Manzo Bulus ya ce Jehobah, * Allah ne na ‘dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.’ (2 Korintiyawa 1:​3, 4) Ayar nan ta tabbatar mana da cewa babu mutumin da ya fi ƙarfi Allah ya ƙarfafa shi kuma babu matsalar da za ta same mu da Jehobah ba zai iya ƙarfafa mu ba.

Babu shakka, muna bukatar mu ɗauki mataki idan muna so Allah ya ƙarfafa mu. Shin zai yiwu likita ya yi mana jinya idan ba mu je asibiti ba ko kuma ba mu ce muna son ganinsa ba? Annabi Amos ya ce: “Mutum biyu za su iya yin tafiya tare, in ba sun rigaya sun yi alkawari ba?” (Amos 3:3) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mu kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare mu.’​—⁠Yaƙub 4:⁠8.

Mene ne zai iya tabbatar mana da cewa Allah zai kusato gare mu? Da farko, domin ya gaya mana sau da sau cewa yana so ya taimake mu. (Ka duba  akwatin da ke shafi na 5.) Na biyu kuma, domin akwai mutane a zamaninmu da kuma zamanin dā waɗanda Allah ya ƙarfafa su.

Mutane da yawa a yau da ke neman taimakon Allah suna kamar Sarki Dauda domin ya fuskanci matsaloli dabam-dabam. Akwai wani lokacin da ya roƙi Jehobah ya ce: “Ka ji muryar addu’o’ina, sa’anda ina yi maka kuka.” Shin Allah ya amsa addu’o’insa? Ƙwarai kuwa. Shi ya sa ya ƙara da cewa: “Na sami taimako: domin wannan zuciyata tana murna ƙwarai.”​—⁠Zabura 28:​2, 7.

YADDA YESU YA ƘARFAFA DUKAN MASU MAKOKI

Allah yana so Yesu ya kasance a kan gaba wajen ƙarfafa mutane. Ɗaya daga cikin ayyukan da Allah ya ɗanka masa shi ne ya “warkar da masu-karyayyen zuciya” kuma ya “yi wa dukan masu-makoki ta’aziyya.” (Ishaya 61:​1, 2) Yesu ya cika annabcin domin ya kasance a kan gaba wajen ƙarfafa mutanen da ke “wahala, masu-nauyin kaya kuma.”​—Matta 11:​28-30.

Yesu ya ƙarfafa mutane ta wajen ba su shawarwari masu kyau da yadda ya bi da su da kuma a wasu lokuta, yadda ya warƙar da su. Akwai wata rana da wani kuturu ya roƙi Yesu ya ce: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Sai Yesu ya ji tsausayin mutumin sosai kuma ya ce: “Na yarda; ka tsarkaka.”  (Markus 1:​40, 41) A sakamakon haka, kuturun ya warke.

A yau, Yesu ba ya duniya kuma ba zai iya ƙarfafa mu ido da ido ba. Amma Jehobah wanda shi ne “Allah na dukan ta’aziyya,” yana ci gaba da taimaka wa mutanen da ke cikin matsala. (2 Korintiyawa 1:3) Ka yi la’akari da hanyoyi huɗu da Allah yake amfani da su wajen ƙarfafa mutane.

  • Littafi Mai Tsarki. “Gama iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.”​—⁠Romawa 15:⁠4.

  • Ruhu Mai Tsarki na Allah. Jim kaɗan bayan Yesu ya mutu, ikilisiyar Kirista gabaki ɗaya ta shiga lokacin salama. Me ya sa? Domin ta yi ‘tafiya cikin tsoron Ubangiji, bisa ga ta’aziyar ruhu mai-tsarki.’ (Ayyukan Manzanni 9:31) Ruhu mai tsarki, wato ikon da Allah yake amfani da shi wajen cim ma nufinsa yana da ƙarfi sosai. Allah zai iya yin amfani da wannan ruhun wajen ƙarfafa kowane mutum da ke fuskantar kowane irin yanayi.

  • Addu’a. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu.” Maimakon haka, ya ce: “Ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku.”​—⁠Filibiyawa 4:​6, 7.

  • ʼYan’uwa Kiristoci abokan kirki ne kuma za su iya ƙarfafa mu sa’ad da muke cikin tsaka mai wuya. Manzo Bulus ya ce abokan aikinsa sun ‘yi masa ta’aziyya’ sa’ad da yake fuskantar ‘wahala da ƙunci.’​—⁠Kolosiyawa 4:11; 1 Tasalonikawa 3:⁠7.

Amma wataƙila kana tunanin yadda hakan zai iya yiwuwa. Bari mu yi la’akari da labaran mutanen da muka ambata ɗazun. Za ka iya zama kamar su domin sun shaida cewa har ila, Allah yana cika wannan alkawarin: “Kamar wanda uwatasa take yi masa ta’aziya, haka nan zan ta’azantar da ku.”​—⁠Ishaya 66:⁠13.

^ sakin layi na 3 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.