“Ga shi, kamar yumɓu a hannun mai-tukwane, hakanan kuke a hannuna.”—IRM. 18:6.

WAƘOƘI: 60, 22

1, 2. Me ya sa Allah ya ɗauki Daniyel a matsayin “mutum ƙaunatacce ƙwarai,” kuma ta yaya za mu zama masu yin biyayya kamar Daniyel?

SA’AD DA Isra’ilawa suka je zaman bauta a birnin Babila na dā, sun ga cewa mutanen suna bauta wa gumaka da kuma aljanu. Amma da akwai wasu Yahudawa masu aminci kamar Daniyel da kuma abokansa guda uku da suka ƙi bin salon rayuwar mutanen Babila. (Dan. 1:6, 8, 12; 3:16-18) Daniyel da abokansa sun ƙudura niyyar cewa za su bauta wa Jehobah shi kaɗai a matsayin mai mulmula su, kuma sun yi nasarar yin hakan! Daniyel ya yi kusan dukan rayuwarsa a Babila amma duk da haka, mala’ikan Allah ya ce shi mutum ne “ƙaunatacce ƙwarai.”—Dan. 10:11, 19.

2 A zamanin dā, maginin tukwane yana mulmula yumɓu kuma ya mai da shi abin da yake so. Kiristoci na gaskiya a yau, suna ɗaukan Jehobah a matsayin Mamallakin Dukan Halitta, wanda yake da ikon mulmula mutane da kuma al’ummai. (Karanta Irmiya 18:6.) Ƙari ga haka, Allah yana da ikon mulmula kowannen mu. Amma ya san muna da ’yancin yin abin da muke so kuma yana so mu bauta masa da son ranmu. Bari mu mai da hankali ga yadda za mu zama kamar yumɓu mai laushi a hannayen Allah ta wajen yin la’akari da waɗannan wurare uku: (1) Ta yaya za mu guji  halayen da za su sa mu ƙi jin shawarwarin da Allah yake ba mu? (2) Ta yaya za mu kasance da halayen da za su taimaka mana mu ci gaba da zama kamar yumɓu mai laushi kuma mu zama masu bin ja-gora? (3) Ta yaya iyaye za su bi ja-gorar Allah sa’ad da suke mulmula yaransu?

KA GUJI HALAYEN DA ZA SU SA KA ƘI JIN SHAWARA

3. Waɗanne irin halaye ne za su sa mu ƙi jin shawara? Ka ba da misali.

3 Littafin Misalai 4:23 ta ce: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da kake kiyayewa: gama daga cikinta mafitan rai suke.” Waɗanne halaye ne za mu guje wa? Sun ƙunshi fahariya da kasancewa da halin yin zunubi da kuma rashin bangaskiya. Waɗannan halayen za su iya sa mu yi tawaye ko kuma rashin biyayya. (Dan. 5:1, 20; Ibran. 3:13, 18, 19) Abin da ya faru da sarki Uzziah ke nan. (Karanta 2 Labarbaru 26:3-5, 16-21.) Da farko, Uzziah “ya yi abin da ke daidai a gaban Ubangiji,” kuma “ya sa kansa ya biɗi Allah.” Amma “sa’anda ya yi ƙarfi, zuciyarsa ta habaka” duk da cewa Allah ne ya ba shi ƙarfi! Ya kasance da fahariya har ya so ya ƙona turare a cikin haikali, aikin da firistoci ne kawai suke da gatan yi. Amma Uzziah ya hasala sa’ad da firistoci suka gaya masa cewa bai kamata ya yi wannan aikin ba! Mene ne sakamakon? Allah ya hukunta shi kuma ya zama kuturu har mutuwarsa.—Mis. 16:18.

4, 5. Mene ne zai faru idan muka ƙi guje wa fahariya? Ka ba da misali.

4 Idan muna da fahariya, muna ma za mu iya soma ‘aza kanmu gaba da inda ya kamata,’ har ya sa mu ƙi bin shawara. (Rom. 12:3; Mis. 29:1) Ka yi la’akari da misalin wani dattijo mai suna Jim wanda ya ƙi amincewa da wata shawara da dattawan ikilisiya suka tsai da a kan wani batu. Jim ya ce: “Na gaya wa dattawan cewa ba sa ƙauna ’yan’uwansu kuma na bar taron.” Bayan wata shida, ya bar ikilisiyar kuma ya koma wata ikilisiya amma ba a naɗa shi dattijo a wurin ba. Ya ce: “Hakan ya sa na karaya. Na kasance da tabbaci cewa abin da nake yi shi ne daidai, saboda haka na daina bauta wa Jehobah.” Jim ya yi shekara goma ba ya halartan taro da kuma fita wa’azi. Ya ƙara cewa: “Na kasance da fahariya kuma na soma ganin laifin Jehobah don abubuwan da suke faruwa. Shekaru da yawa, ’yan’uwa suna zuwa wurina don su taimaka mini amma na yi watsi da su.”

