“Ku biɗi mulkinsa [Allah] waɗannan abu kuma za a ƙara muku su.”—LUK. 12:31.

WAƘOƘI: 40, 98

1. Mene ne bambancin bukatunmu da abin da muke so?

ABUBUWAN da muke bukata don mu rayu ba su da yawa. Waɗannan abubuwan su ne abinci da tufafi da kuma masauki. Amma abubuwan da ’yan Adam suke so ba su da iyaka. Kuma mutane da yawa ba su san bambancin bukatunsu da kuma abubuwan da suke so ba.

2. Waɗanne abubuwa ne mutane suke so?

2 Abubuwan da mutane suke so ya dangana ne da inda suke zama. A ƙasashe masu tasowa, mutane da yawa suna so su sami isashen kuɗi don su sayi wayar selula da babur ko kuma fili don su gina gida. A ƙasashe masu arziki, mutane sha’awar sayen tufafi mai yawa da babban gida ko kuma mota mai tsada. Amma, a duk inda muke da zama da kuma kome yawan kuɗinmu, za mu iya soma son abin duniya ido-rufe ko da muna da kuɗin saya ko a’a.

 KA GUJI WAUTAR SON ABIN DUNIYA

3. Mene ne son abin duniya?

3 Mene ne son abin duniya? Son tara dukiya ne maimakon yin abubuwan da suka shafi bautar Jehobah. Hali ne na son kuɗi ido-rufe da kuma son tara abin duniya mai yawan gaske. Ba dole ba ne sai kana da kuɗi ko kuma sayen abubuwa masu tsada kafin ka zama mai son abin duniya. Talakawa ma suna iya zama masu son abin duniya ainun kuma su manta da biɗan Mulkin Allah farko a rayuwarsu.—Ibran. 13:5.

4. Ta yaya Shaiɗan yake sa mu yi “sha’awar” abubuwan da muke gani?

4 Shaiɗan yana yin amfani da tallace-tallace don ya sa mu ɗauka cewa muna bukatar mu sayi wasu abubuwa don mu ji daɗin rayuwa ko da ba ma bukatarsu. Yana amfani da “sha’awar idanu,” wato yana sa mu yi sha’awar abubuwan da muke gani da idanunmu. (1 Yoh. 2:15-17; Far. 3:6; Mis. 27:20) Wasu abubuwa da ake tallar su suna da kyau wasu kuma ba su da kyau amma kuma suna da ban sha’awa. Ka taɓa sayan abin da ba ka bukata domin ana tallar sa ko kuma don ka gan shi a kanti? Shin daga baya ka ga cewa ba ka bukatarsa a rayuwarka? Irin waɗannan abubuwan da ba su da muhimmanci suna iya zama matsala a rayuwarmu. Za su iya zama tarko ko kuma su raba hankalinmu daga abubuwan da suka shafi bautar mu ga Jehobah, kamar nazarin Littafi Mai Tsarki da shirya da kuma halartan taro ko kuma fita wa’azi a kai a kai. Manzo Yohanna ya yi mana gargaɗi cewa: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awarta.”

5. Mene ne zai iya faruwa da waɗanda suka yi amfani da kuzarinsu don neman abin duniya?

5 Shaiɗan yana son mu yi amfani da dukan kuzarinmu don mu nemi kuɗi maimakon mu bauta wa Jehobah. (Mat. 6:24) Waɗanda suke amfani da dukan kuzarinsu don tara abin duniya ba za su yi farin ciki ba kuma rayuwarsu ba za ta kasance da ma’ana ba. Ƙari ga haka, zai iya sa su daina biɗan Mulkin Allah a rayuwarsu. (1 Tim. 6:9, 10; R. Yoh. 3:17) Yesu ya nuna hakan a kwatancinsa na mai shuka iri. Sa’ad da aka shuka saƙon Mulki a ‘wurin ƙayayuwa . . .  sha’awar abubuwa masu-shigowa, su kan shaƙe magana, ta zama marar-amfani.’—Mar. 4:14, 18, 19.

