Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Yuli 2016

Eric da Amy

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—a Kasar Gana

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—a Kasar Gana

KA SAN wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa da ta ƙaura zuwa ƙasar waje inda ake bukatar masu shela sosai? Shin ka taɓa yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne ya motsa su zuwa hidima a ƙasar waje? Wane shiri ne suka yi don su yi wannan hidimar? Zan iya yin wannan hidimar kuwa?’ Bari mu tambayi waɗannan ’yan’uwa maza da mata don mu sami amsoshin tambayoyin nan.

ME YA SA SUKA ƊAUKI WANNAN MATAKIN?

Me ya sa suka soma tunanin yin hidima a ƙasar waje inda ake bukatar masu shela sosai? Wata ’yar’uwa daga Amirka, mai suna Amy, da ta ba shekara 30 baya, ta ce: “Na yi shekaru ina tunanin yin hidima a ƙasar waje, amma na ɗauka hakan ba zai taɓa yiwuwa ba.” Mene ne ya taimaka mata ta canja ra’ayinta? Ta ci gaba da cewa: “A shekara ta 2004, wasu ma’aurata da suke hidima a ƙasar Belize sun gayyace ni don mu yi hidima tare har tsawon wata ɗaya. Sai na yi hakan kuma na ji daɗinsa sosai! Shekara ɗaya bayan haka, na ƙaura zuwa Gana don in yi hidimar majagaba.”

Aaron da Stephanie

Wasu shekaru da suka shige, wata ’yar’uwa mai suna Stephanie daga Amirka, da ta ba shekara 25 baya ta yi la’akari da yanayinta kuma ta ce wa kanta: ‘Ina da ƙoshin lafiya kuma ba ni da wata ɗawainiya. A gaskiya, zan iya yin hidima ga Jehobah fiye da yadda nake yi a yanzu.’ Wannan tunanin da ta yi ya motsa ta ta ƙaura zuwa Gana don ta daɗa ƙwazo a hidimarta. Filip da Ida ma’aurata ne daga Denmark da suka ba shekara 60 baya kuma sun yi ɗokin yin wa’azi a yankin da ake bukatar masu shela sosai. Sun yi bincike don su cim ma maƙasudinsu. Filip ya ce: “Sa’ad da muka sami damar yin hakan, sai muka ji kamar Jehobah ne ya gaya mana cewa: ‘Lokaci ya yi!’” A shekara ta 2008, sun ƙaura zuwa ƙasar Gana kuma suka yi hidima a wurin fiye da shekara uku.

Brook da Hans

 Hans da Brook, ma’aurata ne da suka ba shekara 30 baya. Suna hidimar majagaba a Amirka. A shekara ta 2005, sun taimaka da aikin agaji bayan an yi wata mahaukaciyar guguwar ruwa da iska, wato Hurricane Katrina. Daga baya, sun cika fom na zuwa aikin gine-gine a ƙasashe dabam-dabam, amma ba a gayyace su ba. Hans ya ce: “Mun saurari wani jawabi a wani babban taro da aka ambata cewa Sarki Dauda bai karaya ba sa’ad da Jehobah ya gaya masa cewa ba zai gina haikali ba, amma ya canja makasudinsa. Hakan ya taimaka mana mu ga cewa ba laifi ba ne mutum ya canja makasudinsa.” (1 Laba. 17:1-4, 11, 12; 22:5-11) Brook ta daɗa cewa, “Jehobah yana so mu yi wata hidima.”

Bayan Hans da Brook sun ji labarai masu daɗi daga abokansu da suka yi hidima a wasu ƙasashe, sai suka soma sha’awar yin hidima a ƙasar waje. A shekara ta 2012, sun je Gana kuma sun yi hidima har tsawon wata huɗu a wata ikilisiyar yaren kurame. Ko da yake sun koma Amirka, amma hidimar da suka yi a Gana ta sa sun daɗa saka mulkin Allah farko a rayuwarsu. Sun taimaka sa’ad da ake gina ofishin Shaidun Jehobah a tsibiran Micronesia.

