Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Yuli 2017

“Ya Sa Dukan Shirye-Shiryenka Su Yi Nasara”

“Ya Sa Dukan Shirye-Shiryenka Su Yi Nasara”

“Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.”​—ZAB. 37:4.

WAƘOƘI: 89, 140

1. Wace shawara ce matashi zai tsai da game da nan gaba, amma me ya sa bai kamata ya damu ainun ba? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

MATASA, za ku yarda cewa in za ku yi tafiya, ya kamata ku yi shiri sosai. Hakazalika, rayuwa tana kama da tafiya kuma yanzu ne ya kamata ku yi shirin wurin da za ku je. Hakika, tsara rayuwarmu ba ta da sauƙi. Wata yarinya mai suna Heather ta ce: “Hakan abin tsoro ne. Wajibi ne ka tsai da shawarar abin da za ka yi a rayuwarka.” Amma kada ku damu don Jehobah ya gaya wa bayinsa: “Kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka: ni taimake ka.”​—Isha. 41:10.

2. Ta yaya kuka san cewa Jehobah yana so ku yi farin ciki a nan gaba?

2 Jehobah yana ƙarfafa ku ku tsara rayuwarku da kyau. (M. Wa. 12:1; Mat. 6:20) Don yana so ku yi farin ciki. Abubuwa masu kyau da ya halitta kamar abinci da dabbobi da dai sauransu sun tabbatar mana da hakan. Jehobah yana kula da mu da kuma koya mana yadda za mu ji daɗin rayuwarmu. Kuma ya gaya ma waɗanda suke ƙin shawararsa cewa: Ku da “kuka zaɓi abin da ban ji daɗinsa ba . . . ga shi, bayina za su yi farin ciki, amma ku za ku ji kunya: ga shi kuma, bayina za su yi rairawa domin murna a zuci.” (Isha. 65:​12-14) Muna sa mutane su ɗaukaka Jehobah idan muka tsai da shawarwari da suka dace a rayuwa.​—Mis. 27:11.

 MAKASUDAN DA ZA SU SA KU FARIN CIKI

3. Mene ne Jehobah yake son ku yi?

3 Wane shiri ne Jehobah yake son ku yi? Ya halicce mutane su riƙa farin ciki don suna bauta masa kuma sun san shi da kyau. (Zab. 128:1; Mat. 5:3) Amma ba hakan dabbobi suke ba, su kawai nasu su ci abinci ne, su sha ruwa kuma su haifi ’ya’ya. Allah yana so ku tsara rayuwarku a hanyar da za ku yi farin ciki kuma ku yi rayuwa mai ma’ana. Mahaliccinku ‘Allah ne na ƙauna’ da Allah mai farin ciki wanda ya halicci mutane “cikin kamaninsa.” (2 Kor. 13:11; Far. 1:27) Za ku yi farin ciki idan kuka yi koyi da Allahnmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (A. M. 20:35) Hakan gaskiya ne. Saboda haka, Jehobah yana so ku tsara rayuwarku a yadda za ku nuna kuna ƙaunar mutane da kuma Allah.​—Karanta Matta 22:​36-39.

4, 5. Mene ne ya sa Yesu farin ciki?

4 Yesu Kristi ya kafa wa matasa misali mai kyau. Babu shakka, sa’ad da yake yaro ya yi wasa. Amma, Kalmar Allah ta ce akwai “lokacin dariya . . . da lokacin rawa.” (M. Wa. 3:4) Yesu ya ƙulla dangantaka da Jehobah ta yin nazarin Nassosi don sa’ad da yake ɗan shekara 12, malamai a haikalin sun yi mamaki sosai game da “fahiminsa da magana da yake mayarwa” a batutuwan da suka shafi ibada ga Jehobah.​—Luk. 2:​42, 46, 47.

5 Yesu ya yi farin ciki sa’ad da ya yi girma. Me ya sa? Ya san cewa Allah yana son ya “yi shelar bishara ga talakawa . . . da mayarwar gani ga makafi.” (Luk. 4:18) Yesu ya yi farin ciki don ya yi abin da Allah ya umurce shi. Ƙari ga haka, littafin Zabura 40:8 ya faɗa yadda Yesu ya ji, ya ce: “Murna nake yi in yi nufinka.” Yesu ya ji daɗin koya wa mutane game da Ubansa. (Karanta Luka 10:21.) Akwai wani lokaci bayan Yesu ya koya ma wata mata game da bauta ta gaske, sai ya gaya wa almajiransa: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yoh. 4:​31-34) Yesu ya yi farin ciki don yana ƙaunar Allah da kuma mutane. Idan ka yi hakan, kai ma za ka yi farin ciki.

