Da farko mun ba ku labarin yadda bokar da ke Delphi ta ruɗi Croesus kuma hakan ya sa sarkin Fasiya ya ci shi da yaƙi. Amma Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da sarkin Fasiya kuma annabcin ya cika daidai yadda aka yi shi.

Shekaru 200 kafin annabcin ya cika kuma kafin a haifi sarki Sayirus, annabi Ishaya ya yi annabci da sunan Sayirus kuma ya ce shi ne zai halaka babban birnin Babila.

Ishaya 44:​24, 27, 28: “In ji Yahweh, . . . Ni ne na cewa zurfin teku, ‘Ka bushe, zan kuma busar da rafuffukanka.’ Ni ne na ce wa Sarki Sayirus, ‘Ga shi, na mai da kai makiyayi, kai ne za ka cika dukan manufata.’ Ni ne na ba da umurni cewa ‘A sake gina Urushalima, a kuma kafa tushen ginin Haikalin.’ ”

Wani masanin tarihin Helenanci mai suna Herodotus ya ce, sojojin Sayirus sun raba kogin Yufiretis wanda ya wuce ta ƙofar birnin Babila. Dabarar da Sayirus ya yi, ya sa sojojinsa sun iya haye kogin. Bayan ya ci birnin da yaƙi, Sayirus ya sallami Yahudawa da suke zaman bauta a Babila don su koma Urushalima su sake gina birnin da aka rushe shi shekaru 70 da suka shige.

Ishaya 45:1: “Ga abin da Yahweh ya ce wa Sarki Sayirus, wanda ya zaɓa ya kuma naɗa. “Na kama hannunka na dama na ba ka ƙarfin da za ka tattake al’ummai, ka tumɓuke sarakuna daga mulkinsu. Zan kuma buɗe ƙofofin birane dominka.”

Sojojin Fasiyan sun shiga ta manyan ƙofofi guda biyu na birnin domin mutanen Babila sun bar ƙofofin birnin a buɗe. Da a ce mutanen Babila sun san abin da Sayirus yake so ya yi, da sun rufe manyan ƙofofin birnin. Amma, ba su yi hakan ba.

Wannan annabcin ɗaya ne kawai daga cikin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika. * Ba kamar hasashe da mutane suke yi ta wurin allolinsu na ƙarya ba, annabcin Littafin Mai Tsarki ya fito daga wurin Wanda ya ce: “Na bayyana ƙarshen abu tun daga farkonsa, tun daga kwanakin dā, abin da bai faru ba.”​— Ishaya 46:10.

Allah na gaskiya wanda sunansa Jehobah ne kawai zai iya yin wannan hasashen. Sunansa yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Sunan ya nuna cewa yana da ikon sa abu ya kasance a nan gaba don  ya cim ma nufinsa. Ya kuma tabbatar mana cewa zai cika dukan abin da ya yi alkawarinsu.

ANNABCE-ANNABCEN DA SUKE CIKA A YAU

Za ka so ka san annabcin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da zamaninmu? Wajen shekaru 2,000 da suka shige, Littafi Mai Tsarki ya ce, “za a sha wuya ƙwarai” a “zamanin ƙarshe.” Ƙarshen me ke nan? Ba ƙarshen duniya ko na ’yan Adam ba, amma ƙarshen wahala da tsanantawa da cin zali da kuma abubuwan da ’yan Adam suka yi shekaru da yawa suna fama da su. Bari mu yi la’akari da kaɗan daga cikin annabce-annabcen da suka nuna cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe.

2 Timoti 3:​1-5: “A zamanin ƙarshe . . .  mutane za su zama masu son kai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zage-zage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka, da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta, da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah, suna riƙe da siffofin ibada, amma suna saɓa wa ikonta.”

Ka yarda cewa mutane da yawa suna da irin wannan halin a yau? Ka lura cewa mutane a duniya suna son kansu da kuɗi kuma suna da girman kai? Ka kuma lura cewa mutane ba sa nuna godiya kuma ba sa yarda da wasu? Hakika, ka kuma lura cewa rashin biyayya ya zama gama gari kuma mutane sun fi son kayan duniya fiye da Allah. Irin waɗannan halayen ƙaruwa suke yi a kullum.

Matiyu 24:​6, 7: “Za ku kuma ji labaran yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu. . . . Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.”

Wani bincike da aka yi ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 100 ne suka mutu sakamakon yaƙi tun daga 1914. Adadin ya fi na yawan mutane a wasu ƙasashe. Ka yi tunanin irin baƙin cikin da hakan ya kawo. Shin ƙasashen sun koyi darasi daga hakan kuma suka daina yaƙi ne?

Matiyu 24:7: “Za a kuma yi yunwa da rawar ƙasa a wurare dabam-dabam.”

Ƙungiyar da Ke Kula da Abinci Na Duniya ta ce: “A yau muna ƙoƙari mu tanadar da isashen abinci don kowa da kowa. Duk da haka, mutane miliyan 815, wato mutum ɗaya cikin mutane tara sukan kwana da yunwa a kullum.” Fiye da hakan, mutum ɗaya a cikin mutane uku ba sa cin isashen abinci.” Bincike ya kuma nuna cewa a kowace shekara, yara miliyan uku ne suke mutuwa a sakamakon yunwa.

Luka 21:11: “Za a yi mummunar rawar ƙasa.”

Kowace shekara, ƙasa takan yi rawa sosai aƙalla sau 50,000. Akan yi girgizar ƙasa aƙalla sau 100 kuma hakan yakan lalata gidaje, sa’an nan akan yi aƙalla girgizar ƙasa sau ɗaya da ke ɓarna sosai a kowace shekara. Wani bincike kuma ya nuna cewa tun daga 1975 zuwa 2000, mutane 471,000 sun mutu a sakamakon girgizar ƙasa.

Matiyu 24:14: “Za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.”

Shaidun Jehobah da suka kai fiye da miliyan takwas, suna yaɗa bisharar Mulkin Allah a dukan duniya a cikin ƙasashe 240. Suna yin shelar Mulkin Allah a manyan birane da ƙauyuka da gonaki da kuma tuddai. Annabcin ya ce bayan an yi wa’azin yadda Allah yake so, ‘Sa’an nan ƙarshen zai zo.’ Me hakan yake nufi? Hakan yana nufin za a kawo ƙarshen gwamnatocin ’yan Adam, a kuma maye gurbinsu da Mulkin Allah. Wanne annabci ne zai cika a ƙarƙashin Mulkin Allah? Ka ci gaba da karatu don ka san da hakan.