Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Yuni 2017

Ka Sani?

Ka Sani?

Ya dace ne da aka kira ’yan kasuwa da suke sayar da dabbobi a haikalin Urushalima “mafasa”?

KAMAR yadda Linjilar Matta ta bayyana, “Yesu ya shiga cikin haikali na Allah, ya fitar da dukan masu-sayarwa da masu-saye cikin haikali, ya jirkitar da tebura na masu-musanyar kuɗi, da kujerun masu-sayar da kurciyoyi; kuma ya ce musu, An rubuta, Za a ce da gidana gidan addu’a: amma kun maishe shi kogon mafasa.”​—Mat. 21:​12, 13.

Littafin tarihin Yahudawa ya bayyana cewa ’yan kasuwa da ke cikin haikali suna yi wa abokan cinikinsu zamba. Suna sayar musu abubuwa da tsada. Alal misali, kurciyoyi suna da araha sosai kuma talakawa suna iya sayan su don su yi hadayu da su. Amma tarihin Yahudawa ya nuna cewa akwai lokacin da sai mutum ya yi aikin kwanaki 25 kafin ya sami kuɗin sayan kurciyoyi biyu. Wannan dalilin ne ya sa talakawa suka kasa sayansu don sun yi tsada sosai. (Lev. 1:14; 5:7; 12:​6-8) Halin ƙuncin da talakawa suka shiga ya sa wani malami mai suna Simeon ben Gamaliel fushi sosai, kuma ya sa aka rage yawan hadayun da ake yi. Nan da nan, farashin kurciya ya faɗi warwas, har ya zama cewa kuɗin aikin awa uku kawai ya isa sayan kurciyoyi biyu.

Abubuwan da aka ambata ɗazu sun nuna cewa ya dace da Yesu ya kira mutanen da suke kasuwanci a haikali “mafasa” saboda haɗamarsu da kuma yadda suke cutar mutane.