa bi ma. (A. M. 2:​44-47; 5:42) Duk da haka, wasu cikin manzannin Yesu a ƙarni na farko sun bar ƙaunarsu ta yi sanyi.

3. Me ya sa ƙaunar wasu Kiristoci ta yi sanyi?

3 A lokacin da aka ta da Yesu daga mutuwa, ya gaya ma wata ikilisiyar Kiristoci na ƙarni na farko da ke Afisa cewa: “Amma ina da bacin-rai game da kai, da ka bar ƙaunarka ta fari.” (R. Yoh. 2:⁠4) Me ya sa ya gaya musu hakan? Wataƙila waɗannan Kiristocin suna da halaye marasa kyau na mutanen  duniya. (Afis. 2:​2, 3) Kamar yadda wasu birane suke, yawancin mutanen da ke Afisa suna aikata ayyukan da ba su dace ba. Akwai wadata a birnin sosai kuma mutane sun mai da hankali ga rayuwar jin daɗi da shaƙatawa. Abubuwan duniya sun sa ƙaunarsu ta yi sanyi. Bugu da ƙari, halin rashin da’a ko lalata sun zama gama gari.

4. (a) Me ya sa ƙaunar yawancin mutane ta ragu a yau? (b) Waɗanne hanyoyi uku za su taimaka mana mu ci gaba da nuna ƙauna?

4 Yesu ya yi annabci cewa ƙaunar da yawancin mutane suke yi za ta ragu. Mutane a yau ba sa yin abin da ya nuna cewa suna ƙaunar Allah. Miliyoyin mutane ba sa dogara ga Allah, a maimakon hakan, suna dogara ga ’yan Adam da kuma ƙungiyoyi don su magance matsalolin da muke fuskanta. Don haka, ƙaunar mutanen da ba sa bauta wa Jehobah sai ƙara yin sanyi take yi. Kuma kamar yadda ya faru da Kiristoci a ƙarni na farko, ƙaunar Kiristoci a yau ma za ta yi sanyi idan ba su mai da hankali ba. Yanzu bari mu bincika hanyoyi uku da za su taimaka mana mu ci gaba da nuna ƙauna: (1) Ƙaunar da muke wa Jehobah (2) ƙaunar da muke wa Kalmar Allah da (3) ƙaunar da muke wa juna.

ƘAUNAR DA MUKE WA JEHOBAH

5. Me ya sa muke bukata mu nuna wa Allah ƙauna?

5 Yesu ya ambata ƙaunar da ta fi muhimmanci a ranar da ya annabta cewa ƙauna za ta yi sanyi. Ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.” (Mat. 22:​37, 38) Hakika, ƙaunar Allah za ta taimaka mana mu riƙa bin dokokin Jehobah da jimrewa da kuma guje wa abubuwa marasa kyau. (Karanta Zabura 97:10.) Amma Shaiɗan da duniyarsa suna ƙoƙari don su sa ƙaunar da muke da shi ta yi sanyi.

6. Me yake faruwa a lokacin da mutane suka bar ƙaunar Jehobah ta yi sanyi?

6 Mutanen duniya ba su san yadda ya kamata su riƙa nuna ƙauna ba. Maimakon su yi ƙaunar Allah wanda ya halicce su, sun zama “masu-son kansu” kawai. (2 Tim. 3:⁠2) Wannan duniyar da Shaiɗan yake iko da ita tana ƙarfafa “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi.” (1 Yoh. 2:16) Manzo Bulus ya ja kunnen Kiristoci game da hakan. Ya ce: “Himmantuwar jiki mutuwa ce: . . . domin himmantuwar jiki gāba ce da Allah.” (Rom. 8:​6, 7) Hakika, waɗanda suka nemi abin duniya ruwa a jallo ko kuma suka biye ma sha’awar jiki ba su sami ribar kome ba sai dai baƙin ciki.​—1 Kor. 6:18; 1 Tim. 6:​9, 10.

