Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

“Maganar Ubangiji Za ta Tsaya Har Abada”

“Maganar Ubangiji Za ta Tsaya Har Abada”

“Ciyawa takan yi yaushi, fure shi yanƙwane, amma maganar Ubangiji za ta tsaya har abada.”​—ISHA. 40:8.

WAƘOƘI: 116, 115

1, 2. (a) Yaya rayuwa za ta kasance in babu Littafi Mai Tsarki? (b) Mene ne zai taimaka mana mu amfana daga karanta Littafi Mai Tsarki?

YAYA rayuwarka za ta kasance, da a ce babu Littafi Mai Tsarki? Da ba za ka samu shawarwari da za su taimaka maka a rayuwa ba. Ban da haka ma, da ba ka san gaskiya game da Allah da rayuwa da kuma nan gaba ba. Kuma da ba za ka san yadda Jehobah ya yi sha’ani da mutane a zamanin dā ba.

2 Muna godiya don yanayinmu ba haka yake a yau ba. Jehobah ya ba mu Kalmarsa wato Littafi Mai Tsarki. Kuma ya tabbatar mana cewa kalmarsa za ta dawwama har abada. Manzo Bitrus ya yi ƙaulin littafin Ishaya 40:​8, kuma wurin ba ya magana game da Littafi Mai Tsarki amma saƙon da ke cikinsa. (Karanta 1 Bitrus 1:​24, 25.) Masu ƙaunar Allah sun san cewa za su amfana sosai idan suka karanta Littafi Mai Tsarki a yaren da suka fi fahimta. A ƙarnuka da suka shige bai kasance da sauƙi mutane su fassara da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki ba amma sun yi iya ƙoƙarinsu su yi hakan. Don Allah yana son “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”​—1 Tim. 2:​3, 4.

3. Mene ne za mu yi nazarinsa a wannan talifin? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

 3 A wannan talifin, za mu ga yadda Kalmar Allah ta jimre (1) sa’ad da yaruka suka canja, (2) sa’ad da siyasa ta kawo wasu canje-canje da suka shafi yaren da kuma (3) sa’ad da ake tsananta wa mafassaran Littafi Mai Tsarki. Ta yaya za mu amfana ta yin wannan nazarin? Nazarin zai taimaka mana mu ɗauki Kalmar Allah da muhimmanci sosai. Ban da haka ma, zai taimaka mana mu kusaci Jehobah wanda shi ne ya sa aka rubuta Littafi Mai Tsarki domin mu.​—Mi. 4:2; Rom. 15:4.

SA’AD DA YARUKA SUKA CANJA

4. (a) Ta yaya yaruka suke canjawa da shigewar lokaci? (b) Me ya nuna mana cewa Allah ba ya son wani yare fiye da wani ba, kuma me sanin hakan zai motsa ka ka yi?

4 Da shigewar lokaci yaruka suna canjawa har da kalmomi da kuma yadda ake furta su. Wataƙila akwai wasu kalmomi a yarenku ma da ma’anarsu suka canja. Haka ma yake a yaren Ibrananci da kuma Girka da aka rubuta yawancin littattafan Littafi Mai Tsarki da su. Yaren Ibrananci da kuma girka da ake yi a yau ya bambanta da wanda aka yi a zamanin dā. Don haka, duk wanda yake so ya karanta da kuma fahimci Littafi Mai Tsarki yana bukatar ya karanta wanda aka fassara, ko da mutumin yana fahimtar yaren Ibrananci da kuma girka da ake yi a yau. Wasu suna ganin idan suka koyi Ibrananci da kuma Girka da ake yi a dā, za su fahimci Littafi Mai Tsarki. Amma hakan ba zai sa su fahimci Littafi Mai Tsarki ba. * A yau muna godiya sosai saboda an fassara Littafi Mai Tsarki zuwa yaruka fiye da 3,200. Babu shakka, hakan ya nuna mana cewa Jehobah yana son “kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma,” su amfana ta wurin karanta Kalmarsa. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:6.) Hakika, sanin hakan yana sa mu mu kusaci Allah sosai.​—A. M. 10:34.

5. Me ya sa fassarar King James take da muhimmanci?

5 An fassara Littafi Mai Tsarki zuwa wasu yaruka kuma canji a yaren ya shafi yarukan ma. Saboda haka, wasu fassarar Littafi Mai Tsarki da aka yi suna da sauƙin fahimta a lokacin da aka fassara su, amma da shigewar lokaci, mutane ba sa fahimtar su. Ka yi la’akari da wannan misalin da ya shafi fassarar Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci. An wallafa fassarar King James da farko a shekara ta 1611, a lokacin shi ne fassarar Littafi Mai Tsarki na Turanci da mutane suka fi sani. Kuma kalmomin da aka yi amfani da su a cikin fassarar sun shafi Turanci. * Ban da haka ma, fassarar Littafi Mai Tsarki na King James bai yi amfani da sunan Allah yadda ya kamata ba. Littafin ya yi amfani da sunan Allah “Jehobah” a ayoyi kaɗan sai aka yi amfani da kalmar nan “LORD” wato, Ubangiji da manyan harufa a wuraren da sunan Allah na asali yake. Ƙari ga haka, an yi amfani da “LORD” a wasu ayoyi na Nassosin Helenanci na Kirista da aka wallafa daga baya ma. Ta yin hakan, mafassaran sun fahimci cewa sunan Allah yana bukatar ya bayyana a Nassosin Helenanci na Kirista.

