Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Hasumiyar Tsaro (Ta Nazari)  |  Satumba 2017

Ka Rika Kame Kanka

Ka Rika Kame Kanka

’Yar “Ruhu . . . kamewa” ne.​—GAL. 5:22, 23.

WAƘOƘI: 83, 52

1, 2. (a) Mene ne rashin kame kai yake jawowa? (b) Me ya sa batun kame kai yake da muhimmanci a yau?

KAMEWA hali ne mai kyau da Allah yake so mu koya. (Gal. 5:​22, 23) Jehobah yana kame kansa sosai. Da yake mutane ajizai ne, ba ya musu sauƙi su riƙa kame kansu. Hakika, mutane da yawa a yau suna fuskantar matsaloli don ba sa kame kansu. Hakan zai iya sa su rashin yin abubuwa da sauri da rashin ƙwazo a makaranta ko kuma a wurin aiki. Ƙari ga haka, zai iya sa mutane su riƙa zagi da maye da mugunta da kashe aure da cin bashi. Ban da haka ma, rashin kame kai zai sa mutum ya shiga cikin matsalar da za ta iya sa a kai shi fursuna ko ya yi baƙin ciki ko kuma ya kamu da cuta. Hakan ma zai iya sa mutum ya ɗauki cikin shige.​—Zab. 34:​11-14.

2 Hakika, mutanen da ba sa kame kansu suna jawo ma kansu da kuma wasu matsaloli. Rashin kame kai yana daɗa ƙaruwa. Bincike da aka yi kwanan nan ya nuna cewa mutane sun fi kame kansu a dā a kan yanzu. Hakan ba abin mamaki ba ne ga masu nazarin Kalmar Allah domin Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane za su zama “marasa kamewa” kuma hakan zai nuna cewa muna cikin “kwanaki na ƙarshe.”​—2 Tim. 3:​1-3.

3. Me ya sa ya dace Kiristoci su riƙa kame kansu?

3 Me ya sa ya dace ka riƙa kame kanka? Muna da dalilai biyu masu muhimmanci. Na farko, an lura cewa mutane da suke  kame kansu ba sa cika faɗa cikin matsaloli. Sun fi riƙe kansu da samun abokai kuma ba sa saurin fushi ko alhini da baƙin ciki kamar mutanen da ba sa kame kansu. Na biyu, idan muka yi tsayin daka a lokacin da muke fuskantar jarabobi kuma muka kame kanmu sa’ad da muke fama da sha’awoyin banza, Allah zai amince da mu. Labarin Adamu da Hauwa’u ya nuna hakan. (Far. 3:6) Tun lokacin Adamu, ka yi tunanin mugun sakamakon da mutanen da ba su kame kansu suke fuskanta.

4. Mene ne zai taimaka ma kowane mutum da yake fama ya riƙa kame kansa?

4 Ba zai yiwu mutane su riƙa kame kansu a kowane lokaci ba. Kuma Jehobah ya san cewa ba ya wa bayinsa sauƙi su yi hakan, shi ya sa yake son ya taimaka musu su shawo kan wannan halin. (1 Sar. 8:​46-50) Tun da yake Jehobah Abokinmu ne mai ƙaunarmu, yana ƙarfafa mutane da suke so su bauta masa amma yana musu wuya su kame kansu a wasu lokuta. Bari mu bincika misalin Jehobah. Ƙari ga haka, za mu koyi darasi daga labarai masu kyau da marasa kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma za mu bincika wasu shawarwari da za su taimaka mana mu riƙa kame kanmu.

JEHOBAH YA KAFA MANA MISALI

5, 6. Wane misali ne Jehobah ya kafa game da kame kai?

5 Jehobah yana kame kansa sosai domin ba ya kuskure a dukan abubuwan da yake yi. (K. Sha. 32:4) Amma, mu ajizai ne. Duk da haka, idan muna son mu san yadda za mu riƙa kame kanmu, muna bukatar mu bincika misalin Jehobah domin mu yi koyi da shi sosai. A waɗanne hanyoyi na musamman ne Jehobah ya kame kansa?

