Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 

Amfanin Zama Mai Gaskiya

Amfanin Zama Mai Gaskiya

“Muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”Ibraniyawa 13:18.

A Littafi Mai Tsarki, asalin kalmar Helenanci da a wasu lokatai ake fassara zuwa “yin gaskiya” tana nufin “wani abu mai kyan gaske.” Ƙari ga haka, yana iya nufin hali mai kyau.

Manzo Bulus ya ce, ‘Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.’ Kuma Kiristoci suna ɗaukan wannan furucin da muhimmanci. Mene ne yin haka ya ƙunsa?

KOKAWAR DA MUKE YI

Yawancin mutane sukan kalli kansu a madubi kowace safiya kafin su fita yin harkokinsu na yau da kullum. Me ya sa? Domin suna so su yi kyau. Amma akwai abubuwan da suka fi gyaran gashi ko kuma saka kaya masu kyau muhimmanci. Hakika, halinmu zai iya sa mu yi kyau ko muni.

Kalmar Allah ta faɗi dalla-dalla cewa muna yawan son yin abu marar kyau. Littafin Farawa 8:21, ya ce: “Tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.” Saboda haka, wajibi ne mu yi kokawa ko ƙoƙari sosai wajen kawar da wannan banzan halin. Manzo Bulus ya kwatanta irin kokawa ko ƙoƙarin da yake yi wajen daina yin zunubi, ya ce: “Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da Shari’ar Allah. Amma ina ganin wata ƙa’ida dabam a gaɓoɓina, wadda ke yaƙi da ƙa’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa’idan nan ta zunubi, wadda ke zaune a gaɓoɓina.”Romawa 7:22, 23, Littafi Mai Tsarki.

Alal misali, idan zuciyarmu ta motsa mu mu yi abu marar kyau ko kuma muna yawan son yin rashin gaskiya, ba lallai sai mun bi zuciyarmu ba. Mu ne za mu iya zaɓan abin da za mu yi. Idan muka tsai da shawarar ƙin mugun tunani, za mu kasance masu yin gaskiya ko da yake mutane da yawa ba sa yin gaskiya.

YADDA ZA MU YI NASARA

Muna bukatar ɗabi’a mai kyau sosai don mu zama masu gaskiya. Abin baƙin ciki shi ne, mutane da yawa sun fi mai da hankali ga ‘saka tufafi masu kyau’ maimakon kasancewa da halaye masu kyau. A sakamakon haka, sukan ba da hujja sa’ad da suka yi rashin gaskiya don su kāre kansu. Littafin nan The (Honest) Truth About Dishonesty (Gaskiya Game da Rashin Gaskiya) ya ce: “Mukan cuci mutane yadda ba za su gane cewa mu masu rashin gaskiya ba ne don mu kāre mutuncinmu.” Shin da akwai ƙa’idar da za ta taimaka mana mu san ko akwai irin rashin gaskiyan da ba laifi ba ne? Ƙwarai kuwa.

Miliyoyin mutane a faɗin duniya sun gano cewa Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya taimaka mana. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki yana koyar da ɗabi’ar da babu kamarta. (Zabura 19:7) Yana mana ja-gora a batun zaman iyali da aiki da ɗabi’a da kuma dangantakarmu da Allah. Mutane sun daɗe suna amfani da shi. Dokokinsa da ƙa’idodinsa suna  da amfani ga dukan mutane. Idan muka bincika Littafi Mai Tsarki da kyau, muka yi bimbini a kansa kuma muka yi amfani da abin da muka karanta, za mu iya sanin yadda za mu riƙa yin gaskiya da kuma adalci.

Amma, ba samun ilimin Littafi Mai Tsarki ne kawai zai sa mu yi nasara wajen daina rashin gaskiya ba. Me ya sa? Domin muna rayuwa ne a duniyar da mutane suke ƙoƙari su rinjaye mu mu bi ɗabi’u marasa kyau. Shi ya sa muke bukatar mu yi addu’a don Allah ya taimake mu. (Filibiyawa 4:6, 7, 13, LMT) Yin hakan zai taimaka mana mu sami ƙarfin zuciyar yin abin da ya dace da kuma kasancewa masu gaskiya a harkokinmu na yau da kullum.