6. Me ya sa ya dace ku nemi shawara daga wurin Kiristoci da suke hidima ta cikakken lokaci?

6 Kiristoci da yawa sun soma hidimar majagaba sa’ad da suke matasa, kuma hakan ya sa su farin ciki sosai. Kuna iya neman shawara daga wasunsu. Don “wurin da babu shawara, nufe-nufe sukan warware: amma cikin taron masu-shawara sukan tabbata.” (Mis. 15:22) Wataƙila waɗannan ’yan’uwan za su gaya maka yadda hidimar majagaba za ta sa ka koyi abubuwan da za su taimaka maka a ibadarka. Bayan da Jehobah ya koyar da shi, Yesu ya koyi abubuwa da yawa sa’ad da yake hidima a duniya. Alal misali, ya yi farin ciki sa’ad da ya sa mutane suka fahimci Kalmar Allah suka yi amfani da shi. Ban da haka, ya yi farin ciki don ya kasance da aminci a lokacin da yake fuskantar jarraba. (Karanta Ishaya 50:4; Ibran. 5:8; 12:2) Yanzu za mu bincika wasu fannoni na hidima ta cikakken lokaci da za su sa ku farin ciki sosai.

MASU WA’AZI SUNA YIN NASARA

7. Me ya sa matasa da yawa suke jin daɗin koya wa mutane game da Littafi Mai Tsarki?

7 Yesu ya ce: “Ku tafi . . . ku almajirtar da dukan al’ummai.” (Mat. 28:​19, 20) Idan kun yi shirin yin wannan hidimar, babu shakka kun yi zaɓi mafi kyau da ke ɗaukaka Allah. Kamar yadda yake da wata sana’a, za ku ƙware da shigewar lokaci. Ba da daɗewa ba, wani ɗan’uwa mai suna Timothy wanda ya soma hidimar majagaba tun yana matashi ya ce: “Ina son bauta wa Jehobah ta yin hidima ta cikakken lokaci domin ina son in nuna wa Jehobah cewa ina ƙaunarsa. Da farko, ban iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ba, amma daga baya na  ƙaura zuwa wani yanki, kuma cikin wata ɗaya na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Wani cikin ɗalibai na ya soma halartan taro a Majami’ar Mulki. Bayan na sauke karatu daga makaranta na wata biyu da ake kiran Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure, * sai aka tura ni hidima a wani wurin da na soma nazari da mutane huɗu. Ina son koya wa mutane Littafi Mai Tsarki don ina ganin yadda ruhu mai tsarki yake sa su canja salon rayuwarsu.”​—1 Tas. 2:19.

8. Mene ne wasu matasa suka yi don su yi wa mutane da yawa wa’azi?

8 Wasu matasa sun koyi wani yare. Alal misali, Jacob da ya fito daga Amirka ya ce: “Sa’ad da nake ɗan shekara bakwai, ’yan ajinmu da yawa ’yan Vietnam ne kuma suna yarensu. Da yake ina son in koya musu abubuwa game da Jehobah, sai na tsai da shawarar koyan yarensu. Kuma abin da na yi don in koyi yaren shi ne yin nazarin Hasumiyar Tsaro na yaren da na Turanci don in fahimta sosai. Ban da haka ma, na nemi abokai da suke yaren a ikilisiyar da take yankin. Da na kai shekara 18, sai na soma hidimar majagaba. Bayan haka, sai aka gayyace ni zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki don ‘Yan’uwa Maza Marasa Aure. Da yake ni kaɗai ne dattijo a rukunin da ake yaren mutanen Vietnam, abubuwan da na koya daga makarantar ya taimaka mini a hidimar majagaba da nake yi a wurin. Mutanen Vietnam sun yi mamaki sosai don na iya yarensu. Idan na je wa’azi, suna sauraro na sosai kuma suna yarda in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Wasu cikinsu ma sun yi baftisma.”​—Gwada A. M. 2:​7, 8.

9. Me kake koya sa’ad da kake wa’azi?

9 Yi wa mutane wa’azi yana taimaka maka ka koyi wasu abubuwa da yawa. Alal misali, za ka iya koyan yadda za ka yi aiki da mutane da lumana da kuma yadda za ka yi magana da kyau. Ban da haka ma, kana iya koyan kasancewa da gaba gaɗi da kuma basira da sanin ya kamata. (Mis. 21:5; 2 Tim. 2:24) Idan kana yin wa’azi da koyar da mutane, hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka tabbatar wa mutane daga Littafi Mai Tsarki abin da ka yi imani da shi. Ƙari ga haka, kana koyan yadda za ka yi aiki tare da Jehobah.​—1 Kor. 3:9.

