Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ka Sani?

Ka Sani?

Me ya sa yadda Yesu ya bi da kutare ya yi dabam da yadda wasu suka bi da su?

A dā, Yahudawa suna tsoron kamuwa da cutar kuturta. Wannan cutar tana iya sa jijiyoyin mutum su riƙa zafi, har wata gaɓar jikinsa ta gutsure. A lokacin, cutar kuturta ba ta da magani. Ana keɓe kutaren a wani wuri kuma idan za su shiga cikin jama’a, suna sanar da su cewa su kutare ne.—Levitikus 13:45, 46.

Ban da dokokin da Allah ya bayar a kan cutar kuturta, limaman Yahudawa sun ƙara nasu dokoki, kuma hakan ya sa rayuwa ta yi wa kutare wuya sosai. Alal misali, limaman sun ce idan kuturu yana so ya zo kusa da wani da ba shi da cutar, ya ba shi ratar wajen kafa shida. Amma idan ana iska sosai, kuturun ya ba shi ratar wajen kafa ɗari da hamsin, wato mita 45. Wasu kuma cikin limaman masu tsattsaurar ra’ayi sun ce dokar da Allah ya bayar cewa kuturu ya kasance a “bayan sansani,” yana nufin cewa kada su zauna cikin birnin. Akwai wani malamin da yake jifar kutare da duwatsu a cikin birnin kuma ya riƙa gaya musu: “Ku koma wurin da aka keɓe muku don kar ku ƙazantar da sauran jama’a.”

Hakan ya yi dabam da yadda Yesu ya bi da kutare! Maimakon ya kore su, ya taɓa su har ma ya warkar da su.—Matta 8:3.

Waɗanne laifuffuka ne limaman Yahudawa suka ce za su iya sa a kashe aure?

Takardar kashe aure da aka rubuta tsakanin shekara ta 71 da 72 B.H.Y.

Malaman addinai sun yi muhawwara sosai a kan wannan batun a ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu. Akwai wani lokaci da Farisawa suka yi wa Yesu tambaya don su gwada shi. Sun ce: “Halal ne mutum ya saki mata tasa a kan kowane dalili?”—Matta 19:3, Littafi Mai Tsarki.

Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta amince mutum ya saki matarsa idan “ya iske wani abin da ba daidai ba a gareta.” (Kubawar Shari’a 24:1) A zamanin Yesu, akwai wasu rukunoni biyu da ake kira Shammai da Hillel da ra’ayinsu game da ma’anar dokar nan bai jitu ba. ʼYan Shammai sun yarda cewa zina ce kaɗai za ta iya sa a kashe aure. ʼYan Hillel kuma sun ce miji zai iya kashe aure idan matarsa ta yi kowane irin laifi. Abin ʼyan Hillel suke nufi shi ne mutum zai iya sakan matarsa idan ba ta iya dafa abinci ba ko kuma ya ga wata macen da ta fi ta kyau.

To, wace amsa ce Yesu ya ba wa Farisawa da suka yi masa tambaya? Ya gaya musu dalla-dalla cewa: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina yake yi.”—Matta 19:6, 9.