SAKAMAKON YIN GASKIYA

Hitoshi da aka ambata a talifi na farko na wannan mujallar ya yi nasara wajen kasancewa mai gaskiya. Yanzu yana aiki da shugaban da ke son masu yin gaskiya. Hitoshi ya ce: “Ina farin ciki cewa yanzu ina aikin da ke ba ni damar kasancewa da lamiri mai tsabta.”

Wasu ma sun amince da abin da ya faɗa. Ka yi la’akari da misalan wasu da suka amfana daga bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki na kasancewa da “tasarrufin kirki cikin dukan abu.”

 • Lamiri Mai Kyau

  “Na bar makaranta sa’ad da nake ‘yar shekara 13 don in yi aiki da ɓarayi. A sakamakon haka, kashi casa’in da biyar cikin ɗari na kuɗin da nake samu daga yin maguɗi ne. Daga baya, sai na yi aure kuma ni da mijina muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Mun canja salon rayuwarmu domin mun koyi cewa Jehobah * ya tsani rashin gaskiya. Mun yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a shekara ta 1990.”Misalai 6:16-19.

  “A dā, gidana ya cika da kayan sata amma yanzu babu kayan sata a gidana kuma hakan ya sa na kasance da kwanciyar hankali. Idan na tuna yawan shekarun da na yi ina cucin mutane, ina gode wa Jehobah don ya nuna mini jin ƙai. Ina samun kwanciyar hankali sa’ad da nake barci da dare don na san cewa yanzu Jehobah yana amincewa da ni.”—In ji Cheryl a ƙasar Ireland.

  “Sa’ad da shugabana ya gano cewa na ƙi karɓan cin hanci daga wani kwastomanmu, sai ya ce mini: ‘Allahnka ne ya sa kake da irin wannan hali mai kyau! Muna farin cikin yin aiki tare da kai a wannan kamfanin.’ Yin gaskiya a harkokin yau da kullum yana taimaka mini in kasance da lamiri mai kyau a gaban Jehobah Allah. Hakan na kuma ba ni zarafin taimaka wa iyalina da kuma wasu su riƙa yin gaskiya.”—In ji Sonny a ƙasar Hong Kong.

 • Kwanciyar Hankali

  “Na yi aiki a matsayin mataimakin shugaba a wani babban banki. A wannan sana’ar, neman arziki ya fi yin gaskiya muhimmanci. Ra’ayin yawancin mutane shi ne, ‘Ba laifi ba ne a yi ɗan maguɗi don a sami ƙarin kuɗi ko kuma a bunƙasa tattalin arziki.’ Amma ina da kwanciyar hankali domin ina yin gaskiya. Na tsai da shawara cewa zan riƙa yin gaskiya ko da me zai faru. Shugabannina sun san cewa ba zan yi musu ƙarya ba kuma ba zan taya su yin ƙarya ba.”—In ji Tom a Amirka.

 • Mutunci

  “Shugabana ya gaya mini in yi ƙarya don wasu kayayyakin da suka ɓata, amma na ƙi. Da aka kama ɓarayin, mai kamfanin ya gode mini don matakin da na ɗauka. Kasancewa mai gaskiya a duniyar da ake rashin gaskiya sosai yana bukatar ƙarfin zuciya. Amma idan muka yi hakan, mutane za su yarda da mu kuma su mutunta mu.”—In ji Kaori a ƙasar Jafan.

Kasancewa da lamiri mai tsabta da kwanciyar hankali da kuma mutunci ya nuna cewa zama mai gaskiya ba tsohon yayi ba ne, ko ba haka ba?

^ sakin layi na 18 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.