GAYUS da wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun fuskanci matsaloli da yawa. Wasu da suke yaɗa koyarwar ƙarya suna ƙoƙari su sa ’yan’uwa a ikilisiyoyi su yi sanyin gwiwa. (1 Yoh. 2:​18, 19; 2 Yoh. 7) Wani ɗan’uwa mai suna Diyoturifis yana yaɗa ‘miyagun zantattuka’ a kan manzo Yohanna da kuma wasu Kiristoci. Ban da haka ma, ba ya taimaka wa Kiristoci masu ziyara kuma yana zuga wasu su yi abin da yake yi. (3 Yoh. 9, 10) A wannan yanayin ne Yohanna ya rubuta wa Gayus wasiƙa. Wannan wasiƙar da ya rubuta wajen shekara ta 98 a zamaninmu tana cikin Nassin Helenanci na Kirista da ake kira “Wasiƙar Yohanna ta Uku.”

Duk da matsalolin da Gayus ya fuskanta, ya bauta wa Jehobah da aminci. Ta yaya ya nuna cewa yana da aminci? Me ya sa muke bukatar mu bi misalin Gayus? Ta yaya wasiƙar Yohanna zai taimaka mana mu yi hakan?

WASIƘA ZUWA GA AMINI

Wanda ya rubuta wasiƙa ta uku ta Yohanna ya kira kansa ‘dattijo.’ Wannan ya sa Gayus ya san cewa manzo Yohanna ne ya rubuta wasiƙar. Kuma a wasiƙar, Yohanna ya kira Gayus “ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.” Bayan haka, ya ce kamar yadda Gayus yake da lafiya, hakan dangantakarsa da Jehobah take. Wannan furuci mai ban ƙarfafa ne, ko ba haka ba?​—3 Yoh. 1, 2, 4.

Wataƙila Gayus dattijo ne a ikilisiya, amma wasiƙar ba ta ambata hakan ba. Yohanna ya yabi Gayus don yadda ya nuna wa ’yan’uwan karimci ko da yake bai san su ba. Yohanna ya san cewa wannan halin Gayus ya nuna cewa shi mai aminci ne da yake an san Kiristoci da taimaka wa baƙi.​—Far. 18:​1-8; 1 Tim. 3:2; 3 Yoh. 5.

Abin da Yohanna ya rubuta a wasiƙarsa don ya gode wa Gayus ya nuna cewa ’yan’uwan da ke yankin Yohanna sun saba tafiya zuwa waɗannan ikilisiyoyin, kuma bayan sun dawo, sai su gaya wa Yohanna abin da ya faru. Wannan dalilin ne ya sa Yohanna ya ji labarin waɗannan ikilisiyoyin.

Babu shakka, masu ziyara za su so su zauna a gidajen ’yan’uwansu. Mutane da yawa ba sa son masaukai don wuraren ba su da kyau kuma ana lalata sosai a wuraren. Shi ya sa matafiya, sun gwammace su  zauna da abokansu, Kiristoci masu ziyara kuma suna zama da ’yan’uwansu Kiristoci.

“SABILI DA SUNAN SUKA FITA”

Yohanna ya ƙarfafa Gayus ya riƙa taimaka wa ’yan’uwa, kuma manzo ya gaya masa ya dinga “raka su [wato, baƙin] da guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah.” Kuma hakan ya ƙunshi ba su abubuwan da za su biya bukatarsu da shi har sai sun isa inda suke son su je. Akwai tabbaci cewa Gayus ya saba taimaka wa baƙi shi ya sa suka ba wa Yohanna rahoton bangaskiyar Gayus da kuma yadda ya kula da su.​—3 Yoh. 3, 6.

Wataƙila waɗannan baƙin suna hidima a ƙasashen waje, wato suna aiki tare da Yohanna ko wataƙila masu kula masu ziyara ne. Ko da mene ne yanayinsu, tafiyar da suka yi don yaɗa bishara ne. Yohanna ya ce: “Sabili da sunan suka fita.” (3 Yoh. 7) Yohanna yana magana game da Allah ne (ka duba aya ta 6), don haka, wannan furucin “sabili da sunan” yana nuni ga sunan Jehobah ne. Saboda haka, waɗannan ’yan’uwan suna cikin ikilisiya shi ya sa aka ce a marabce su da kyau. Yohanna ya ce: “Ya kamata fa mu yi ma irin waɗannan maraba, domin mu zama abokan aiki tare da gaskiya.”​—3 Yoh. 8.

YA TAIMAKA TA WAJEN MAGANCE WATA MATSALA

Dalilin da ya sa Yohanna ya rubuta wa Gayus wasiƙa ba don ya yaba masa kaɗai ba ne. Amma ya so ya taimaka masa ya magance wata matsala ce. Akwai wani a cikin ikilisiya mai suna Diyoturifis da ya ƙi ya taimaka wa Kiristoci masu ziyara. Kuma yana zuga wasu ma su yi hakan.​—3 Yoh. 9, 10.

