Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

Labari Mai Muhimmanci

Labari Mai Muhimmanci

Littafi Mai Tsarki ya yi dabam da sauran littattafan addinai. Babu wani littafi da ya daɗe yana gyara rayuwar mutane da yawa kamar Littafi Mai Tsarki. Har ila, babu wani littafin da aka kushe da kuma yi mahawwara a kai kamarsa.

Alal misali, wasu masana ba su yarda cewa Littafi Mai Tsarki da muke da shi a yau ɗaya yake da wanda aka fara wallafawa ba. Wani farfesan addini ya ce: “Mu dai ba mu da tabbaci cewa Littafi Mai Tsarki da muke da shi yanzu ya yi daidai da wanda aka fara wallafawa ba. Littattafan da muke da su yanzu suna cike da kura-kurai kuma an kofe yawancinsu ƙarnuka da yawa bayan na farko. Saboda haka, sun bambanta a hanyoyi da yawa.”

Wasu kuma suna shakkar Littafi Mai Tsarki don abin da addininsu ya koya musu. Alal misali, wani mai suna Faizal ya ce iyayensa da ba Kiristoci ba sun koya masa cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce amma an canja saƙon da ke cikinsa. Ya ce: “Don haka, idan ana min zance game da Littafi Mai Tsarki, ba na cika yarda da shi. An canja Littafi Mai Tsarki, kuma waɗanda ake da su yanzu ba ɗaya ba ne da waɗanda aka fara wallafawa!”

Shin ya kamata mu damu ko an canja Littafi Mai Tsarki ko a’a? Ka yi la’akari da waɗannan tambayoyin: Za ka iya gaskatawa da alkawuran Littafi Mai Tsarki na yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba, idan ba ka san ko alkawuran suna cikin Littafi Mai Tsarki na farko ba? (Romawa 15:4) Shin za ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don yanke shawarwarin da suka shafi aiki da iyali da kuma bauta idan abin da ke cikinsa ra’ayin mutane ne kawai?

Ko da yake a yau, babu kofofin Littafi Mai Tsarki da aka fara wallafawa, duk da haka, za mu iya bincika wasu dubban kofofin Littafi Mai Tsarki na dā. Ta yaya aka adana waɗannan littattafai don kada su ruɓe? Kuma ta yaya suka tsira duk da hamayya da kuma ƙoƙarin da mutane suka yi don su canja saƙon da ke cikinsa? Ta yaya hakan ya tabbatar maka da cewa saƙon da ke cikin naka Littafi Mai Tsarki daidai ne? Ka yi la’akari da amsoshin waɗannan tambayoyin a cikin talifofi na gaba.