6. Wane darasi ne muka koya daga labarin Baruch?

6 Baruch sakataren annabi Irmiya ne. Ana gab da halaka Urushalima, sai Baruch ya soma ‘biɗan manyan’ abubuwan da ba za su dawwama ba. Amma, abin da ya kamata ya biɗa shi ne alkawarin da Jehobah ya yi masa cewa: ‘Zan ba ka naka rai ganima.’ (Irm. 45:1-5) Allah zai ƙyale a halaka birnin da dukan abubuwan da ke cikinsa. (Irm. 20:5) Yayin da ƙarshen wannan duniyar yake gabatowa, bai kamata mu mai da hankali ga tara dukiya ba. Kuma kada mu sa rai cewa ba abin da zai sami dukiyarmu a lokacin ƙunci mai girma.—Mis. 11:4; Mat. 24:21, 22; Luk. 12:15.

7. Mene ne za mu tattauna, kuma me ya sa?

7 Yesu ya ba mu shawara mai kyau da za ta taimaka mana mu biya bukatunmu ba tare da mun raba hankalinmu ko kuma mu so abin duniya ba. Ƙari ga haka, shawarar ta taimaka mana mu guji yin alhini ainun. Ya ƙara ba da wannan shawarar a Huɗuba da ya yi a kan Dutse. (Mat. 6:19-21) Bari mu karanta kuma mu bincika ayoyin da ke  Matta 6:25-34. Yin hakan zai sa mu kasance da tabbaci cewa wajibi ne mu ‘biɗi Mulkin Allah,’ ba abin duniya ba.—Luk. 12:31.

JEHOBAH YANA BIYAN BUKATUNMU

8, 9. (a) Me ya sa bai kamata mu riƙa yawan damuwa game da abubuwan da muke bukata ba? (b) Mene ne Yesu ya sani game da ’yan Adam da kuma bukatunsu?

8 Karanta Matta 6:25. Sa’ad da Yesu ya gaya wa masu sauraronsa su daina ‘alhini saboda ransu,’ yana nufin su “daina damuwa.” Suna alhini a kan abubuwan da bai kamata ba. Saboda haka, ya dace da Yesu ya ce su daina yin hakan. Yawan damuwa a kan abubuwan da muke bukata ma zai iya raba hankalin mutum kuma ya hana shi mai da hankali a kan abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa. Yesu ya damu da almajiransa shi ya sa a huɗubar da ya yi, ya gargaɗe su sau huɗu game da haɗarin da ke tattare da yawan damuwa.—Mat. 6:27, 28, 31, 34.

9 Me ya sa Yesu ya gaya mana kada mu damu game da abin da za mu ci ko abin da za mu sha ko kuma tufafin da za mu saka? Babu shakka, waɗannan abubuwan suna da muhimmanci a rayuwa. Idan ba mu da waɗannan abubuwan za mu riƙa damuwa, kuma Yesu ya san da hakan don ya san bukatunmu na yau da kullum. Ƙari ga haka, ya san cewa waɗanda za su zama almajiransa daga baya, wato a “kwanaki na ƙarshe,” za su fuskanci mawuyacin yanayi. (2 Tim. 3:1) Za su fuskanci rashin aiki da hawan farashin kaya da karancin abinci da kuma matuƙar talauci. Duk da haka, Yesu ya san cewa ‘rai ya fi gaban abinci, jiki kuma ya fi tufafi.’

10. Sa’ad da Yesu ya koya wa mabiyansa yadda ya kamata su yi addu’a, mene ne ya ce su sa a kan gaba a rayuwarmu?

10 A huɗubarsa ta farko a kan dutse, Yesu ya gaya wa masu sauraronsa su roƙi Ubansu na sama ya biya bukatunsu, ya ce su yi addu’a cewa: “Ka ba mu yau abincin yini.” (Mat. 6:11) Ko kuma kamar yadda ya sake faɗa: ‘Ka ba mu yau da gobe abincin yini.’ (Luk. 11:3) Amma hakan ba ya nufin za mu riƙa yawan tunani game da bukatunmu. A wannan addu’ar, Yesu ya nuna cewa abu mafi muhimmanci shi ne mu riƙa yin addu’a Mulkin Allah ya zo. (Mat. 6:10; Luk. 11:2) Don ya kwantar da hankalin masu sauraronsa, Yesu ya ƙarfafa su kuma ya tuna musu yadda Jehobah yake kula da dukan halittunsa.

