An haife ni a ranar 9 ga watan Nuwamba, 1929, a birnin Sukkur da ke yammacin Kogin Indus wanda yanzu shi ne ƙasar Pakistan. A wannan lokacin ne iyayena suka karɓi waɗansu littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki daga wurin wani Bature da ya zo wa’azi a ƙasarsu. Waɗannan littattafan sun taimaka wajen koya mini game da Jehobah.

ANA kiran waɗannan littattafan rainbow set. Sa’ad da na bincika littattafan, na ga hotunan da suka sa na so yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Don haka, tun ina ƙarami, na soma son bincika koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da waɗannan littattafan suka bayyana.

Rayuwata ta soma taɓarɓarewa a lokacin da Yaƙin Duniya na Biyu ya kusan mamaye ƙasar Indiya. Iyayena sun rabu da juna, bayan haka suka kashe aure. Ban san dalilin da ya sa mutanen da nake ƙauna suka kashe aurensu ba. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai kuma na kaɗaita. Ni kaɗai ne iyayena suka haifa, duk da haka, ban sami ƙarfafa da kuma tallafawa da nake bukata ba.

Ni da mahaifiyata muna zama a Karachi, babban birnin ƙasar. Wata rana, wani tsoho likita mai suna Fred Hardaker ya ƙwanƙwasa ƙofarmu. Da shi da Baturen da ya ba iyalinmu waɗannan littattafan suna bin addini ɗaya. Ya gaya wa mahaifiyata ko tana so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, amma ba ta yarda ba. Sai ta gaya masa wataƙila zan so a yi nazari da  ni. Ɗan’uwa Hardaker ya soma nazari da ni a mako na gaba.

Bayan wasu makonni, na soma halartan taro a asibitin Ɗan’uwa Hardaker. Shaidu tsofaffi wajen 12 ne suke halartan taro a wurin. ’Yan’uwan sun ƙarfafa ni sosai kuma sun kula da ni kamar ɗansu. Na tuna yadda suke zama a kujera da ni kuma su tattauna da ni kamar abokinsu. Abin da nake bukata a wannan lokacin ke nan.

Ba da daɗewa ba, Ɗan’uwa Hardaker ya ce mu fita wa’azi tare. Ya koya mini yadda zan yi amfani da garmaho don mu riƙa saka wa mutane jawabai na Littafi Mai Tsarki. Wasu jawaban sun sa wasu mutane fushi don ba su so saƙon ba. Duk da haka, na yi farin cikin yi wa mutane wa’azi. Na kasance da gaba gaɗi sosai kuma ina son yi wa mutane wa’azi.

Sa’ad da sojojin ƙasar Jafan suke shirin kai wa Indiya hari, hukumomin Birtaniya ta soma taƙura wa Shaidun Jehobah sosai. A watan Yuli na 1943, wannan taƙura ta shafe ni. Shugaban makarantarmu wanda limamin cocin Anglican ne ya kore ni daga makaranta. Ya gaya wa mahaifiyata cewa cuɗanyar da nake yi da Shaidun Jehobah yana sa in ɓata sauran ɗaliban. Hakan ya sa ta baƙin ciki sosai kuma ta hana ni yin cuɗanya da Shaidu. Daga baya, ta tura ni wurin mahaifina a garin Peshawar da ke arewacin ƙasar kuma wajen tafiyar mil 850 ne. Zuwa wannan wurin ya sa dangantakata da Jehobah ta yi tsami domin na daina halartar taro da kuma karanta Littafi Mai Tsarki.

NA SAKE ƘARFAFA DANGANTAKATA DA JEHOBAH

A shekara ta 1947, na dawo birnin Karachi don neman aiki. Da nake birnin, na ziyarci asibitin Ɗan’uwa Hardaker kuma ya marabce ni sosai.

Ɗan’uwa Hardaker ya tambaye ni, “Me ke damun ka?” Ya yi wannan tambayar ne don yana tunanin cewa ina rashin lafiya.

Sai na ce, “Lafiyata kalau” amma ina bukatar nazarin Littafi Mai Tsarki.

Ya tambaye ni, “Yaushe kake so mu soma?”

Na ce, “Yanzu, in zai yiwu!”

Mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare a wannan ranar. Na sami ƙarfafa sosai domin na sake soma cuɗanya da Shaidun Jehobah. Mahaifiyata ta so ta hana ni, amma na yanke shawarar bauta wa Jehobah. Na yi baftisma a ranar 31 ga Agusta, 1947. Jim kaɗan bayan haka, sa’ad da nake ɗan shekara 17, na soma yin hidimar majagaba na kullum.