Babu shakka, ba wani Kirista mai aminci da zai yarda ya sauka ko zauna a gidan Diyoturifis ko da ya amince da hakan. Me ya sa? Yana son shugabanci a ikilisiya kuma ba ya mutunta abin da Yohanna ya faɗa kuma yana ɓata sunan manzon da kuma wasu ’yan’uwa. Ba za a iya kiran Diyoturifis annabin ƙarya ba, duk da cewa bai so ya bi ja-gorancin Yohanna ba. Amma Diyoturifis bai kasance da aminci ba sa’ad da ya nemi shugabanci a ikilisiya ƙarfi da yaji da kuma wasu halaye marasa kyau da ya nuna. Labarin Diyoturifis ya nuna yadda girman kai da son matsayi ruwa a jallo za su iya ɓata haɗin kan ikilisiya. Wannan dalilin ne ya sa Yohanna ya gaya wa Gayus har da mu ma cewa: ‘Kada ku bi mugun gurbi.’​—3 Yoh. 11.

DALILI MAI KYAU NA YIN NAGARTA

Yohanna ya ambata cewa Dimitriyas ya kafa misali mai kyau ba kamar Diyoturifis ba. Yohanna ya ce: “Dimitiriyas na da kyakkyawar shaida . . . Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.” (3 Yoh. 12) Wataƙila Dimitiriyas ya so Gayus ya taimaka masa shi ya sa aka rubutu wasiƙar Yohanna ta uku don Gayus ya san shi da kyau. Kuma wataƙila Dimitiriyas ne ya ba wa Gayus wasiƙar. Wataƙila ya ƙarfafa abin da Yohanna ya rubuta da yake shi wakilinsa ne ko wataƙila mai ziyara.

Me ya sa Yohanna ya ƙarfafa Gayus ya ci gaba da taimaka wa ’yan’uwa bayan ya saba yin hakan? Ko Yohanna ya so ƙarfafa Gayus don kada ya yi sanyin gwiwa wajen taimaka wa mutane ne? Shin manzon ya damu ne don yana ganin kamar Diyoturifis yana yunkurin koran waɗanda suke karɓan baƙi a ikilisiya? Ko da mene ne yanayin, Yohanna ya tabbatar wa Gayus cewa: “Wanda yake aika nagarta na Allah ne.” (3 Yoh. 11) Wannan furucin zai iya ƙarfafa mutum ya ci gaba da yin nagarta babu fashi.

 Wannan wasiƙar ta taimaka wa Gayus ya ci gaba da karɓan baƙi ne? E, shi ya sa aka saka wannan wasiƙar a Littafi Mai Tsarki kuma muna karantawa a yau, don ya ƙarfafa mu mu yi abu “mai-kyau.”

DARUSSA DAGA YOHANNA TA UKU

Ba a ƙara wata magana kuma game da Gayus ba. Duk da haka, ɗan labarin da muka ji game da shi zai koya mana darussa masu yawa.

A waɗanne hanyoyi ne za mu ‘riƙa karɓan baƙi’?

Da farko, yawancinmu mun koyi gaskiya game da Littafi Mai Tsarki daga waɗannan bayi masu aminci da suke ziyara. Hakika, ba dukan Kiristoci ba ne a yau suke tafiya wurare da nisa don su yi shelar bishara. Amma kamar Gayus, mu ma za mu iya tallafa da kuma ƙarfafa waɗanda suke ziyara kamar su mai kula da da’ira da matarsa. Ko kuma mu taimaka wa ’yan’uwa da suka ƙaura zuwa wasu wurare ko ƙasa don su yi hidima a inda ake da bukatar masu shela. Saboda haka, bari dukanmu mu ‘riƙa karɓan baƙi.’​—Rom. 12:13; 1 Tim. 5:​9, 10.

Na biyu, bai kamata mu yi mamaki ba idan wasu a ikilisiya suka ƙi su saurari masu ja-goranci a wasu lokuta. Me ya sa? Don hakan ya taɓa faruwa da Yohanna da kuma manzo Bulus. (2 Kor. 10:​7-12; 12:11-13) Me za mu yi idan muka fuskanci irin wannan yanayin a ikilisiya? Bulus ya gaya wa Timotawus cewa: “Kada bawan Ubangiji kuwa ya yi husuma, amma sai ya yi nasiha ga duka, mai-sauƙin koyarwa, mai-haƙuri cikin tawali’u yana horon masu jayayya.” Idan muka yi haƙuri sa’ad da wani ya ba mu haushi, hakan zai iya sa masu yawan fushi su daina yin hakan. Kuma Jehobah zai sa “su tuba zuwa sanin gaskiya.”​—2 Tim. 2:​24, 25.

Na uku, ya kamata a yaba wa Kiristoci da suke bauta wa Jehobah da aminci duk da tsanantawa. Manzo Yohanna ya ƙarfafa Gayus kuma ya gaya masa cewa abin da yake yi daidai ne. Hakazalika, dattawa suna bin misalin Yohanna ta wurin ƙarfafa ’yan’uwa don kada su “su yi suwu” ko kasala.​—Isha. 40:31; 1 Tas. 5:11.

Wannan wasiƙar da manzo Yohanna ya rubuta wa Gayus da ke ɗauke da kalamai 219 a Hellenanci ne ta fi ƙanƙanta a littattafan Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, Kiristoci sun koyi darussa masu muhimmanci daga ciki.