7. Waɗanne haɗarurruka ne mabiyan Kristi suke fuskanta a yau?

7 A wasu ƙasashe, masu musun wanzuwar Allah da masu shakka ko yana wanzuwa da kuma waɗanda suka gaskata da juyin halitta suna sa mutane su ƙi ƙaunar Allah kuma su zama da ra’ayin nan cewa, ba ya wanzuwa. Kuma suna sa mutane su gaskata cewa sai wawaye ne da waɗanda ba su yi makaranta ba suke gaskata akwai Mahalicci. Ban da haka ma, mutane suna daraja ’yan kimiyya fiye da Allah wanda ya halicce su. (Rom. 1:25) Idan muka mai da hankali ga irin waɗannan ra’ayoyin, za mu yi sanyin gwiwa kuma ƙaunar da muke yi wa Jehobah za ta yi sanyi.​—Ibran. 3:12.

8. (a) Waɗanne irin abubuwa ne suke iya sa bayin Jehobah su yi sanyin gwiwa? (b) Wace ƙarfafa muka samu a littafin Zabura 136?

8 Idan muka mai da hankali ga abubuwan da suke sa mu yi sanyin gwiwa, bangaskiyarmu za ta raunana kuma ƙaunar  da muke wa Allah za ta ragu. Dukanmu a wasu lokuta muna fuskantar yanayoyin da suke sa mu sanyin gwiwa a duniyar nan da Shaiɗan yake mulki. (1 Yoh. 5:19) Wataƙila muna fama da wasu matsaloli kamar tsufa da ciwo ko kuma rashin abin biyan bukata. Ban da haka ma, za mu iya yin baƙin ciki don kasawarmu ko kuma mu yi sanyin gwiwa don abubuwan da muke zato ba su faru ba. Duk da haka, bai kamata mu bar waɗannan abubuwan su sa mu ji kamar Jehobah ba ya ƙaunar mu ba. A maimakon haka, zai dace mu yi bimbini a kan furucin Jehobah game da irin ƙaunar da yake yi mana. Irin wannan furucin yana littafin Zabura 136:23. Wurin ya ce: “Wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙantarmu: Gama jinƙansa har abada ne.” Hakika, Jehobah yana ƙaunar bayinsa ba fashi. Don haka, muna da tabbaci cewa zai ji ‘addu’oinmu’ kuma ya ɗauki mataki.​—Zab. 116:1; 136:​24-26.

9. Mene ne ya taimaka wa Bulus ya ci gaba da ƙaunar Allah?

9 Bulus ya ƙarfafa bangaskiyarsa sa’ad da ya yi bimbini a kan yadda Jehobah yake taimaka masa kamar yadda marubucin zabura ya yi. Bulus ya ce: “Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum zai mini?” (Ibran. 13:⁠6) Wannan tabbacin da Bulus ya kasance da shi ya taimaka masa ya shawo kan matsalolin da suke damunsa. Bai bar matsalolinsa sun sa shi sanyin gwiwa ba. Shi ya sa a lokacin da yake fursuna ya rubutu wasiƙu da yawa don ya ƙarfafa bayin Allah. (Afis. 4:1; Filib. 1:7; Fil. 1) Hakika, a lokacin da yake shan wahala, bai bar ƙaunar da yake yi wa Allah ta yi sanyi ba. Me ya ƙarfafa shi ya yi hakan? Ya ci gaba da dogara ga “Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Kor. 1:​3, 4) Ta yaya za mu bi misalin Bulus kuma mu ci gaba da ƙaunar Jehobah sosai?

Ku ƙaunaci Jehobah (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya za mu ci gaba da ƙaunar Jehobah sosai?

