Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro  |  Na 2 2016

 

Yadda Rashin Gaskiya Zai Iya Shafan Ka

Yadda Rashin Gaskiya Zai Iya Shafan Ka

“A yawancin lokuta, ana iya magance manya-manyan matsaloli ta wajen yin rashin gaskiya.”—In ji Samantha a Afirka ta Kudu.

Ka yarda da wannan furucin? Kamar Samantha, dukanmu mun taɓa fuskantar manya-manyan matsaloli. Matakin da muka ɗauka sa’ad da aka matsa mana mu yi rashin gaskiya zai nuna ko mu masu gaskiya ne ko a’a. Alal misali, idan a kullum muna ƙoƙari mu kāre kanmu, babu shakka, za mu iya yin ƙarya don mu cim ma hakan. Kuma za mu sami mummunan sakamako idan aka gano cewa ƙarya muka yi. Ka yi la’akari da abubuwan da ke gaba.

RASHIN GASKIYA YAKAN ƁATA DANGANTAKA

Mutane sukan zama abokai bayan sun yarda da junansu. Idan mutane biyu suka yarda da juna, dangantakarsu za ta yi danƙo. Amma hakan ba ya faruwa farat ɗaya. Mutane suna amincewa da juna ne idan suna yawan kasancewa tare kuma suna tattaunawa a sake babu son kai. Amma, yin rashin gaskiya sau ɗaya tak zai iya ragargaje wannan dangantakar. Kuma da zarar an daina yarda da juna, zai iya zama da wuya a sake yarda da juna.

Shin wani abokinka ya taɓa cin amanarka? Yaya ka ji sa’ad da hakan ya faru? Babu shakka, ranka ya ɓace sosai. Ba laifi ba ne idan ka yi fushi domin rashin gaskiya yana ɓata abokantaka.

RASHIN GASKIYA YANA SA WASU MA SU YI RASHIN GASKIYA

Wani bincike da farfesan ilimin tattalin arziki mai suna Robert Innes da ke Jami’ar Kalifoniya ya yi, ya nuna cewa “mutane sukan yi rashin gaskiya domin wasu sun yi musu rashin gaskiya.” Hakazalika, rashin gaskiya yana kamar ƙwayoyin cuta masu yaɗuwa. Idan ka ci gaba da abota da marar gaskiya, babu shakka, kai ma za ka bi halinsa.

Ta yaya za ka guji yin rashin gaskiya? Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka. Don Allah ka bincika wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da ke gaba.