Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Yuli 2016

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne haɗa sanduna biyu da aka kwatanta a littafin Ezekiyel 37 yake nufi?

Ta bakin annabi Ezekiyel, Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa za su koma Ƙasar Alkawari kuma za su sāke kasancewa da haɗin kai a matsayinsu na al’umma ɗaya. Ƙari ga haka, wannan saƙon ya nuna haɗin kan da zai kasance tsakanin mutanen Allah a kwanaki na ƙarshe.

Jehobah ya gaya wa annabi Ezekiyel ya yi rubutu a kan sanduna biyu. Sandan guda “domin Yahuda, da ’ya’yan Isra’ila abokan zamansa,” ɗayan kuma “domin Yusufu, sandar Ifraimu, domin dukan gidan Isra’ila kuma, abokan zamansa.” Waɗannan sanduna biyun za su “zama . . . sanda ɗaya” a hannun Ezekiyel.—Ezek. 37:15-17.

Mene ne kalmar nan “Ifraimu” take nufi? Jeroboam ya fito daga al’ummar Ifraimu kuma shi ne Sarkin da ya fara sarautar  al’umma goma na Isra’ila. Ƙari ga haka, Ifraimu ne ya fi daraja a cikin dukan sauran al’ummai goma na Isra’ila. (K. Sha. 33:13, 17; 1 Sar. 11:26) Wannan al’ummar ta fito ne daga Ifraimu ɗan Yusufu. (Lit. Lis. 1:32, 33) Yusufu ya sami albarka ta musamman daga wurin mahaifinsa Yaƙubu. Saboda haka, ya dace da aka ƙira sandar da ke wakiltar al’ummar goma na Isra’ila sandar “Ifraimu.” A shekara ta 740 kafin haihuwar Yesu, da daɗewa kafin Ezekiyel ya yi wannan annabcin, sarkin Assuriya ya ci al’umma goma na Isra’ilawa da yaƙi, kuma ya kai su bauta a ƙasarsa. (2 Sar. 17:6) Amma da shigewar lokaci, Babiloniyawa sun ci Assuriyawa da yaƙi. Saboda haka, lokacin da Ezekiyel ya rubuta wannan annabcin game da sanduna biyu, yawancin waɗannan Isra’ilawa sun bazu a ƙasar Babila.

A shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu, Babiloniyawa sun ci masarautar ƙabilu biyu na kudancin Yahuda da yaƙi kuma suka kai su ƙasar Babila don su zama bayi. Wataƙila, mutanen da suka rage daga al’umma goma na Isra’ila ne suka kai bauta a Babila. Sarakunan ƙabilu biyu na kudancin Yahuda sun fito ne daga al’ummar Yahuda, kuma firistoci suna zama ne a Yahudiya domin suna hidima a haikalin da ke Urushalima. (2 Laba. 11:13, 14; 34:30) Shi ya sa aka kira sandar da ke wakiltar ƙabilu biyun, sandar “Yahuda.”

A yaushe ne wannan annabcin ya cika? Annabcin ya cika a shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu, sa’ad da waɗanda suke wakiltan ƙabilu biyu na Yahuda da al’umma goma na Isra’ila suka koma Urushalima don su sake gina haikalin. Hakan ya sa al’ummar Isra’ila ta kasance da haɗin kai kamar dā. (Ezek. 37:21, 22) Annabi Ishaya da kuma Irmiya ma sun yi annabci cewa hakan zai faru.—Isha. 11:12, 13; Irm. 31:1, 6, 31.

Wane abu mai muhimmanci ne aka ambata game da bauta ta gaskiya a wannan annabcin? Amsar ita ce: Jehobah zai sa mutanensa su “zama . . . ɗaya.” (Ezek. 37:18, 19) Shin wannan annabcin yana cika a zamaninmu kuwa? E. Da farko, wannan annabcin ya soma cika ne a shekara ta 1919, sa’ad da Allah ya ’yanta mutanensa daga addinin ƙarya, kuma suka sake kafa bauta ta gaskiya kuma suka sake kasancewa da haɗin kai. Duk ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya ga cewa hakan bai yiwu ba ya bi iska.

A lokacin, yawancin ’yan’uwan da suka soma bauta wa Allah tare suna da begen yin sarauta da Yesu a sama. (R. Yoh. 20:6) Suna kama da sandar Yahuda. Amma da shigewar lokaci, mutanen da suke da begen yin rayuwa a sabuwar duniya suka haɗa kai da waɗanda za su yi sarauta da Yesu. (Zak. 8:23) Waɗannan suna kama da sandar Yusufu kuma ba su da begen yin sarauta da Kristi a sama.

A yau, waɗannan rukunin biyu suna da haɗin kai kuma suna bauta wa Jehobah tare. Ƙari ga haka, Yesu ne sarkinsu. A cikin annabcin da Ezekiyel ya yi, ya kira Yesu Kristi “bawana Dauda.” (Ezek. 37:24, 25) Yesu ya yi addu’a cewa dukan mabiyansa “su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka.” * (Yoh. 17:20, 21) Yesu ya ce waɗanda za su yi sarauta da shi za su zama “garke ɗaya” tare da “waɗansu tumaki,” kuma dukansu za su kasance a ƙarƙashin “makiyayi ɗaya.” (Yoh. 10:16) Kamar yadda Yesu ya ambata, dukan mutanen Allah suna da haɗin kai duk da cewa suna da bege dabam-dabam!

^ sakin layi na 5 Yesu ya yi wa almajiransa kwatanci da yawa sa’ad da yake yi musu bayani game da kwanaki na ƙarshe. Yesu ya ambata “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” wato wani ƙaramin rukunin shafaffu da za su ja-goranci mutanen Allah a bauta ta gaskiya. (Mat. 24:45-47) Bayan haka, sai ya ba da kwatancin da suka shafi dukan waɗanda za su yi sarauta da shi a sama. (Mat. 25:1-30) A ƙarshe, Yesu ya yi magana game da waɗanda suke da begen yin rayuwa a sabuwar duniya kuma za su taimaka wa waɗannan ’yan’uwan Kristi, wato shafaffu. (Mat. 25:31-46) Hakazalika a zamaninmu, annabcin Ezekiyel ya soma cika ne da waɗanda suke da begen yin sarauta da Yesu a sama. Ko da yake al’ummai goma na Isra’ila ba su wakilci waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya har abada ba, amma haɗin kai da aka kwatanta a wannan annabcin ya tuna mana da haɗin kai da ke tsakanin waɗanda suke da begen yin sarauta da Yesu a sama da kuma waɗanda za su yi rayuwa a nan duniya.