Jehobah “ya san abin da aka yi mu da shi, yana kuma tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne.”​—ZAB. 103:14.

WAƘOƘI: 30, 10

1, 2. (a) Ta yaya yadda Jehobah yake bi da mutane ya bambanta da yadda shahararru suke bi da mutane? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

MUTANEN da suka shahara suna yawan nuna wa waɗansu “iko” har ma su riƙa zalunta da kuma wulaƙanta su. (Mat. 20:25; M. Wa. 8:9) Amma ba haka Jehobah yake ba! Duk da cewa shi ne Maɗaukaki, yana la’akari da mutane ajizai. Yana kula da mu da kuma biyan bukatunmu. Da yake yana “tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne,” ba ya sa mu yin abin da ya fi ƙarfinmu.​—Zab. 103:​13, 14.

2 A Littafi Mai Tsarki, da akwai labarai da yawa da suka nuna yadda Jehobah ya yi la’akari da mutanensa. Bari mu tattauna guda uku daga cikinsu. Na farko shi ne yadda Jehobah ya taimaka wa Sama’ila ya idar da saƙon hukunci ga Babban Firist Eli. Na biyu, Jehobah ya yi haƙuri sa’ad da Musa ya ƙi ya yi wa Isra’ilawa ja-goranci. Na uku kuma shi ne yadda Jehobah ya yi la’akari da yanayin Isra’ilawa sa’ad da yake fitar da su daga ƙasar Masar. Yayin da muke tattauna waɗannan misalan, bari mu  mai da hankali ga darussan da za su koya mana game da Jehobah.

YA YI LA’AKARI DA WANI ƘARAMIN YARO

3. Wane abu ne ya faru da Sama’ila wata rana daddare, kuma wace tambaya ce za mu iya yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

3 A lokacin da Sama’ila yake ƙarami ne ya soma yi wa “Yahweh hidima” a mazauni. (1 Sam. 3:1) Wata rana daddare sa’ad da Sama’ila yake barci, wani abin mamaki ya faru. * (Karanta 1 Sama’ila 3:​2-10.) Ya ji wata murya tana kiran sa. Sama’ila ya ɗauka cewa Babban Firist Eli ne yake kiran sa, sai ya je wurinsa da gudu, ya ce: “Ga ni nan, ai, ka kira ni.” Amma Eli ya ce bai kira shi ba. Da hakan ya faru sau uku, sai Eli ya fahimci cewa Allah ne yake kiran Sama’ila. Don haka, sai ya gaya wa yaron yadda zai amsa idan Jehobah ya sake kiran sa kuma Sama’ila ya bi shawarar. Me ya sa Jehobah bai nuna wa Sama’ila tun da farko cewa shi ne ke kiran sa ba? Littafi Mai Tsarki bai faɗi dalilin ba, amma zai yiwu cewa Jehobah ya yi hakan ne domin ya yi la’akari da Sama’ila. Ta yaya?

4, 5. (a) Mene ne Sama’ila ya yi sa’ad da Jehobah ya ba shi saƙo ya gaya wa Eli, kuma mene ne ya faru washegari? (b) Mene ne wannan labarin ya koya mana game da Jehobah?

4 Karanta 1 Sama’ila 3:​11-18. A dokar da Jehobah ya ba da ta hannun Musa, ya umurci yara su riƙa yi wa tsofaffi ladabi musamman ma waɗanda ke yin ja-goranci. (Fit. 22:28; L. Fir. 19:32) Babu shakka, zai yi wuya a ce Sama’ila wanda yaro ne a lokacin zai je wurin Eli da gaba gaɗi ya idar da saƙon hukuncin da Jehobah ya ba shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya ji tsoro ya faɗa wa Eli ru’uyar.” Amma, Allah ya sa Eli ya san cewa shi ne yake kiran Sama’ila. A sakamakon haka, Eli ya umurce Sama’ila cewa ya faɗa masa dukan abin da Allah ya ce. Ya ce masa kada ya ‘ɓoye masa kome.’ Sama’ila ya yi biyayya kuma ya “faɗa masa kome da kome.”