6. Me ya sa muke godiya don fassarar New World Translation?

6 Ƙari ga haka, yanzu yawancin mutane ba sa amfani da kalmomin aka yi amfani  da su a fassarar King James. Haka ma yake da fassarar da aka yi zuwa wasu yaruka. Don haka, muna farin cikin samun New World Translation of the Holy Scriptures da aka yi amfani da kalmomin da mutane suke amfani da su a harkokin su na yau da kullum. Za a iya samun rabin wannan fassarar ko gabaki ɗayansa a yaruka fiye da 150. Kuma hakan yana nufin cewa mutane da yawa za su iya karantawa a yarensu. Ƙari ga haka, da yake yana da sauƙin fahimta, yana taɓa zuciyar mutane sosai. (Zab. 119:97) Ban da haka ma, a fassarar New World Translation an mayar da sunan Allah zuwa inda yake a dā.

YAREN DA MUTANE SUKA SABA YI

7, 8. (a) Me ya sa Yahudawa da yawa kafin haihuwar Yesu ba su fahimci Nassosin Ibrananci ba? (b) Mene ne Septuagint a yaren Girka?

7 Duk da cewa siyasa takan kawo canje-canje da suke shafan yaren da mutane suke yi, Jehobah ya tabbata cewa mutane sun sami Littafi Mai Tsarki a yaren da suka fi fahimta. Alal misali, littattafai 39 na farko na Littafi Mai Tsarki, Yahudawa ko kuma Isra’ilawa ne suka rubuta. Don su ne Jehobah da farko ya “amince su da ajiyar zantattukan Allah.” (Rom. 3:​1, 2) Amma a ƙarni na uku kafin haihuwar Yesu, Yahudawa da yawa ba sa fahimtar yaren Ibrananci. Me ya sa? Dalilin shi ne a lokacin da Alexander the Great ya ci wurare da yawa da yaƙi ya faɗaɗa daularsa na Girka sosai. (Dan. 8:​5-7, 20, 21) Hakan ya sa yaren Girka ya zama yaren da mutane da yawa daga cikin waɗanda ya ci da yaƙi suke amfani da shi har ma da Yahudawa. Da yake Yahudawa sun soma yin yaren Girka, fahimtar Nassosin Ibrananci ya zama musu da wuya sosai. Me za a yi don a taimaka musu?

8 Misalin shekaru 250 kafin haihuwar Yesu ne aka fassara littattafai biyar na farko na Littafi Mai Tsarki daga Ibrananci zuwa yaren Girka. Daga baya, an kammala fassara sauran littattafan. Kuma wannan fassarar ce aka sani da sunan nan Septuagint a yaren Girka. Kuma ita ce fassara ta farko na Littafi Mai Tsarki da aka fassara duka Nassosin Ibrananci.

9. (a) Ta yaya Septuagint da kuma wasu fassarar Littafi Mai Tsarki suka shafi masu karatu? (b) Wane sashen Nassin Ibrananci ne ka fi so?

9 Fassarar Septuagint ta sa Yahudawa da suke yin yaren Girka da kuma wasu su iya karanta Nassosin Ibrananci. Babu shakka, karanta da kuma sauraran Kalmar Allah a yarensu ya sa su farin ciki sosai. Daga baya, an fassara wasu sashen Littafi Mai Tsarki zuwa wasu yarukan da mutane suke yi kamar su Syriac da Gothic da kuma Latin. Mutane da yawa sun soma karanta Littafi Mai Tsarki a yaren da suka fi fahimta kuma babu shakka, hakan ya sa sun sami wurare a cikin littafin da suke so sosai kamar mu ma a yau. (Karanta Zabura 119:​162-165.) Hakika, Kalmar Allah ta jimre duk da yadda yaruka suke canjawa.

YADDA AKA TSANANTA WA MAFASSARAN LITTAFI MAI TSARKI

10. Me ya sa mutane da yawa ba su da Littafi Mai Tsarki a zamanin John Wycliffe?

10 A wasu lokuta, mutane da suke da iko sun yi iya ƙoƙarinsu don su hana mutane samun Littafi Mai Tsarki. Amma duk da haka, mutane da suke son Kalmar Allah sun yi tsayin dāka don kowa ya sami Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ka yi la’akari da labarin John Wycliffe wani masanin addini wanda ya yi rayuwa a Ingila shekaru 600 da suka shige. Wannan mutumin yana son kowa ya sami Littafi Mai Tsarki kuma ya amfana daga karantawa. Amma a lokacin, mutane da yawa  a Ingila ba su da Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Wani dalili shi ne, mutane da yawa ba za su iya sayan Littafi Mai Tsarki ba, domin da hannu aka rubuta saboda haka, yana da tsada sosai. Ban da haka ma, yawancin mutanen ba su iya karatu ba. Babu shakka, wataƙila sukan ji ana karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da suka je coci, amma wataƙila ba sa fahimtar abin da ake karantawa. Me ya sa? Domin (Vulgate) ne Littafi Mai Tsarki da aka ce Coci su riƙa amfani da shi kuma an rubuta wannan littafin a yaren Latin, yaren da mutane ba sa yi kuma! Ta yaya Jehobah ya tabbata cewa mutane sun sami Littafi Mai Tsarki a yarensu?​—Mis. 2:​1-5.

