Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Wane ra’ayi ne ‘yan’uwa masu kula da da’ira da kuma dattawa suke bukatar su kasance da shi sa’ad da ƙungiyar Jehobah ta ba da wani umurni?

Ya kamata su yi biyayya ba tare da ɓata lokaci ba. Saboda haka, suna iya tambayar kansu: ‘Shin ina ƙarfafa ‘yan’uwana su kasance da aminci ga Jehobah? Ina saurin bin shawarar da ƙungiyar Jehobah take bayarwa?’​—w16.11, shafi na 11.

A wane lokaci ne bayin Allah suka yi zaman bauta a Babila?

Hakan ya faru ne jim kaɗan bayan da manzannin suka mutu. A lokacin ne limaman addinai suka taso kuma suka soma koyarwarsu. Bayan hakan, sai Coci da gwamnatin Roma suka haɗa kai kuma suka yi ƙoƙarin su yaɗa koyarwar ƙarya kuma su hana mutane saurarar Kiristoci masu aminci. Amma shafaffun Kiristoci sun soma ƙin su shekaru da yawa kafin 1914.​—w16.11, shafaffuka na 23-25.

Me ya sa aikin da Lefèvre d’Étaples ya yi yake da muhimmanci sosai?

A shekara ta 1520 da wani abu ne, Lefèvre ya fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Faransanci don mutane da yawa su karanta. Kuma fassarar da ya yi ta shafi Martin Luther da William Tyndale da kuma John Calvin.​—wp16.6, shafuffuka na 10-12.

Mene ne bambanci da ke tsakanin waɗanda suka ƙwallafa ransu ga ‘al’amuran jiki’ da kuma waɗanda suka ƙwallafa ransu ga ‘al’amuran ruhu’? (Rom. 8:6)

Wanda yake ƙwallafa ransa ga al’amuran jiki a kullum yana mai da hankali ne ga sha’awoyi da kuma abubuwan jiki. Kuma hirarsa da kome da yake yi bai shafi abubuwan ibada ba. Amma wanda yake ƙwallafa ransa ga al’amuran ruhu yana mai da hankali ga abubuwan da suka shafi ibada da kuma ra’ayin Allah. Kuma wannan mutum ruhu mai tsarki ne yake masa ja-goranci. Wanda yake ƙwallafa ransa ga al’amuran jiki zai hallaka. Amma wanda ya ƙwallafa ransa ga al’amuran ruhu zai sami rai da kuma salama.​—w16.12, shafaffuka na 15-17.

Wane mataki ne za ka ɗauka don ka rage alhini?

Ka sa abubuwan da suka fi muhimmanci a kan gaba. Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Ka keɓe lokacin hutawa a kowace rana. Ka more abubuwan da Jehobah ya halitta. Ka zama mai fara’a. Ka riƙa motsa jiki kuma ka riƙa samun isashen barci.​—w16.12, shafuffuka na 22-23.

Ta yaya aka “ɗauki Anuhu domin kada ya ga mutuwa”? (Ibran. 11:⁠5)

Wataƙila Jehobah ya sa Anuhu ya mutu ba tare da sanin Anuhu ba.​—⁠wp17.1, shafuffuka na 12-13.

Me ya sa tawali’u yake da muhimmanci?

Mutum mai tawali’u ya san abubuwan da zai iya yi da abubuwan da ya cim ma da kuma kura-kuransa. Saboda haka, muna bukatar mu riƙa tuna yadda halinmu zai iya shafan wasu kuma mu daina ganin kanmu wani abu.​—w17.01, shafi na 18.

Wane tabbaci muke da shi cewa Allah ne ya ja-goranci Hukumar Kiristoci a ƙarni na farko kamar yadda yake yi wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a yau?

Ruhu mai tsarki ya taimaka musu su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ban da haka ma, mala’iku sun ja-gorance su sa’ad da suke wa’azi kuma sun dogara ga Kalmar Allah. Hukumar Shaidun Jehobah ma suna yin hakan.​—w17.02, shafuffuka na 26-28.

Sanin waɗanne abubuwa ne za su taimaka mana mu ɗauki fansar da muhimmanci?

Abubuwa guda huɗu su ne: Wanda ya ba ka kyautar da dalilin da ya sa aka ba ka kyautar da sadaukarwar da mutumin ya yi da kuma dalilin da ya sa kake bukatar kyautar.​—wp17.2, shafuffuka na 4-6.

Zai dace mutum ya canja ra’ayinsa ne bayan ya tsai da shawarar yin wani abu?

Ya kamata mu riƙa yin abin da muka tsai da shawarar yi. Amma a wani lokaci, zai dace mutum ya canja wata shawarar da ya yanke. Allah ya canja shawarar da ya yanke bayan da mutanen Nineba suka tuba daga zunubansu. A wasu lokuta, canjin yanayi ko kuma wani bayani zai iya sa mutum ya canja wata shawarar da yanke.​—w17.03, shafuffuka na 16-17.

Me ya sa gulma take da hadari?

Gulma tana jawo matsala sosai a ikilisiya. Gulma ko bakar magana ba zai magance matsala ba ko da mu muka yi kuskuren ko kuma wani ya yi mana kuskuren.​—w17.04, shafi na 21.