5 Eli bai yi mamaki da ya ji wannan saƙon ba. Me ya sa? Domin kafin wannan lokacin wani “annabi” wanda ba a ambata sunansa ba ya gaya wa Eli irin wannan saƙon hukunci. (1 Sam. 2:​27-36) Wannan labari game da Sama’ila da Eli ya nuna cewa Jehobah mai hikima ne kuma yana yin la’akari da mutane.

6. Waɗanne darussa ne muka koya daga yadda Jehobah ya taimaka wa Sama’ila?

6 Kai matashi ne? Idan haka ne, labarin Sama’ila ya nuna cewa Jehobah ya san matsalolin da kake fuskanta da kuma yadda kake ji. Wataƙila kana jin kunyar yi wa mutanen da suka girme ka wa’azi ko kuma ka fita dabam don ba ka yin abin da tsararka suke yi. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ya taimaka maka. Don haka, ka gaya masa dukan abubuwan da ke damun ka. (Zab. 62:8) Ka yi tunani sosai a kan misalin matasa kamar Sama’ila da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ka tattauna da ’yan’uwan da suka manyanta ko kuma tsararka da suka fuskanci irin wannan matsalar don su gaya maka yadda suka magance ta. Babu shakka, suna iya gaya maka yadda Jehobah ya taimaka musu a hanyar da ba su yi zato ba.

YA YI LA’AKARI DA MUSA

7, 8. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya damu da yadda Musa yake ji?

7 A lokacin da Musa yake shekara 80, Jehobah ya ba shi wani aiki mai wuya. Wane aiki ke nan? Zai ceto Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar. (Fit. 3:10)  Babu shakka, haka ya ba Musa mamaki sosai domin ya yi shekaru 40 yana kiwo a ƙasar Midiya. Sai ya ce: “Wane ne ni da har zan tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da jama’ar Isra’ila daga cikin ƙasar Masar?” Amma Jehobah ya tabbatar wa Musa da cewa ‘zai kasance tare da shi.’ (Fit. 3:​11, 12) Ƙari ga haka, Jehobah ya yi wa Musa alkawari cewa: Dattawan Isra’ila “za su kasa kunne ga maganarka.” Duk da haka Musa ya ce: “Idan . . . ba su kasa kunne ga maganata ba fa?” (Fit. 3:18; 4:1) Kamar dai Musa yana cewa abin da Jehobah ya ce ba zai faru ba! Amma Jehobah ya yi haƙuri da shi, har ma ya ba shi ikon yin mu’ujizai. Hakan ya sa Musa ya zama mutum na farko a Littafi Mai Tsarki da ya yi mu’ujiza.​—Fit. 4:​2-9, 21.

8 Duk da haka, Musa ya nemi hujjar ƙin yin aikin ta wurin cewa bai ƙware a yin magana ba. Sai Allah ya ce: “Zan bi da bakinka, in kuma koya maka abin da za ka faɗa.” Shin Musa ya amince ya yi aikin ne? A’a, ya roƙi Allah ya ba wani aikin. Hakan ya sa Jehobah fushi. Amma duk da haka ya yi la’akari da Musa da kuma yadda yake ji. Don haka, Jehobah ya sa Haruna ya zama wanda zai riƙa magana a madadin Musa.​—Fit. 4:​10-16.

9. Ta yaya haƙurin Jehobah da kuma alherinsa ya taimaka wa Musa ya zama shugaba nagari?

9 Mene ne labarin nan ya koya mana game da Jehobah? Da yake Jehobah Maɗaukaki ne, da ya yi amfani da ikonsa don ya tilasta wa Musa ya yi abin da ya umurce shi. Jehobah bai yi hakan ba, amma ya yi haƙuri da bawansa mai tawali’u kuma ya tabbatar masa da cewa zai kasance da shi. Shin ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa? E! Musa ya zama fitaccen shugaba. Ya yi la’akari da Isra’ilawa kamar yadda Jehobah ya yi la’akari da shi.​—L. Ƙid. 12:3.