John Wycliffe da kuma wasu sun so kowa ya sami nasa Littafi Mai Tsarki. Shin kai ma abin da kake son yi ke nan? (Ka duba sakin layi na 11)

11. Ta yaya Littafi Mai Tsarki na Wycliffe ya shafi mutane?

11 A shekara ta 1382, John Wycliffe da abokan aikinsa sun fassara Littafi Mai Tsarki zuwa Turanci, kuma daga baya aka soma kiran littafin, Littafi Mai Tsarki na Wycliffe. Wasu mabiyan Wycliffe sun soma amfani da littafin sosai. Waɗannan mutanen suna son Kalmar Allah sosai kuma suna yin tafiya da kafa zuwa ƙauyuka a duk Ingila suna wa’azi. Sukan karanta wa mutane da suka haɗu da su Littafi Mai Tsarki kuma su ba su waɗanda da aka kofa da hannu. Abin da suke yi ya sa mutane da yawa suka san Littafi Mai Tsarki.

12. Mene ne limaman addinai suka yi wa Wycliffe da littattafansa?

12 Mene ne limaman addinai suka yi? Sun ƙi jinin Wycliffe da littafin da ya fassara da kuma abokan aikinsa, sai suka soma tsananta wa rukunin Lollards sosai. Sun hallaka dukan Littafi Mai Tsarki da Wycliffe ya fassara da suka samu. Har ma bayan mutuwar Wycliffe suka ce wai shi maƙiyin coci ne. Da yake ba za su iya azabtar da shi ba don ya riga ya mutu, sai suka je suka tono ƙasusuwansa suka ƙona kuma suka zuba tokan a kogin Swift. Amma limaman ba su iya hana mutane da yawa da suka so karanta da kuma fahimtar Littafi Mai Tsarki yin hakan ba. Wasu shekaru bayan hakan, mutane da yawa a Turai da kuma wasu wurare a faɗin duniya sun soma fassara Littafi Mai Tsarki da kuma rarrabawa don mutane da yawa su amfana.

“WANDA YAKE KOYA MAKA ZUWA AMFANINKA”

13. Me muke da tabbacinsa, kuma yaya hakan yake ƙarfafa bangaskiyarmu?

13 Allah ne ya hure a rubuta Littafi Mai Tsarki. Amma hakan ba ya nufin cewa  Allah ne ya hure fassara Septuagint ko Littafi Mai Tsarki na Wycliffe ko kuma na King James kai tsaye. Amma idan muka yi la’akari da yadda aka wallafa fassara dabam-dabam, hakan zai nuna mana cewa abin da Jehobah ya faɗa ya faru kuma Kalmarsa ta jimre. Kuma hakan yana sa mu sake ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Jehobah zai cika dukan alkawarin da ya yi.​—Josh. 23:14.

14. Ta yaya abin da muka koya daga kalmar Allah take sa mu riƙa ƙaunar Allah sosai?

14 Sanin yadda Jehobah ya kāre Kalmarsa zai ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya sa mu ƙara ƙaunarsa sosai. * Amma me ya sa Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki kuma ya yi alkawarin kāre shi? Ya yi hakan ne don yana ƙaunarmu kuma yana son ya koya mana yadda za mu amfana. (Karanta Ishaya 48:​17, 18.) Abin da Jehobah ya yi mana yana sa mu riƙa yi masa biyayya kuma mu ci gaba da ƙaunarsa.​—1 Yoh. 4:19; 5:3.

15. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

15 Muna godiya sosai don samun Littafi Mai Tsarki. Amma ta yaya za mu amfana daga karanta shi? Ta yaya za mu taimaka ma waɗanda muka haɗu da su a wa’azi su riƙa daraja Littafi Mai Tsarki? Kuma ta yaya masu koyarwa a ikilisiya za su nuna cewa Littafi Mai Tsarki ne ainihi suke koyarwa? Za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

^ sakin layi na 4 Ka duba talifin nan “Do You Need to Learn Hebrew and Greek?” a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba 2009 a Turanci.

^ sakin layi na 5 An samo wasu karin magana da aka yi amfani da su a Turanci daga fassarar King James. Alal misali: “ya fāɗi a fuskarsa” da “liƙe ma fatata” da kuma “ku zazzage zuciyarku.”​—Lit. Lis. 22:31; Ayu. 19:20; Zab. 62:8.

^ sakin layi na 14 Ka duba akwatin nan “ Ka Zo Ka Gani da Kanka!