Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?

Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?

Ba a iya halaka Littafi Mai Tsarki ba, shi ya sa za mu iya samun namu kofin a yau. Kuma idan ka zaɓi juyin Littafi Mai Tsarki mai kyau, babu shakka, za ka ga cewa abin da kake karantawa ya yi daidai da wanda aka fara wallafawa. * Amma me ya sa Littafi Mai Tsarki ya tsira duk da cewa an rubuta shi a kan abubuwan da za su iya lalacewa kuma ʼyan hamayya sun yi ƙoƙarin halaka shi da kuma canja saƙon da ke cikinsa? Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya fi sauran littattafai?

“Yanzu na yarda cewa Littafi Mai Tsarki da nake da shi kyauta ce daga Allah”

Ra’ayin ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa ya yi daidai da na manzo Bulus wanda ya ce: “Kowane Nassi hurarre na Allah ne.” (2 Timotawus 3:16, Littafi Mai Tsarki) Sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki ya tsira don Kalmar Allah ce kuma don Allah ne da kansa ya kāre shi har wa yau. Faizal da aka ambata a farkon wannan mujallar ya tsai da shawarar bincika Littafi Mai Tsarki da kansa don ya ga ko Kalmar Allah ce da gaske. Abin da ya gano daga binciken ya ba shi mamaki sosai. Ya fahimci cewa abubuwa da dama da ake koyarwa a coci ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya yi farin cikin koyon dalilin da ya sa Allah ya halicci mutane.

Ya ce: “Yanzu na yarda cewa Littafi Mai Tsarki da nake da shi kyauta ce daga Allah. Tun da Allah yana da ikon halittar sama da ƙasa, ai ba zai yi masa wuya ya ba mu littafi kuma ya kāre shi ba. Idan muka ce ba zai iya yin haka ba, muna raina ikon da Allah Maɗaukaki yake da shi ke nan! Kuma waye ne ni da zan raina ikon Allah?”—Ishaya 40:8.

^ sakin layi na 3 Ka duba talifin nan “How Can You Choose a Good Bible Translation?” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2008 na Turanci.