Kana bin misalin Jehovah sa’ad da kake cuɗanya da mutane? (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya za mu amfana idan muka bi misalin Jehobah na yin la’akari da mutane?

10 Waɗanne darussa ne za mu iya koya? Kai mai iko ne idan kai miji ne ko mahaifi  ko kuma dattijo. Don haka, yana da muhimmanci ka yi koyi da yadda Jehobah yake yin la’akari da mutane da kuma haƙuri sa’ad da kake sha’ani da su! (Kol. 3:​19-21; 1 Bit. 5:​1-3) Ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi misalin Jehobah da kuma Yesu Kristi. Domin hakan zai sa ya yi wa mutane sauƙi su riƙa gaya maka abin da ke damunsu kuma su riƙa samun ƙarfafa daga gare ka. (Mat. 11:​28, 29) Ban da haka, za ka kafa musu misali mai kyau.​—Ibran. 13:7.

MAI IKO DA KE YIN LA’AKARI DA MU

11, 12. Ta yaya Jehobah ya kāre Isra’ilawa sa’ad da yake fitar da su daga Masar?

11 Wataƙila Isra’ilawa fiye da miliyan uku ne suka bar ƙasar Masar a shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu. A cikinsu da akwai yara da tsofaffi da guragu ko kuma marasa lafiya. Babu shakka, irin waɗannan mutane suna bukatar Shugaba mai ƙauna da zai nuna ya damu da su. Jehobah ya yi amfani da Musa don ya nuna cewa shi irin wannan shugaba ne. Saboda haka, Isra’ilawa ba su ji tsoro ba sa’ad da suke barin Masar, wadda ita ce kaɗai ƙasar da suka sani.​—Zab. 78:​52, 53.

12 Ta yaya Jehobah ya kāre mutanensa kuma ya sa suka kasance da kwanciyar hankali? Jehobah ya tsara al’ummar “kamar sojojin da suke a shirye domin yaƙi.” (Fit. 13:18) Babu shakka, wannan tsarin ya tabbatar wa Isra’ilawa da cewa Jehobah ne yake yi musu ja-goranci. Ban da haka, da “rana ya bi da su da girgije, da dare ya bi da su da hasken wuta.” Ta hakan, Jehobah ya nuna musu cewa yana tare da su. (Zab. 78:14) Kamar dai Jehobah yana ce musu: “Kada ku ji tsoro. Ina tare da ku kuma zan kāre ku.” Babu shakka, suna bukatar wannan tabbaci domin abin da zai faru a nan gaba!

Ta yaya Jehobah ya kula da Isra’ilawa a Jar Teku? (Ka duba sakin layi na 13)

13, 14. (a) Ta yaya Jehobah ya kāre Isra’ilawa a Jar Teku? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna wa Masarawa ƙarfinsa?

13 Karanta Fitowa 14:​19-22. A ce kana tare da Isra’ilawa a gaɓar Jar Teku kuma ba ku da mafita. Sojojin Masar suna bayanku kuma a gabanku ga Jar teku. Sai Allah ya nuna ƙarfinsa. Girgijen ya koma bayan zangon don ya raba tsakaninku da Masarawa. Hakan ya sa Masarawa cikin duhu. Amma zangonku akwai haske! Sai Musa ya miƙa hannunsa bisa tekun kuma iskar gabas mai ƙarfi ta taso ta raba tekun. Kai da iyalinka da dabbobinka da kuma sauran al’ummar kuka shiga tekun kuna tafiya. Nan ba da daɗewa ba, sai ka lura cewa yashin tekun ba a jike yake ba kuma ba ya santsi. Amma ya bushe, kuma hakan ya sa yin tafiya ya kasance da sauƙi. Saboda haka, har yara da tsofaffi da kuma marasa lafiya suka haye tekun.