MATAKAN DA SUKA ƊAUKA DON SU CIM MA MAƘASUDINSU

Ta yaya kuka yi shiri don zuwa hidima a inda ake bukatar masu shela sosai? Stephanie * ta ce: “Na yi bincike a talifofin Hasumiyar Tsaro da suka yi magana a kan yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Ƙari ga haka, na gaya wa dattawan ikilisiyarmu da kuma mai kula da da’ira da matarsa cewa ina so in je wa’azi a ƙasar waje. Mafi muhimmanci, nakan yi addu’a ga Jehobah game da maƙasudina.” Ban da haka, Stephanie ta sauƙaƙa rayuwarta kuma hakan ya taimaka mata ta yi ajiyar kuɗi don biyan bukatunta sa’ad da ta je hidima a ƙasar waje.

Hans ya ce: “Mun yi addu’a ga Jehobah ya ja-gorance mu don mu je duk  inda yake so. Kuma mun ambaci ranar da za mu yi hakan a cikin addu’armu.” Hans da matarsa sun aika wasiƙu zuwa ofisoshin Shaidun Jehobah guda huɗu. Sai ofishin Shaidun Jehobah da ke Gana ya gayyace su, sai suka je ƙasar da niyyar yin hidima na wata biyu. Hans ya ce: “Mun ji daɗin yin hidima tare da ikilisiyar sosai, har muka ɗaga tafiyarmu.”

Adria da George

George da Adria, ma’aurata ne daga Kanada da suka ba shekara 35 baya. Sun yi la’akari da cewa Jehobah zai albarkaci shawarwari masu kyau ne kawai idan ka ɗauki matakan da suka dace. Saboda haka, sun ɗauki matakai da za su sa su cim ma maƙasudinsu. Sun tuntuɓi wata ’yar’uwa da take hidima a inda ake bukatar masu shela sosai a ƙasar Gana kuma suka yi mata tambayoyi da yawa game da ƙasar. Ƙari ga haka, sun rubuta wasiƙa zuwa ofisoshin Shaidun Jehobah da ke Kanada da kuma Gana. Adria ta ce: “Kuma mun yi ƙoƙari mu daɗa sauƙaƙa rayuwarmu fiye da yadda muka yi a dā.” Waɗannan matakan da suka ɗauka ya taimaka musu su ƙaura zuwa Gana don yin hidima a shekara ta 2004.

YADDA SUKE BI DA ƘALUBALE

Waɗanne ƙalubale ne kuka fuskanta bayan kun ƙaura, kuma ta yaya kuka jimre? Amy ta yi fama da kewar gida. Ta ce: “Kome a nan ya bambanta da abubuwan da na saba.” Shin me ya taimaka mata? “Membobin iyalina sun yi ta kira na a waya kuma suna gaya min cewa hidimar da nake yi tana sa su farin ciki. Hakan ya taimaka min in ci gaba da hidimata a nan. Ina yin hira da iyalina ta hanyar sadarwar Intane kuma hakan ya sa muna ganin juna. Saboda haka, sai na soma ji kamar ba su da nisa daga inda nake.” Amy ta ƙara cewa yin abota da wata ’yar’uwa da ta manyanta a yankin ya taimaka mata ta  san al’adu dabam-dabam na mutanen ƙasar. Ta ce: “Nakan je wajen abokiyata a duk lokacin da na kasa fahimtar dalilin da ya sa mutane suke yin wasu abubuwa. Ta taimaka min in san abin da ya kamata in yi da kuma abin da ya kamata in guje wa. Hakan ya taimaka min in yi hidimata da farin ciki.”

George da Adria sun ce sa’ad da suka ƙaura zuwa Gana, sai suka ji kamar sun koma yin rayuwa irin ta mutanen dā. Adria ta ce: “Mun yi amfani da bokiti don wanke kayanmu maimakon injin wanki. Dahuwa takan ɗauki lokaci sosai fiye da yadda muke dahuwa a can ƙasarmu. Amma bayan wani lokaci, sai muka saba da waɗannan ƙalubalen, har ma muna jin daɗinsu.” Brook ya ce: “Duk da waɗannan ƙalubalen da muka fuskanta, mun yi rayuwa mai gamsarwa. Idan muka tuna da duka waɗannan abubuwan da muka shaida, muna jin daɗi cewa mun yi irin wannan rayuwa.”