11, 12. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah yake kula da tsuntsaye? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.)

11 Karanta Matta 6:26. Ya kamata mu lura da “tsuntsaye na sama.” Ko da yake ba su da girma, suna cin hatsi da ’ya’yan itatuwa da ƙwari ko kuma tāna masu yawa. Sun fi ’yan Adam cin abinci, amma Jehobah yana biyan dukan bukatunsu duk da cewa ba sa noma kuma ba sa shuki. (Zab. 147:9) Hakika, ba ya saka abincin a bakinsu, su ne da kansu suke zuwa neman abinci, kuma suna samu sosai.

12 Yesu ya san cewa tun da Ubansa na sama yana biya bukatun tsuntsaye, zai biya bukatun ’yan Adam. [1] (1 Bit. 5:6, 7) Ba zai saka abincin a bakinmu ba, amma zai albarkaci duk ƙoƙarin da muke yi don mu samu abinci ko kuma mu samu kuɗin sayan abubuwan da muke bukata. A wani lokaci, zai iya sa wasu su taimaka mana. Ko da yake Yesu bai ce Jehobah ya yi wa tsuntsaye  tanadin masauki ba, amma ya ba su basira da kayan da suke bukata don su gina sheƙarsu. Hakazalika, Jehobah zai taimaka mana mu samu masaukin da ya dace da iyalinmu.

13. Mene ne ya nuna cewa mun fi tsuntsaye daraja?

13 Yesu ya tambayi masu sauraronsa: “Ku ba ku fi [tsuntsaye na sama] daraja dayawa ba?” Babu shakka, Yesu ya san cewa, ba da daɗewa ba zai ba da ransa a madadin ’yan Adam. (Gwada Luka 12:6, 7.) Yesu ya ba da ransa don ’yan Adam kawai. Bai mutu don tsuntsaye ba, amma ya mutu don mu sami rai na har abada.—Mat. 20:28.

14. Mene ne mai yawan damuwa ba zai taɓa yi ba?

14 Karanta Matta 6:27. Me ya sa Yesu ya ce yawan damuwa ba zai sa mutum ya ƙara kamu ɗaya ga kwanakin rayuwarsa ba? Domin yawan damuwa game da bukatunmu na yau da kullum ba zai sa rayuwarmu ta yi tsawo ba. Maimakon haka, yawan damuwa yana iya rage kwanakin rayuwarmu.

15, 16. (a) Mene ne muka koya daga yadda Jehobah yake kula da furanni na jeji? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.) (b) Waɗanne tambayoyi ne muke bukata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa?

15 Karanta Matta 6:28-30. Ba wanda ba ya son saka tufa mai kyau musamman idan zai yi ayyuka da suka shafi bautar Jehobah, kamar halartan taro da fita wa’azi ko kuma halartan manyan taro. Duk da haka, bai kamata mu riƙa “alhini da zancen tufa” ba!  Yesu ya ce mu lura da halittun Jehobah. Ya ce za mu koyi abubuwa da yawa daga “furanni na jeji.” Wataƙila a nan Yesu yana magana ne game da furanni kamar baɗo da makamatansu. Waɗannan furanni suna da ban sha’awa sosai. Ba sa sāka ko kuma ɗinki. Duk da haka, suna da kyaun gaske. Ko Sulemanu “da darajarsa duka, ba ya [saka kaya] kamar guda ɗayansu ba.”

16 Yesu yana nufin cewa ‘Allah yakan yi ma ganyaye sutura . . . , balle ku, ku masu-ƙanƙantar bangaskiya?’ Babu shakka zai kula da mu! Almajiran Yesu ba su da bangaskiya sosai. (Mat. 8:26; 14:31; 16:8; 17:20) Suna bukatar su ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su dogara ga Jehobah. Mu kuma fa? Shin muna da bangaskiya cewa Jehobah zai biya bukatunmu kuma zai yi hakan?