10. Ta yaya za ka ji daɗin wa’azi ko da mutane kaɗan ne suke son yin nazari?

10 Ko da mutane da yawa a yankinku ba sa yarda ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, za ka iya kasancewa da farin ciki. Idan ya zo ga yin wa’azi, dukanmu a ikilisiya muna yin hakan tare da haɗin kai. Maƙasudinmu shi ne mu nemi waɗanda suke son su ji wa’azin da muke yi. Ko da yake mutum ɗaya ne kawai zai iya samo wani da zai zama Mashaidi, dukanmu mun yi wa’azin kuma muna yin farin cikin yin hakan. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Brandon ya yi shekaru tara yana wa’azi a yankin da mutane ba sa son jin wa’azi. Ya ce: “Ina son yin wa’azi don Jehobah ne ya umurce mu yi hakan. Na soma hidimar majagaba sa’ad da na gama makaranta. Ina jin daɗin ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyarmu kuma ina farin cikin ganin yadda suke samun ci gaba a ibada. Bayan na je Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure, sai aka tura ni wani wuri don in yi hidima. Amma ko da yake ni ban sami wani a wurin da na koya masa Littafi Mai Tsarki har ya yi baftisma ba, wasu sun yi hakan. Ina farin ciki cewa ni ma na yi wa’azin tare da su.”​—M. Wa. 11:6.

SHIRYE-SHIRYENKU ZA SU SA KU SAMU WASU ZARAFI

11. Waɗanne irin hidimomi ne matasa da yawa suke yi?

11 Matasa suna da zarafi da yawa na bauta wa Jehobah. Alal misali, da yawa daga  cikinsu suna yin aikin gine-gine da ake yi a faɗin duniya don ana bukatar a gina sababbin Majami’un Mulki da yawa. Kuma gina waɗannan majami’u aiki ne da ke ɗaukaka Allah. Ban da haka, zai sa ka farin ciki. Kamar yadda yake da sauran hidimomi da muke yi, yin wannan aikin yana sa mu yi cuɗanya da ’yan’uwa kuma hakan yana sa mu farin ciki. Ƙari ga haka, wannan aikin gine-gine yana koya mana abubuwa da yawa kamar yadda za mu yi aiki ba tare da jin rauni ba da yin aiki da ƙwazo da kuma ba da haɗin kai ga waɗanda suke ja-goranci.

Waɗanda suka soma hidima ta cikakken lokaci za su samu albarka sosai (Ka duba sakin layi na 11-13)

12. Ta yaya hidimar majagaba take sa mutum ya samu zarafin yin wasu hidimomi?

12 Wani ɗan’uwa mai suna Kevin ya ce: “Tun lokacin da nake yaro, ina son in yi hidima ta cikakken lokaci. Daga baya, na soma hidima sa’ad da nake ɗan shekara 19. Kuma ina yin aiki na ɗan lokaci tare da wani ɗan’uwa mai yin gini don na tallafa wa kai na a hidimar. Na koya yadda ake rufin gida da saka wundo da kuma ƙofofi. Ƙari ga haka, na yi shekara uku ina aiki tare da rukunin ba da agaji don mutanen da suka fuskanci mahaukaciyar guguwa, muna gyara gidajen ’yan’uwa da Majami’un Mulki. Sa’ad da na ji cewa ana bukatar masu gine-gine a Afirka ta Kudu, sai na cika fam ɗin kuma aka gayyace ni yin aiki a ƙasar. A nan Afirka, nakan je gina Majami’un Mulki dabam-dabam. Rukunin da nake aikin ginin da su suna kamar iyali ne a gare ni. Muna zama tare da nazarin Littafi Mai Tsarki tare kuma muna yin aiki tare. Ƙari ga haka, ina jin daɗin yin wa’azi da ’yan’uwa da ke yankin a kowane mako. Makasudai da na kafa sa’ad da nake yaro ya sa ni farin ciki a hanyoyin da ban taɓa tsammani ba.”