5 Abin da ya faru da Jim ya nuna yadda fahariya za ta sa mu soma ganin cewa abin da muke yi ne daidai kuma hakan zai sa ba za mu zama kamar yumɓu mai laushi da za a iya mulmulawa ba. (Irm. 17:9) Jim ya ce: “Na ci gaba da ganin cewa ’yan’uwan ne suke da laifi.” Shin wani ɗan’uwa ya taɓa ɓata maka rai? Ka taɓa fushi don ka rasa gatan da kake da shi a cikin ikilisiya? Idan haka ne, yaya ka bi da batun? Shin ka yi fahariya ne? Ko kuma ka nemi ka sulhunta da ɗan’uwanka kuma ka ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah?—Karanta Zabura 119:165; Kolosiyawa 3:13.

6. Mene ne zai iya faruwa idan muka ci gaba da yin zunubi?

6 Idan muka ci gaba da yin zunubi, wataƙila a ɓoye, hakan zai sa mu ƙi jin shawara. Ƙari ga haka, yin zunubi ba zai riƙa damun mu kuma ba. Wani ɗan’uwa ya ce da shigewar lokaci, abubuwa marasa kyau da yake yi ba sa damunsa kuma. (M. Wa. 8:11) Wani ɗan’uwa, da ya soma kallon hotunan batsa ya ce: “Hakan ya sa na soma kushe dattawa.” Halinsa ya ɓata dangantakarsa da Jehobah. Daga baya, an gano abin da yake yi kuma dattawa suka taimaka masa. Hakika, dukan mu ajizai ne. Amma idan muka soma kushe mutane ko kuma muka soma ba da hujjoji don abubuwa marasa kyau da muke yi maimakon mu roƙi Jehobah ya yafe  mana zunubanmu kuma ya taimaka mana, hakan zai sa zuciyarmu ta taurara kuma mu ƙi bin shawarwari.

7, 8. (a) Ta yaya Isra’ilawa na dā suka nuna rashin bangaskiya? (b) Wane darasi ne muka koya daga wannan?

7 Isra’ilawa sun nuna rashin bangaskiya bayan Jehobah ya cece su daga ƙasar Masar. Wannan misali ya nuna mana yadda rashin bangaskiya zai iya taurara zuciyarmu. Al’ummar Isra’ila ta ga yadda Allah ya yi abubuwan ban al’ajabi don ya cece ta! Duk da haka, sun nuna rashin bangaskiya sa’ad da suka kusan shiga Ƙasar Alkawari. Maimakon su dogara ga Jehobah, sun tsorata kuma suka soma gunaguni game da Musa. Ƙari ga haka, sun so su koma ƙasar Masar inda suka yi zaman bayi! Jehobah ya yi fushi kuma ya ce: “Har yaushe mutanen nan za su rena ni.” (Lit. Lis. 14:1-4, 11; Zab. 78:40, 41) Saboda taurin kansu da kuma rashin bangaskiyarsu, waɗannan mutanen sun mutu a jeji.

8 Da yake mun kusa mu shiga sabuwar duniya, za mu fuskanci gwaji na bangaskiyarmu. Saboda haka, muna bukata mu bincika bangaskiyarmu. Alal misali, za mu iya yin nazari game da abin da Yesu ya ce a littafin Matta 6:33. Ka tambaye kanka: ‘Shin maƙasudaina da kuma shawarwarina suna nuna cewa na gaskata da abin da Yesu ya ce? Zan ƙi zuwa taro ko kuma wa’azi don neman kuɗi? Me zan yi idan ana bukatar in ƙara ba da lokaci a wurin aiki? Shin zan bar tasiri na wannan duniyar ya mulmula ni har ya sa na daina bauta wa Jehobah?’

9. Me ya sa muke bukata mu ci gaba da “gwada” bangaskiyarmu, kuma ta yaya za mu yi hakan?

9 Alal misali, ka yi la’akari da wani bawan Jehobah, wanda ba ya bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, wataƙila game da tarayyar banza ko yankan zumunci ko kuma nishaɗi. Ka tambayi kanka, ‘Shin haka nake?’ Idan muka ga cewa muna da irin wannan halin, muna bukata mu bincika bangaskiyarmu nan da nan! Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawara cewa: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.” (2 Kor. 13:5) Idan ka ga cewa kana bukata ka yi gyara, ka riƙa yin amfani da Kalmar Allah don ka daidaita ra’ayinka.