NA JI DAƊIN HIDIMAR MAJAGABA

Wurin da na soma hidimar majagaba shi ne yankin Quetta. A dā, wurin ne barikin sojojin Birtaniya yake, amma a shekara ta 1947, an raba ƙasar zuwa Indiya da Pakistan. * Hakan ya jawo tashin hankali sosai tsakanin Musulmai da ’yan Hindu da Sikh. A sakamakon haka, mutane masu dumbin yawa suka ƙaura. Wajen mutane miliyan 14 sun yi gudun hijira. Musulmai da ke Indiya sun ƙaura zuwa Pakistan, ’yan Hindu da Sikh kuma suka ƙaura zuwa ƙasar Indiya. A lokacin tashin hankalin ne na shiga wani jirgin ƙasa da mutane suka cika maƙil daga Karachi zuwa Quetta kuma na riƙe wani ƙarfe da ke jirgin har zuwa Quetta.

Na halarci taron da’ira a Indiya a shekara ta 1948

A yankin Quetta, na haɗu da wani ɗan’uwa ɗan wajen shekara 25 da ke hidimar majagaba na musamman mai suna George Singh. Ɗan’uwan ya ba ni wani tsohon keke don in riƙa tuƙawa. Akwai tuddai sosai a yankin da muke. A yawanci lokaci, ni kaɗai ne nake yin wa’azi kuma a cikin watannin shida, na soma yin nazari da mutane 17. Yawancin waɗanda na yi nazari da su sun karɓi gaskiya. Ɗaya daga cikinsu wani soja ne mai suna Sadiq Masih. Ya taimaka mana mu fassara wasu littattafai zuwa yaren Urdu da mutanen Pakistan suka fi yi. Da shigewar lokaci, Sadiq ya soma bauta wa Jehobah da ƙwazo sosai.

Sa’ad da za mu Makarantar Gilead a jirgin ruwa mai suna Queen Elizabeth

Daga baya, na koma birnin Karachi kuma na yi hidima da Ɗan’uwa Henry Finch da Harry Forrest waɗanda suka halarci Makarantar Gilead kuma aka tura su wa’azi a ƙasar waje. Sun koya mini abubuwa masu tamani sosai! Da akwai wani lokacin da na bi Ɗan’uwa Finch yin wa’azi a arewacin ƙasar Pakistan. Mun haɗu da mutane da yawa da ke zama kusa da duwatsu. Mutanen suna yaren Urdu kuma sun saurari wa’azi. Bayan shekara biyu, ni ma na halarci Makarantar Gilead, kuma da na dawo, nakan yi hidimar  mai kula da da’ira a wasu lokuta. A masaukin ’yan’uwan da ke hidima a ƙasar waje a birnin Lahore ne nake zama tare da ’yan’uwa guda uku da suka zo wa’azi.

NA SAKE SOMA FARIN CIKI A HIDIMATA

Amma abin taƙaici, a shekara ta 1954, ’yan’uwan da ke wa’azi a ƙasar waje a birnin Lahore sun sami saɓani da juna. Da yake na goyi bayan wasu cikinsu, hakan ya sa aka yi mini gargaɗi. Abin ya sa ni baƙin ciki sosai. Daga baya, sai na koma birnin Karachi. Bayan haka, na ƙaura zuwa Landan don in ci gaba da bauta wa Jehobah a wani wuri dabam.

A ikilisiyar da nake a Landan, da akwai masu hidima a Bethel da yawa. Ɗan’uwa Pryce Hughes da ke kula da ofishin Landan, ya koya mini abubuwa da yawa. Wata rana, Ɗan’uwan ya gaya mini gargaɗin da Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford wanda yake kula da aikin wa’azi a faɗin duniya a lokacin ya yi masa. Sa’ad da Ɗan’uwa Hughes yake so ya wanke kansa, Ɗan’uwa Rutherford bai ba shi damar yin hakan ba. Na yi mamaki da na ga yana murmushi sa’ad da yake ba ni labarin. Ɗan’uwa Hughes ya gaya mini cewa da farko abin ya sa shi baƙin ciki. Amma daga baya ya lura cewa yana bukatar wannan gargaɗin kuma Jehobah yana horar da shi ne domin yana ƙaunar sa. (Ibran. 12:6) Abin da ya faɗa ya ratsa zuciyata sosai kuma ya taimaka mini na sake farin ciki a hidimata ga Jehobah.

A wannan lokacin ne mahaifiyata ta ƙauro zuwa Landan kuma ta yarda Ɗan’uwa John E. Barr wanda daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya yi nazari da ita. Ta sami ci gaba sosai kuma a shekara ta 1957, ta yi baftisma. Daga baya an gaya mini cewa kafin mahaifina ya rasu ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah.

