An kasa warware naɗaɗɗen littafin da wuta ta ƙona da aka samo a Ein Gedi tun shekara ta 1970 ba. Amma fasahar 3-D ta taimaka a gano cewa littafin yana ɗauke da wasu sassa na littafin Levitikus kuma akwai sunan Allah a ciki

A SHEKARA TA 1970, masu tone-tonen ƙasa sun haƙo wani naɗaɗɗen littafi da wuta ta ƙona a Ein Gedi da ke ƙasar Isra’ila. Wannan wurin yana kusa da yammacin gaɓar Tekun Gishiri. An samo wannan littafin sa’ad da ake tone-tone a wata majami’a da wuta ta ƙone a lokacin da aka halaka ƙauyen, wataƙila a ƙarni na shida bayan haihuwar Yesu. Da yake wuta ta ƙone littafin, ba a iya warware shi ba, ballantana ma a karanta rubutun da ke cikinsa. Amma fasahar 3-D da kuma wani manhajar ɗaukar hoto sun sa ya yiwu a warware littafin kuma a ga rubutun da ke cikinsa.

Me aka gano a cikin littafin? Rubutu ne na Littafi Mai Tsarki. Sashen da aka warware yana ɗauke da ayoyin da ke surorin farko na littafin Levitikus. Waɗannan ayoyin suna ɗauke da sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu na Ibrananci. An ce an rubuta littafin tsakanin wajen ƙarshen ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu da kuma ƙarni na huɗu. Hakan ya sa littafin ya zama littafin Nassosin Ibrananci mafi daɗewa da aka samo tun lokacin da aka samo littattafan Qumran. Wani mai suna Gil Zohar ya rubuta a jaridar The Jerusalem Post cewa: “Kafin a warware wannan littafin Levitikus da aka samo a Ein Gedi, an samu ƙarni ɗaya tsakanin littattafan Tekun Gishiri da aka rubuta shekara 2,000 da suka shige a lokacin da aka gina Haikalin Urushalima a ƙaro na biyu da kuma littattafan Aleppo Codex da aka rubuta a ƙarni na 10 bayan haihuwar Yesu.” Ƙwararru sun ce wannan littafin da aka warware ya nuna cewa an adana littafin Masoretic na Attaurat sosai kuma mutanen da suka kofe littafin ba su yi kurakurai ba.