10 Bulus ya faɗi wata hanya da za ta taimaka mana mu ci gaba da ƙaunar Jehobah. Ya rubuta wa ’yan’uwa cewa: “Ku yi addu’a ba fasawa.” Bayan haka ya ce: “Kuna lizima cikin addu’a.” (1 Tas. 5:17; Rom. 12:12) Yin addu’a ita ce hanya ta farko da mutum zai bi don ya zama abokin Jehobah. (Zab. 86:3) Idan muka nemi isashen lokaci kuma muka yi wa Jehobah addu’a muka gaya masa duk abin da ke zuciyarmu, za mu kusace shi kuma zai ‘ji addu’ar’ da muke yi masa. (Zab. 65:⁠2) Ƙari ga haka, sa’ad da muka gane cewa Jehobah yana amsa addu’o’inmu, za mu riƙa ƙaunarsa sosai. Ban da haka ma, za mu gane cewa “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira bisa gareshi.” (Zab. 145:18) Saboda haka, wannan tabbacin da muke da shi cewa Jehobah yana tallafa mana, zai taimaka mana mu jimre da matsalolin da muke fuskanta.

ƘAUNAR DA MUKE WA KALMAR ALLAH

11, 12. Mene ne zai taimaka mana mu so Kalmar Allah sosai?

11 Kiristoci suna son gaskiyar da suke koya daga Littafi Mai Tsarki sosai. Kalmar Allah ce tushen wannan gaskiyar. Yesu ya yi addu’a cewa: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yoh. 17:17) Saboda haka, sanin Kalmar Allah da kyau shi ne zai taimaka mana mu ƙaunaci gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. (Kol. 1:10) Amma hakan ba ya nufin sanin Kalmar Allah kaɗai. Ka lura da yadda marubucin Zabura 119 ya taimaka mana mu san abin da yake nufi mutum ya yi ƙaunar Kalmar Allah. (Karanta Zabura 119:​97-100.) Shin kana neman isasshen lokaci don ka yi bimbini ko tunani a kan wasu Nassosi  kowace rana? Idan muka yi bimbini a kan yadda yin amfani da Kalmar Allah yake taimaka mana, za mu riƙa ƙaunar Kalmar Allah sosai.

12 Wani marubucin zabura ya ce: “Kalmominka suna da zaƙi ga bakina ba misali! I, sun fi zuma zaƙi a bakina.” (Zab. 119:103) Littattafan da bawan nan suke tanadar mana yana kama da abinci mai daɗi. Muna zama da kyau mu ci abincin da muke so, ko ba haka ba? Haka ma yake da littattafanmu, muna bukata mu nemi lokaci sosai mu bincika su. Idan muka yi hakan, za mu fahimci “magana masu-daɗin ji” kuma mu yi amfani da shi don taimaka ma wasu.​—M. Wa. 12:10.

13. Me ya taimaka wa Irmiya ya so Kalmar Allah, kuma ta yaya hakan ya shafe shi?

13 Annabi Irmiya ya so Kalmar Allah sosai. Ka lura da abin da ya faɗa game da Kalmar Allah. Ya ce: “Na iske maganarka, na kuwa ci su: zantattukanka sun zama mini murna da farin ciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji Allah mai-runduna.” (Irm. 15:16) Kamar dai Irmiya ya ci Kalmar Allah ne sa’ad da ya yi bimbini a kan abubuwan da ya karanta. Ta hakan ne ya san cewa gata ne babba a kira shi da sunan Allah. Shin ƙauna da muke wa Kalmar Allah yana sa mu ɗauki gatan yin amfani da sunan Allah da kuma wa’azin Mulkinsa a waɗannan kwanaki na ƙarshe da muhimmanci?

