An kashe Yesu Banazare a shekara ta 33. Me ya sa? An ce ya yi saɓo, saboda haka, aka yi masa dūkan tsiya kuma aka kafa shi a kan gungume. Ya sha azaba sosai kafin ya mutu. Amma Allah ya ta da shi daga mutuwa kuma bayan kwana 40, Yesu ya koma sama.

Mun samo wannan labarin daga Linjilar da ke Nassosin Helenanci da ake yawan kira Sabon Alkawari. Shin wannan labarin ya faru kuwa da gaske? Wannan tambayar tana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin idan bai faru ba, to bangaskiyarmu banza ce kuma begenmu na yin rayuwa har abada a cikin Aljanna ƙage ne kawai. (1 Korintiyawa 15:14) Amma idan ya faru da gaske, ‘yan Adam suna da bege kuma za su iya gaya wa mutane wannan begen. To, shin labaran da ke cikin Linjila gaskiya ne ko kuma ƙage?

ABIN DA YA SA HAKAN GASKIYA NE

Linjila ba tatsuniya ba ce, labaran da ke cikinta sun faru da gaske. Alal misali, sunayen wurare da yawa da aka ambata gaskiya ne domin har yau akwai waɗannan wuraren. Sun yi magana game da mutanen da suka wanzu da gaske, kuma sun jitu da sunayen da ‘yan tarihi suka gano.Luka 3:1, 2, 23.

 Marubutan da suka rayu a ƙarni na ɗaya da na biyu ma sun yi magana game da Yesu. * Bayanan da aka yi a cikin Linjilar game da yadda aka kashe Yesu ya yi daidai da yadda Romawa suke hukunta mutane a lokacin. Ƙari ga haka, abubuwan da aka ambata a ciki sun faru da gaske kuma an rubuta kura-kuran da wasu almajiran Yesu suka yi. (Matta 26:56; Luka 22:24-26; Yohanna 18:10, 11) Waɗannan abubuwan sun tabbatar mana da cewa marubutan Linjila sun faɗi gaskiya kuma abubuwan da suka ce game da Yesu daidai ne.

TASHIN YESU DAGA MUTUWA KUMA FA?

Ko da yake mutane da yawa sun yarda cewa Yesu ya rayu a duniya kuma ya mutu, amma wasu ba su amince da tashinsa daga mutuwa ba. Almajiransa ma ba su yarda ba sa’ad da aka fara gaya musu cewa Yesu ya tashi daga mutuwa. (Luka 24:11) Amma sun daina shakka sa’ad da su da kuma sauran almajiran suka ga Yesu a lokuta dabam-dabam. Akwai lokacin da mutane sama da 500 suka gan shi.1 Korintiyawa 15:6.

Da gaba gaɗi, almajiran Yesu sun sanar da mutane har da waɗanda suka kashe shi cewa Yesu ya tashi daga mutuwa. (Ayyukan Manzanni 4:1-3, 10, 19, 20; 5:27-32) Shin waɗannan almajiran za su kasance da gaba gaɗi da a ce ba su da tabbaci cewa Yesu ya tashi daga mutuwa? Babu shakka, tabbacin da Kiristoci suke da shi cewa Yesu ya tashi daga mutuwa ne ya sa ba su yi sanyin gwiwa ba a zamanin dā da kuma a yau.

Akwai tabbacin da suka nuna cewa labarin mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga mutuwa da ke cikin Linjila ya faru da gaske. Idan ka karanta wannan labarin da kyau, za ka kasance da tabbaci cewa waɗannan abubuwan sun faru da gaske. Za ka ƙara samun tabbaci idan ka fahimci dalilan da suka sa waɗannan abubuwan suka faru. Talifi na gaba zai yi wannan bayanin.

^ sakin layi na 7 Tacitus da aka haifa a wajen shekara ta 55 ya ce “Kristi wanda daga sunansa aka samu Kiristoci, ya sha azaba sosai a hannun Bilatus Babunti a ƙarƙashin sarautar Tiberius.” Suetonius (a ƙarni na farko) ma ya ambata sunan Yesu; da wani marubuci Bayahude mai suna Josephus (a ƙarni na farko); da kuma Pliny Ƙarami, wanda shi ne gwamnar ƙasar Bitiniya (a farkon ƙarni na biyu).