KA CI GABA DA ZAMA YUMƁU MAI LAUSHI

10. Mene ne zai taimaka mana mu zama kamar yumɓu mai laushi a hannun Jehobah?

10 Allah ya yi mana tanadin Kalmarsa da taron ikilisiya da kuma wa’azin bishara don mu ci gaba da zama kamar yumɓu mai laushi. Kamar yadda ruwa yake sa yumɓu ya yi laushi, haka ma karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma yin bimbini a kansa yake taimaka mana mu zama kamar yumɓu mai laushi a hannu Jehobah. Jehobah ya bukaci sarakunan Isra’ila su rubuta wa kansu Dokokin Allah kuma su karanta shi kullum. (K. Sha. 17:18, 19) Manzannin sun gano cewa idan suna so su yi nasara a hidimarsu, suna bukata su karanta Nassosi kuma su yi bimbini a kansu. A rubuce-rubucensu, sun yi ƙaulin Nassosin Ibrananci sosai kuma sun ƙarfafa mutanen da suka yi wa wa’azi su yi hakan. (A. M. 17:11) A yau, mu ma mun ga muhimmancin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kai kullum. (1 Tim. 4:15) Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da tawali’u a gaban Jehobah kuma mu zama kamar yumɓu da zai iya mulmulawa.

Ka yi amfani da abubuwan da Allah ya tanadar don su taimaka maka ka zama kamar yumɓu da zai a iya mulmulawa (Ka duba sakin layi na 10-13)

11, 12. Ta yaya Jehobah yake amfani da ikilisiyar Kirista don ya mulmula mu bisa ga bukatan mu? Ka ba da misali.

11 Ta wurin ikilisiyar Kirista, Jehobah yana mulmula mu bisa ga abin da kowannen mu yake bukata. Jim, wanda aka ambata ɗazu ya soma canja halayensa sa’ad da wani dattijo ya kusace shi kuma suka zama abokai.  Jim ya ce: “Bai taɓa nuna min cewa ina da laifi kuma bai kūshe ni ba. Maimakon haka, ya ƙarfafa ni kuma ya nuna min cewa yana so ya taimake ni da gaske.” Bayan wata uku, dattijon ya gayyaci Jim zuwa taron Kirista. Jim ya ce: “’Yan’uwa sun marabce ni sosai kuma ƙaunar da suka nuna min ya sa na canja halina. Na soma ganin cewa ra’ayina ba shi ne ya fi muhimmanci ba. Da taimakon ’yan’uwan da kuma matata, na soma bauta wa Jehobah. Na amfana sosai daga karatun talifofin da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga watan Nuwamba 1992 mai jigo ‘Jehovah Is Not to Blame’ da kuma ‘Serve Jehovah Loyally.’”

12 Da shigewar lokaci, Jim ya sake zama dattijo. Tun daga lokacin, ya taimaka wa wasu ’yan’uwa su shawo kan irin waɗannan halayen kuma su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. A ƙarshe Jim ya ce: “Na ɗauka cewa ina da dangantaka mai kyau da Jehobah amma da gaske, ban da shi! Na yi da-na-sanin barin fahariya ya sa na mai da hankali ga laifofin mutane maimakon in mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci.”—1 Kor. 10:12.

13. Waɗanne halaye ne wa’azin bishara yake taimaka mana mu kasance da su, kuma ta yaya muke amfana daga hakan?

13 Ta yaya za mu amfana sa’ad da muke yin wa’azin bishara? Yi wa mutane wa’azin bishara zai taimaka mana mu kasance da tawali’u da kuma fannoni dabam-dabam na ’ya’yan ruhu mai tsarki. (Gal. 5:22, 23) Ka yi tunanin yadda fita wa’azi ya taimaka maka ka kasance da halaye masu kyau. Ban da haka, yayin da muke nuna halaye irin na Kristi, za mu sa mutane su daraja wa’azin da muke yi kuma hakan zai shafi halayensu. Alal misali, wasu Shaidun Jehobah a ƙasar Ostareliya suna yi wa wata mata wa’azi a gidanta, amma ta yi fushi kuma ta soma yi musu baƙar magana. Waɗannan Shaidun sun saurare ta kuma ba su ce komai ba.  Daga baya, wannan matan ta yi da-na-sani kuma ta rubuta wa ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar wasiƙa. Ta ce: “Ina so in roƙi gafara daga waɗannan mutane biyu masu tawali’u da kuma haƙuri. Ni wawuya ce da har zan yi wa mutanen da ke wa’azin Kalmar Allah baƙar magana kuma in kore su.” Shin wannan matan za ta rubuta hakan da a ce ’yan’uwan nan sun nuna cewa sun yi fushi? A’a. Hakika, wa’azin bishara yana amfanar mu da kuma waɗanda muke yi wa wa’azi!