HIDIMAR DA KE KAWO ALBARKA

Me ya sa za ku ba mutane shawara cewa su yi irin wannan hidimar? Stephanie ta ce: “Yin wa’azi a yankin da za ka haɗu da mutanen da suke son koyan gaskiya da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki a kullum abin farin ciki ne. Ba zan taɓa yin da-na-sanin shawarar da na yi game da zuwa hidima a inda ake bukatar masu shela ba!” A shekara ta 2014, Stephanie ta auri Aaron, kuma a yanzu suna hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Gana.

Wata majagaba mai suna Christine daga Jamus da ta ba shekara 30 ta yi hidima a ƙasar Bolivia kafin ta ƙaura zuwa ƙasar Gana. Ta ce: “Yin hidima a wata ƙasa yana da daɗi sosai.” Ta daɗa cewa: “Da yake ina nesa da iyalina, ina addu’a ga Jehobah ya taimake ni. Hakan ya sa na kasance da dangantaka ta kud ta kud da Jehobah fiye da dā. Ƙari ga haka, na shaida haɗin kai da ke tsakanin mutanen Jehobah. Hakan ya sa na ji daɗin hidimata sosai.” Kwanan baya, Christine ta auri Gideon, kuma suka ci gaba da hidima a Gana.

Christine da Gideon

Filip da Ida sun gaya mana abubuwan da suka yi don su taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su sami ci gaba. Filip ya ce: “A dā, muna da ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 15 ko fiye da hakan, amma yanzu mun rage ɗalibanmu zuwa 10 don mu koyar da su da kyau.” Shin ɗaliban sun amfana daga hakan? Filip ya ce: “Na yi nazari da wani matashi mai suna Michael. Muna yin nazari kullum kuma yana yin shiri da kyau. Hakan ya sa muka gama nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a cikin wata ɗaya. Bayan haka, Michael ya zama mai shela da bai yi baftisma ba. A rana ta farko da ya fita wa’azi, sai ya tambaye ni: ‘Za ka iya taimaka min wajen yin nazari da ɗalibaina?’ Hakan ya ba ni mamaki sosai. Michael ya ce ya soma nazari da ɗalibai uku kuma yana so in taimaka masa sa’ad da yake nazari da su.” Abin ban al’ajabi, domin bukatar da ake da ita na masu wa’azi, hakan ya sa ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun zama masu koyar da Littafi Mai Tsarki!

Ida da Filip

Amy ta bayyana yadda ta fahimci cewa ana bukatar masu wa’azi sosai. Ta ce: “Jim kaɗan bayan mun isa Gana, mun nemi kurame yayin da muke wa’azi a wani ƙaramin ƙauye. Mun sami kurame guda takwas a wannan ƙauyen!” Amy ta auri Eric kuma yanzu suna hidimar majagaba na musamman tare. Suna taimaka wa wata ikilisiyar yaren kurame. Ƙari ga haka, da akwai kurame masu shela fiye da 300 da kuma wasu da suke son saƙonmu a ƙasar. Yin hidima a ƙasar Gana ya ba George da Adria damar zama masu wa’azi a ƙasar waje. Sun yi farin ciki sosai sa’ad da aka gayyace su zuwa aji na 126 na Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. A yau suna hidima a ƙasar Mazambik.

ƘAUNA CE TA MOTSA SU

Ganin ƙoƙarin da ’yan’uwa daga ƙasashen waje suke yi tare da ’yan’uwa maza da mata a yankin, don a cim ma wa’azin bisharar da Yesu ya kwatanta da girbi, abin farin ciki ne sosai. (Yoh. 4:35) A kowane mako, kimanin mutane 120 ne suke yin baftisma a Gana. ’Yan’uwa 17 da suka ƙaura zuwa Gana sun motsa dubban masu wa’azi da suke ƙaunar Jehobah su ba da kansu “da yardan rai” don su yi hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Hakika, aikin da waɗannan ’yan’uwa suke yi yana faranta wa Jehobah rai!—Zab. 110:3; Mis. 27:11.

^ sakin layi na 9 Alal misali, ka duba talifofin nan “Za Ka Iya Yin Hidima a Inda Ake Bukatar Masu Shelar Mulki?” da kuma “Za Ka Iya Ƙetaro Zuwa Makidoniya?” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Afrilu da kuma na 15 ga Disamba, 2009.