13. Ta yaya yin hidima a Bethel yake sa matasa farin ciki?

13 Wasu da suka ƙafa makasudan bauta wa Jehobah ta hidima na cikakken lokaci suna hidima yanzu a Bethel. Yin hidima a  Bethel yana sa mutum farin ciki domin duk aikin da ake yi a wajen don Jehobah ne. A Bethel ana wallafa Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke taimaka wa mutane su koya game da Jehobah. Wani da ke hidima a Bethel mai suna Dustin ya ce: “Na kafa makasudin yin hidima ta cikakken lokaci sa’ad da nake ɗan shekara tara, kuma na soma hidimar majagaba sa’ad da na gama makaranta. Bayan shekara ɗaya da rabi, sai aka gayyace ni Bethel, kuma a wurin na koya yadda ake buga littattafai kuma daga baya na yi aikin kwamfuta. A Bethel, ina jin daɗin jin rahoton aikin wa’azi da ake yi a faɗin duniya. Ina jin daɗin yin hidima a nan domin muna yin abin da yake taimake wa mutane su kusaci Jehobah.”

WAƊANNE MAKASUDAI NE ZA KU KAFA WA KANKU

14. Ta yaya za ku yi shirin soma hidima ta cikakken lokaci?

14 Ta yaya za ku yi shirin yin hidima ta cikakken lokaci? Don ku bauta wa Jehobah sosai, kuna bukatar ku kasance da halaye masu kyau. Saboda haka, ku riƙa yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai, ku riƙa bimbini sosai a kan abin da kuka karanta kuma ku yi ƙoƙari ku riƙa kalami a taron ikilisiya. A lokacin da kuke makaranta, ku kyautata yadda kuke yi wa mutane wa’azi. Ƙari ga haka, ku riƙa nuna cewa kun damu da mutane ta wajen tambayarsu ra’ayinsu da kuma saurarar amsoshinsu. Kuma ku riƙa yin abubuwa a ikilisiyarku, kamar share Majami’ar Mulki da kuma yin wasu ayyuka. Jehobah yana son yin amfani da masu tawali’u da waɗanda suke son su taimaka wa mutane. (Karanta Zabura 110:3; A. M. 6:​1-3) Manzo Bulus ya ce Timotawus ya yi hidima a wata ƙasa tare da shi domin “yan’uwa . . . suna shaidar” Timotawus.​—A. M. 16:​1-5.

15. Ta yaya za ku yi shirin biyan bukatunku?

15 Masu hidima ta cikakken lokaci suna bukatar su yi aikin da zai taimaka musu su biya bukatunsu. (A. M. 18:​2, 3) Wataƙila kuna iya koyan wata sana’a da za ta sa ku samu aiki na ɗan lokaci da ake yi a yankinku. Yayin da kuke shirin yin hakan, ku nemi shawarar mai kula da da’irarku da kuma majagaba da ke da’irarku. Ku tambaye su irin sana’ar da majagaba za su iya yi. Ƙari ga haka, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘ku damƙa ma Ubangiji ayyukanku, nufe-nufenku kuma za su tabbata.’​—Mis. 16:3; 20:18.

16. Ta yaya yin hidima ta cikakken lokaci sa’ad da kuke matasa zai shirya ku don yin rayuwa a nan gaba?

16 Ku kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ku ji daɗin rayuwa a nan gaba. (Karanta 1 Timotawus 6:​18, 19.) Yin hidima ta cikakken lokaci yana sa ku haɗu da wasu ’yan’uwa da suke hidima ta cikakken lokaci kuma yana taimaka muku ku manyanta sosai. Ƙari ga haka, mutane da yawa sun lura cewa yin wannan hidima sa’ad da suke matashi ya taimaka musu su yi nasara a aure. Sau da yawa, waɗanda suka yi hidimar majagaba kafin su yi aure sun ci gaba da hidimarsu.​—Rom. 16:​3, 4.

17, 18. Ta yaya yin shiri ya shafi zuciyarku?

17 Ta yaya yin shiri ya shafi zuciyarmu? Zabura 20:4 ta ce game da Jehobah: “Shi biya maka muradin zuciyarka, shi cika dukan shawararka.” Saboda haka, ku yi tunanin abin da kuke son ku yi da rayuwarku. Ku yi la’akari da abin da Jehobah yake yi a zamaninmu da abin da za ku iya yi don ku yi masa hidima. Sai ku yi shirin yin abin da zai faranta masa rai.

18 Ku yi amfani da zarafin da kuke da shi yanzu don ku yi wa Jehobah hidima, kuma za ku yi farin ciki yayin da kuke ɗaukaka shi. Hakika, ‘ku faranta zuciyarku cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya muku muradin zuciyarku.’​—Zab. 37:4.

^ sakin layi na 7 An sauya da Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.