17. Mene ne zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah?

17 Karanta Matta 6:31, 32. Kada mu yi koyi da mutanen duniya don ba su da bangaskiya ga Ubanmu na sama. Yana kula da waɗanda suke saka al’amura na Mulki kan gaba a rayuwarsu. Idan muka yi ƙoƙarin tara dukan abubuwan da “al’ummai” suke biɗa, hakan zai ɓata dangantakarmu da Jehobah. Maimakon haka, muna da tabbaci cewa idan muka yi abin da ya kamata mu yi, wato, idan muka saka bautar Jehobah farko a rayuwarmu, zai albarkace mu. Ya kamata “ibada” ta sa mu gamsu da “abinci da sutura” da muke da su.—1 Tim. 6:6-8.

 KANA BARIN MULKIN ALLAH YA ZAMA FARKO A RAYUWARKA?

18. Mene ne Jehobah ya sani game da mu, kuma mene ne zai yi mana?

18 Karanta Matta 6:33. Wajibi ne almajiran Kristi su sa al’amuran Mulki farko a rayuwarsu. Idan muka yi hakan, kamar yadda Yesu ya ce, ‘waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara mana su.’ Me ya sa ya ce hakan? Ya bayyana a cikin ayar da ta gabata cewa: ‘Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka,’ wato abubuwan biyan bukata. Jehobah ya san abin da kake bukata kamar abinci da tufafi da masauki, kafin ma ka san da hakan. (Filib. 4:19) Ya san tufafinmu da suka kusan koɗewa. Ya san irin abincin da muke bukatar mu ci da irin masaukin da ya dace da iyalinmu. Jehobah zai biya dukan bukatunmu.

19. Me ya sa bai kamata mu riƙa damuwa da abin da zai faru a nan gaba?

19 Karanta Matta 6:34. A nan Yesu ya sake cewa: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe.” Yana so mu biya bukatunmu na kowace rana, da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana. Idan mutum yana yawan damuwa game da abin da zai faru a nan gaba, zai soma dogara ga kansa maimakon Allah, kuma hakan zai iya shafan dangantakarsa da Jehobah sosai.—Mis. 3:5, 6; Filib. 4:6, 7.

KA BIƊI MULKIN ALLAH FARKO, JEHOBAH ZAI KULA DA KAI

Shin za ka iya sauƙaƙa rayuwarka don ka ƙara biɗan al’amura na Mulkin Allah? (Ka duba sakin layi na 20)

20. (a) Wane maƙasudi ne za ka iya kafawa a bautarka ga Jehobah? (b) Mene ne za ka iya yi don ka sauƙaƙa rayuwarka?

20 Bai kamata mu yi amfani da dukan kuzarinmu don mu biɗi abin duniya maimakon al’amura da suka shafi bautarmu ga Jehobah ba. Ya kamata mu kafa maƙasudai a ibadarmu. Alal misali, za ka iya ƙaura zuwa ikilisiyar da ake bukatar masu shelar Mulki? Shin za ka iya soma hidimar majagaba? Idan kana hidimar majagaba, shin ka yi tunanin cika fom don halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Za ka iya yin hidima na ɗan lokaci don ka taimaka a Bethel ko kuma a ofishin fassara? Shin za ka iya yin aiki na ɗan lokaci a wurin da ake gina Majami’ar Mulki? Ka yi tunanin yadda za ka sauƙaƙa rayuwarka don ka saka hannu sosai a ayyukan Mulki. Ka yi addu’a kuma ka yi nazarin akwatin nan “ Yadda Za Ka Sauƙaƙa Rayuwarka” da ke shafi na goma. Ƙari ga haka, ka soma ɗaukan matakan da za su sa ka cim ma maƙasudanka.

21. Mene ne zai taimaka mana mu kusaci Jehobah?

21 Ya dace da Yesu ya ce mu biɗi Mulkin Allah ba abin duniya ba. Idan muka yi hakan, ba za mu yi alhini game da bukatunmu ba. Za mu kusaci Jehobah, za mu dogara da shi kuma ba za mu sayi duk wani abin da ake tallarsa da ba ma bukata ko da muna da kuɗin saya ba. Sauƙaƙa rayuwarmu yanzu zai taimaka mana mu sami “rai wanda yake hakikanin rai.”—1 Tim. 6:19.

^ [1] (sakin layi na 12) Don mu san dalilin da ya sa a wani lokaci Jehobah yana iya ƙyale Kirista ya rasa abinci, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2014, shafi na 22.