Ku ƙaunaci Kalmar Allah (Ka duba sakin layi na 14)

14. Me zai ƙara taimaka mana mu so Kalmar Allah sosai?

14 Ban da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da bawan nan yake tanadar mana, mene ne zai taimaka mana mu so Kalmar Allah kuma? Za mu ƙara sanin Kalmar Allah ta wurin halartan taro kullayaumi. Nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi kowane mako ta wurin amfani da Hasumiyar Tsaro shi ne hanya mafi muhimmanci na sanin Kalmar Allah. Idan muna so mu fahimce batun da ake tattaunawa da kyau, ya kamata mu bincika talifin sosai kafin a yi nazarinsa. Kuma wani abin da zai taimaka mana shi ne karanta dukan Nassosin da suke ciki. A yau, za mu iya sauko da Hasumiyar Tsaro daga dandalinmu na jw.org/⁠ha ko kuma mu karanta shi ta manhajar JW Library a  harsuna da yawa. Idan muna amfani da waya ko kwamfutar hannu, za mu iya karanta Nassosin da suke talifin ba tare da ɓata lokaci ba. Ko ta yaya muke so mu yi nazari, zai dace mu riƙa karanta Nassosin da kyau kuma mu yi bimbini a kai don mu so Kalmar Allah sosai.​—Karanta Zabura 1:2.

ƘAUNAR DA MUKE WA JUNA

15, 16. (a) Me muke bukatar mu yi bisa ga Yohanna 13:​34, 35? (b) Me ya sa ƙaunar da muke yi wa ’yan’uwanmu take da alaƙa da ƙaunar Allah da kuma son Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki?

15 A daren Yesu na ƙarshe a duniya, ya gaya wa almajiransa cewa: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”​—Yoh. 13:​34, 35.

16 Nuna wa ’yan’uwanmu ƙauna yana da alaƙa da ƙaunar Allah. Hakika, ba zai yiwu mu ƙaunaci Allah ba tare da ƙaunar ’yan’uwanmu ba. Manzo Yohanna ya ce: ‘Wanda bai yi ƙaunar ɗan’uwansa wanda ya gani ba, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani.’ (1 Yoh. 4:20) Ƙari ga haka, ƙaunar Jehobah da ’yan’uwanmu yana da alaƙa da son Kalmar Allah. Me ya sa? Domin ƙaunar da muke wa Kalmar Allah ce take motsa mu mu yi biyayya da dokar nan cewa mu ƙaunaci Allah da kuma ’yan’uwanmu.​—1 Bit. 1:22; 1 Yoh. 4:⁠21.

Ku ƙaunaci ’yan’uwa (Ka duba sakin layi na 17)

17. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙauna?

17 Karanta 1 Tasalonikawa 4:​9, 10. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna ƙauna a ikilisiyarmu? Wani tsoho ko tsohuwa za ta iya bukaci wani ya taimaka mata don ta halarci taro. Wata gwauruwa za ta so wani ya zo ya gyara mata gidanta. (Yaƙ. 1:27) Ko da tsofaffi ne ko kuma matasa, waɗanda suke sanyin gwiwa ko baƙin ciki ko fuskantar wasu matsaloli suna bukatar ƙarfafa ko ta’aziyya. (Mis. 12:25; Kol. 4:11) Muna nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu da gaske sa’ad da muka ƙarfafa da kuma taimaka ma ‘waɗanda suke cikin iyalin imaninmu.’​—Gal. 6:10.

18. Me zai taimaka mana mu sasanta wani saɓani da muka samu da ’yan’uwanmu?

18 An annabta a Littafi Mai Tsarki cewa, a “kwanaki na ƙarshe” mutane za su zama masu son kai da kuma hadama. (2 Tim. 3:​1, 2) Da yake mu Kiristoci ne, zai dace mu yi ƙwazo don mu ƙara ƙaunar Allah da Kalmarsa da kuma junanmu. A gaskiya, a wasu lokuta za mu iya samun saɓani da ’yan’uwanmu. Amma da yake muna ƙaunar juna, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sasanta saɓannin da sauri kuma cikin lumana. (Afis. 4:32; Kol. 3:14) Don haka, maimakon mu bar ƙaunarmu ta yi sanyi, zai dace mu ci gaba da ƙaunar Allah da Kalmarsa da kuma ’yan’uwanmu sosai kuma da zuciya ɗaya.