Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro  |  Na 5 2016

Mene ne Mulkin Allah?

Mene ne Mulkin Allah?

Mene ne Mulkin Allah?

WASU SUN CE sarautar da Allah yake yi a cikin zuciyar mutum ne; wasu kuma sun ce yana nufin ƙoƙarin da ‘yan Adam suke yi don su kawo salama da haɗin kai a duniya. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, . . . za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na ‘yan Adam] ya cinye su.” (Daniyel 2:44) Mulkin Allah gwamnati ce ta gaske.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Mulkin Allah yana iko a sama.Matta 10:7; Luka 10:9.

  • Allah yana amfani da Mulkinsa wajen cim ma nufinsa a sama da duniya.Matta 6:10.

Yaushe ne Mulkin Allah zai zo?

ME ZA KA CE?

  • Babu wanda ya sani

  • Nan ba da daɗewa ba

  • Ba zai taɓa zuwa ba

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Da zarar an yi wa’azin bisharar nan a ko’ina, Mulkin zai cire dukan muguntar da ke faruwa a duniyar nan.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Babu kowa a duniya da ya san ranar da Mulkin Allah zai zo.Matta 24:36.

  • Annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mulkin zai zo nan ba da daɗewa ba.Matta 24:3, 7, 12.