Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro  |  Na 4 2016

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

Littafi Mai Tsarki Bai Rube Ba

Littafi Mai Tsarki Bai Rube Ba

ƘALUBALE: Fata da takardar ganye ne asalin abubuwan da marubuta da kuma mutanen da suka kofe Littafi Mai Tsarki suka yi amfani da su. (2 Timotawus 4:13) Ta yaya fata da kuma takardar ganye suka sa adana rubutun Littafi Mai Tsarki ya zama da wuya?

Takardar ganye tana saurin yagewa ko kuma koɗewa. Wasu ’yan bincike a ƙasar Masar, Richard Parkinson da Stephen Quirke sun ce: “Takardar da aka yi da ganye za ta iya ruɓewa kuma ta zama zare-zare ko kuma gari-gari. Idan aka adana ta, za ta iya kumbura ko ta jiƙe ko kuma ƙwari da ɓeraye su cinye ta. Idan aka binne takardar kuma, gara suna iya yin kaca-kaca da ita.” Wasu littattafan da aka samo sun lalace ba tare da ɓata lokaci ba domin rana ko danshi sun yi musu yawa.

Fata kuma ta fi takarda da aka yi da ganye jurewa, amma shi ma yana iya lalacewa idan aka bar shi a rana ko a wurare masu danshi ko kuma wuri mai zafi sosai. * Ƙwari suna son cin fata. Shi ya sa aka kasa adana littattafai da dama na dā. Da a ce Littafi Mai Tsarki ya ruɓe kamar sauran littattafai, da ba mu san saƙon da ke cikinsa ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Dokar da aka ba Yahudawa ta ce kowane sarki ya “sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki,” wato littattafai biyar da Musa ya rubuta. (Kubawar Shari’a 17:18, Littafi Mai Tsarki) Amma ƙwararrun marubuta da yawa sun kofe Littafi Mai Tsarki sau da yawa har ya zama cewa a ƙarni na farko, akwai nassosi a dukan majami’u a Isra’ila da Makidoniya. (Luka 4:16, 17; Ayyukan Manzanni 17:11) Yaya aka yi waɗannan tsofaffin littattafan suka tsira har wa yau?

An adana Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri ƙarnuka da dama a cikin tuluna a kogon dutse marar danshi

Wani masanin Littattafan Sabon Alkawari mai suna Philip W. Comfort ya ce: “Yahudawa suna yawan saka irin waɗannan littattafan ne a cikin tuluna don kada su lalace.” Hakan ma Kiristoci suka ci gaba da adana su. An samo wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki na dā a cikin tuluna da ƙananan ɗakuna da kogon dutse da kuma wuraren da babu danshi.

SAKAMAKO: Hakan ya sa dubban littattafai na Littafi Mai Tsarki na dā sun tsira har wa yau, wato kusan shekara 2,000 ke nan. Babu wani littafi da ya jure kamar Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 5 Alal misali, an rubuta littafin nan U.S. Declaration of Independence (Wa’adin Samun ’Yanci na Ƙasar Amurka) a fata shekaru 250 da suka shige. Amma yanzu, littafin ya koɗe sosai har ma da ƙyar ake iya gane abin da aka rubuta a ciki.