KU BI JA-GORAR ALLAH SA’AD DA KUKE MULMULA YARANKU

14. Mene ne ya kamata iyaye su yi idan suna son su yi nasara wajen mulmula yaransu?

14 Yawancin yara suna da tawali’u kuma suna son koyan abubuwa. (Mat. 18:1-4) Hakazalika, iyaye masu basira suna iya ƙoƙarinsu don su koya wa yaransu gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma suna son yaransu so koyarwar da dukan zukatansu. (2 Tim. 3:14, 15) Babu shakka, don iyaye su yi nasara a yin hakan, suna bukata su ƙaunaci gaskiyar Kalmar Allah da dukan zuciyarsu kuma su bi ƙa’idodin da ke cikinta. Idan iyaye suka yi hakan, zai kasance da sauƙi wa yaransu su ƙaunaci Kalmar Allah. Ƙari ga haka, za su ga cewa Jehobah da kuma iyayensu suna ƙaunarsu, kuma hakan ne ya sa suke yi musu horo.

15, 16. Ta yaya iyaye za su nuna cewa sun dogara ga Jehobah sa’ad da aka yi wa ɗansu ko ’yarsu yankan zumunci?

15 A wani lokaci, duk da ƙoƙarin da iyaye suka yi don su koya wa yaransu Kalmar Allah, wasu yaran suna daina bauta wa Jehobah ko kuma a yi musu yankan zumunci. Hakan yana sa iyalin baƙin ciki. Wata ’yar’uwa a Afirka ta Kudu ta ce, “Sa’ad da aka yi wa ɗan’uwana yankan zumunci, na ji kamar mutuwa ya yi. Hakan ya sa ni baƙin cikin sosai.” Mene ne ita da iyayenta suka yi? Sun bi umurnin da Kalmar Allah ta bayar game da hakan. (Karanta 1 Korintiyawa 5:11, 13.) Iyayen sun ce: “Mun yanke shawara cewa za mu bi umurnin da Littafi Mai Tsarki ya bayar, tun da mun san cewa yin abubuwan da Allah yake so zai kawo sakamako mai kyau. Mun ɗauki yankan zumunci a matsayin horo daga Allah kuma muna da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu shi ya sa yake mana horo. Saboda haka, abubuwan da yake haɗa mu da ɗanmu, shi ne al’amura da suka shafi iyali kawai.”

16 Yaya ɗansu ya ji game da hakan? Ya ce: “Na san cewa iyayena suna ƙaunata. Suna yin biyayya ne ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.” Ya daɗa cewa: “Idan yanayinka ya sa ka nemi taimako da kuma gafara daga wurin Jehobah, hakan zai sa ka san cewa kana bukata ka dogara gare shi.” Ka yi tunanin farin cikin da iyayen suka yi sa’ad da aka dawo da ɗansu! Hakika, za mu yi farin ciki sosai kuma za mu yi nasara idan muna yi wa Allah biyayya a koyaushe.Mis. 3:5, 6; 28:26.

17. Mene ya sa ya kamata mu riƙa yi wa Jehobah biyayya, kuma ta yaya hakan zai amfane mu?

17 Annabi Ishaya ya ambata lokacin da Yahudawa za su daina zama bayin a Babila, kuma waɗanda suka tuba za su ce: “Ya Ubangiji, kai ubanmu ne, mu yumɓu ne, kai ne mai-yin tukwane da mu: mu dukanmu kuma aikin hannunka ne.” Bayan haka sun roƙe shi cewa: ‘Kada ka tuna da muguntarmu har abada kuma: ka duba, ka gani, muna roƙonka, mu duka mutanenka ne.’ (Isha. 64:8, 9) Idan mu ma muka yi biyayya ga Jehobah kuma muka ci gaba da yin hakan, zai ɗauke mu da tamani kamar annabi Daniyel. Ƙari ga haka, Jehobah zai ci gaba da mulmula mu ta wajen yin amfani da Kalmarsa da ruhu mai tsarki da kuma ƙungiyarsa don wata rana mu tsaya a gabansa a matsayin kamiltattun “’ya’yan Allah.”—Rom. 8:21.