Ka tuna lokacin da ka taɓa faɗiwa a ƙasa sa’ad da kake ƙarami? Wataƙila ka ji rauni a hannu ko a ƙafa. Ka tuna yadda mahaifiyarka ta lallashe ka? Wataƙila ta wanke ciwon kuma ta ɗaure shi da bandeji. Babu shakka, ka yi kuka amma yadda ta lallashe ka ya sa ka ji sauƙi. A lokacin, akwai mutanen da ke gaggauta wajen ƙarfafa ka.

Amma yayin da kake daɗa girma, abubuwa suna canjawa. Matsalolinka suna daɗa ƙaruwa kuma mutane ba sa saurin ƙarfafa ka. Abin baƙin cikin shi ne, ba a iya magance matsalolin manya kamar na ƙaramin yaron da muka ambata ɗazun. Ka yi la’akari da waɗannan misalan.

  • Shin an taɓa sallamar ka daga aiki? Yaya ka ji a lokacin? Wani mai suna Julian ya ce sa’ad da aka sallame shi daga aiki, hankalinsa ya tashi sosai. Sai ya soma tunani: ‘Ta yaya zan biya bukatun iyalina? Me ya sa kamfanin nan suka wulaƙanta ni haka bayan na daɗe ina musu aiki?’

  • Wataƙila abin da ke tayar maka da hankali shi ne aurenka da ya mutu. Wata mai suna Raquel ta ce: “Na yi baƙin ciki sosai sa’ad da maigidana ya sake ni shekara ɗaya da rabi da ya gabata. Na ji kamar zuciyata ta fashe. Jikina ya mutu gabaki ɗaya kuma na tsorata ainun.”

  • Mai yiwuwa kana fama da ciwo mai tsanani kuma ba ka samun sauƙi. A wasu lokuta, kana iya ji kamar Ayuba sa’ad da ya ce: “Ina ƙyamar raina, ba ni so in zauna har abada.” (Ayuba 7:16) Wataƙila kai ma kana ji kamar wani ɗan shekara 80 da wani abu mai suna Luis da ya ce: “A wasu lokuta, ina ji kamar abin da nake jira kawai shi ne mutuwa.”

  • Wataƙila kana bukatar ƙarfafa domin wani naka ya rasu. Wani mai suna Robert ya ce: “Sa’ad da na ji cewa ɗana ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin sama, ban yarda cewa hakan ya faru ba. Bayan haka, sai na soma baƙin ciki irin wanda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta da sukar takobi.”​—Luka 2:35.

Robert da Luis da Raquel da kuma Julian sun sami ƙarfafa a waɗannan mawuyacin yanayi. Allah Maɗaukaki ya ba su ƙarfafar da suke bukata. Ta yaya yake ƙarfafa mu? Zai ƙarfafa ka kuwa?