MENE NE ZAI FARU A NAN GABA?

Ka taɓa tunanin yadda rayuwarka da na iyalinka za ta kasance a nan gaba? Littafi Mai Tsarki ya ce:

“Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.”​—Zabura 37:29.

Mujallar Hasumiyar Tsaron nan za ta taimaka maka ka san alkawarin da Allah ya yi game da mutane da kuma duniya da kuma abin da za ka yi don ka more albarkar nan.