14 Karanta Fitowa 14:​23, 26-30. Yayin da hakan yake faruwa, Fir’auna wawa mai girman kai ya sunduma cikin tekun yana bin ku. Sai Musa ya sake miƙa hannunsa bisa tekun. Amma yanzu, ruwan da ya rabu biyu ya haɗu kuma ya halaka Fir’auna da sojojinsa!​—Fit. 15:​8-10.

15. Mene ne wannan labarin ya koya mana game da Jehobah?

15 Wannan labarin ya nuna cewa Jehobah Allah ne mai tsara abubuwa da kyau. Hakan yana taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa zai kāre mu. (1 Kor. 14:33) Jehobah ya nuna cewa shi makiyayi ne mai ƙauna da ke kula da mutanensa a hanyar da ta dace, kuma ya kāre su daga maƙiyansu. Babu shakka, hakan yana ƙarfafa mu sosai don ƙarshen wannan zamani ya kusa!​—K. Mag 1:33.

16. Ta yaya za mu amfana idan muka yi bitar yadda Jehobah ya ceci Isra’ilawa?

16 A yau ma, Jehobah yana kula da  mutanensa gabaki ɗaya. Yana taimaka musu su kasance da dangantaka mai kyau da shi kuma yana kāre su daga maƙiyansu. Jehobah zai ci gaba da yin hakan har lokacin ƙunci mai girma da ke nan tafe. (R. Yar. 7:​9, 10) Don haka, ko da mutanen Allah matasa ne ko tsofaffi ko marasa lafiya, ba za su yi fargaba ba a lokacin ƙunci mai girma. * A maimakon haka, za su kasance da gaba gaɗi! Za su tuna da abin da Yesu ya faɗa, cewa: “Idan waɗannan abubuwa suka fara faruwa, ku shirya kanku sosai domin cetonku ya yi kusa.” (Luk. 21:28) Za su kasance da wannan tabbaci har ma a lokacin da Gog, wato al’ummai da suka haɗa kai da suka fi Fir’auna ƙarfi za su kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:​2, 14-16) Me ya sa mutanen Allah za su kasance da gaba gaɗi? Domin sun san cewa Jehobah ba ya canjawa. Zai nuna cewa shi mai kula ne da kuma mai iko da ke ceton mutanensa.​—Isha. 26:​3, 20.

17. (a) Ta yaya za mu amfana daga labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah ya yi la’akari da mutanensa? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 A talifin nan, mun ga wasu misalan yadda Jehobah ya nuna ya damu da mutanensa. Ya yi hakan a lokacin da yake yi musu ja-goranci da kuma a lokacin da ya cece su. Yayin da kake yin bimbini a kan labarin nan, ka mai da hankali ga abubuwan da suka bayyana irin halayen da Jehobah yake da su. Idan ka yi hakan, za ka daɗa ƙaunar Jehobah kuma bangaskiyarka za ta yi ƙarfi sosai. A talifi na gaba, za mu ga hanyoyin da za mu iya bin misalin Jehobah na yin la’akari da mutane. Za mu mai da hankali ga yadda za mu yi hakan a iyali da ikilisiya da kuma sa’ad da muke wa’azi.

^ sakin layi na 3 Masanin tarihin Yahudawa mai suna Josephus ya ce Sama’ila yana ɗan shekara 12 a lokacin.

^ sakin layi na 16 Zai yiwu cewa bayan yaƙin Armageddon, naƙasassu za su ci gaba cikin yanayinsu. A lokacin da Yesu yake duniya, ya warkar da “kowane irin ciwo da rashin lafiya.” Hakan ya nuna mana abin da zai yi a nan gaba ga waɗanda suka tsira wa yaƙin Armageddon. Sai bayan yaƙin ne za a warkar da su. (Mat. 9:35) Waɗanda aka tayar daga mutuwa za su tashi da ƙoshin lafiya.