A shekara ta 1958, na auri wata ’yar Denmark mai suna Lene da take zama a Landan. Bayan shekara ɗaya, sai muka haifi ’yarmu ta fari mai suna Jane. Bayan haka, muka ƙara haifan yara huɗu. Kuma na sami wasu gata a ikilisiyar Fulham. Amma da shigewar lokaci sai matata ta soma rashin lafiyar da ya bukaci mu koma wurin da babu sanyi sosai. Don haka, a shekara ta 1967, muka ƙaura zuwa birnin Adelaide da ke Ostareliya.

ABIN BAƘIN CIKI YA FARU

A ikilisiyarmu da ke Adelaide, da akwai ’yan’uwa guda 12 da shafaffu ne. ’Yan’uwan sun saka ƙwazo sosai a yin wa’azi. Ba da daɗewa ba, muka soma yin abubuwan da za su taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah.

A shekara ta 1979, mun sami ƙaruwar ɗa mai suna Daniel. Amma yaron yana da ciwon da ake kira Down  syndrome. * Don haka, ba mu yi tsammanin cewa zai jima da rai ba. Har yanzu ba zan iya bayyana irin baƙin cikin da muka yi ba. Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu kula da shi, amma hakan bai hana mu kula da sauran yaranmu ba. A wasu lokuta, launin fatar Daniel yakan canja zuwa ruwan shuɗi domin ramuka biyu da ke zuciyarsa na hana shi numfashi. Kuma haka na sa mu kai shi asibiti da gaggawa. Amma duk da cewa ba shi da lafiya, yana da ilimi sosai kuma yana da fara’a. Ban da haka ma, yana ƙaunar Jehobah sosai. Idan za mu ci abinci kuma muna addu’a, sai ya naɗa hannuwansa kuma ya ce “Amin” ta wajen nuna alama da kansa kafin ya soma cin abinci.

A lokacin da Daniel yake ɗan shekara huɗu, ya kamu da kansar jini. Hakan ya sa ni da matata damuwa sosai har na ji kamar zan haukace. Wata rana da muka yi sanyin gwiwa sosai, mai kula da da’irarmu Ɗan’uwa Neville Bromwich ya kawo mana ziyara. A wannan daren, Ɗan’uwan ya rungume mu yana zub da hawaye, sai dukanmu muka soma kuka. Yadda ya nuna ya damu da mu da kuma kalamansa sun ƙarfafa mu sosai. Bayan hakan, sai ya tafi da ƙarfe ɗaya na tsakar dare. Ba da daɗewa ba, Daniel ya rasu. Wannan ne abin da ya fi sa mu baƙin ciki a rayuwa. Amma mun jimre kuma muka kasance da gaba gaɗi cewa babu abin da zai hana Jehobah ƙaunar Daniel, har ma mutuwa. (Rom. 8:​38, 39) Muna ɗokin sake kasancewa tare da shi a lokacin da zai tashi daga matattu a sabuwar duniya!​—Yoh. 5:​28, 29.

TAIMAKA WA MUTANE NA SA NI FARIN CIKI

Har yanzu ni dattijo ne a ikilisiyarmu, duk da cewa na yi ciwon bugun jini har sau biyu. Abubuwan da na fuskanta a rayuwa sun sa ina tausaya wa mutane sosai musamman ma waɗannan suke fuskantar matsaloli. Ina iya ƙoƙarina don kada in riƙa shari’anta mutane. Maimakon haka, nakan tambayi kaina: ‘Ta yaya abubuwan da suka fuskanta a rayuwa ya shafi yadda suke tunani? Ta yaya zan nuna musu cewa na damu da su? Ta yaya zan ƙarfafa su su ci gaba da bauta wa Jehobah?’ Hakika, ina jin daɗin zuwa ziyarar ƙarfafawa sosai! A duk lokacin da na ƙarfafa wasu don su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, hakan yana ƙarfafa ni.

Har yanzu ina samun gamsuwa a duk lokacin da na kai ziyarar ƙarfafawa

Ra’ayina kamar na marubucin wannan Zabura ne da ya ce: “Sa’ad da damuwoyi sukan yi mini yawa, ta’aziyyarka [Jehobah] takan ƙarfafa raina.” (Zab. 94:19) Jehobah ya taimaka mini sa’ad da nake fuskantar matsalolin a iyalina da hamayya don imanina da kurakuren da na yi da kuma lokacin da nake cikin damuwa. Babu shakka, Jehobah Uba ne a gare ni!

^ sakin layi na 19 A dā, gabashin Pakistan wanda yanzu ake kira Bangladesh da yammancin Pakistan ne ƙasar Pakistan.

^ sakin layi na 29 Ka duba talifin nan “Raising a Child With Down Syndrome​—The Challenge and the Reward” da ke Awake! na Yuni, 2011.