6 Ka yi tunanin yadda Jehobah ya kame kansa a lokacin da Shaiɗan ya yi tawaye. Jehobah yana bukatar ya yi wani abu don ya magance wannan matsalar. Babu shakka cewa wannan tawayen ya sa mala’iku masu aminci baƙin ciki da kuma fushi. Wataƙila kai ma kana jin hakan idan ka yi tunanin duk matsalolin da Shaiɗan ya jawo a wannan duniyar. Amma, Jehobah ba ya yin abubuwa da garaje kuma yana ɗaukan matakin da ya dace. Ƙari ga haka, ba ya saurin fushi kuma yana bi da Shaiɗan ɗan tawaye yadda ya dace. (Fit. 34:6; Ayu. 2:​2-6) Me ya sa? Jehobah yana jinkirin ɗaukan mataki domin ba ya son a halaka kowa amma “duka su kai ga tuba.”​—2 Bit. 3:9.

7. Mene ne za mu iya koya daga misalin Jehobah?

7 Yadda Jehobah ya kame kansa ya koya mana cewa bai kamata mu riƙa yin hanzarin yin abubuwa ba amma mu riƙa tunani sosai kafin mu ɗauki wani mataki ko mu faɗi wasu abubuwa. Ƙari ga haka, ya kamata ka ɗau lokaci sosai kuma ka yi tunani idan kana so ka tsai da wata shawara mai muhimmanci. Ka yi addu’a Allah ya ba ka hikimar faɗa ko yin abin da ya dace. (Zab. 141:3) A lokacin da mutum yake fuskantar matsala, yana da sauƙi ya ɗauki matakin da bai dace ba. Mutane da yawa suna da-na-sani don baƙar magana da suka yi ko kuma matakin da suka ɗauka da garaje.​—Mis. 14:29; 15:28; 19:2.

MISALAI MASU KYAU DA MARASA KYAU

8. (a) A ina ne za mu samu misalan mutane da suka nuna halayen da Allah yake so? (b) Mene ne ya taimaka wa Yusufu ya ɗauki matakin da ya dace a lokacin da matar Fotifar ta yi ƙoƙari ta rinjaye shi? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

8 Waɗanne labaran Littafi Mai Tsarki  ne suka nuna muhimmancin kame kanmu? Babu shakka, za ka iya tuna mutane da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka kame kansu a lokacin da aka jaraba su. Yusufu ɗan Yakubu ɗaya ne a cikinsu. Ya kame kansa a lokacin da yake bauta a gidan Fotifar, shugaban masu gadin Fir’auna. Matar Fotifar ta soma sha’awar Yusufu don shi “kyakyawa ne, murzaje kuma,” sai ta yi ƙoƙari ta rinjaye shi. Mene ne ya hana Yusufu faɗawa cikin tarkonta? Hakika, ya keɓe lokaci don ya yi la’akari da abin da zai faru idan ya yi lalata da ita. Ƙari ga haka, ya gudu ya bar ta a lokacin da ta kama shi don ya kwana da ita ƙarfi da yaji. Ya yi tunani: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?”​—Far. 39:​6, 9; karanta Misalai 1:10.

9. Ta yaya za ka yi shiri don ka guji jarabobi?

9 Mene ne muka koya daga misalin Yusufu? Muna bukatar mu guji jarabar taka dokokin Allah. A dā, wasu da yanzu Shaidu ne sun yi ƙoƙari su daina yawan cin abinci da maye da shan taba sigari da ƙwaya da lalata da dai sauransu. Bayan sun yi baftisma, a wasu lokuta sukan yi fama da halinsu na dā. Saboda haka, idan aka masa maka ka taka wata dokar Jehobah, ka ƙarfafa kanka ta wajen yin tunani a kan mugun sakamakon da za ka fuskanta idan ba ka kame kanka ba. Ban da haka, ka yi ƙoƙari ka hangi yanayi da zai iya sa ka faɗa cikin jaraba kuma ka tsai da shawarar yadda za ka guje shi. (Zab. 26:​4, 5; Mis. 22:3) Idan kuma ka fuskanci irin wannan gwaji, ka roƙi Jehobah ya ba ka hikimar da za ta taimaka maka ka kame kanka kuma ka guje wa yanayin.

10, 11. (a) Waɗanne abubuwa ne matasa suke fuskanta a makaranta? (b) Mene ne zai taimaka wa matasa su guji matsin yin lalata?

10 Matasa da yawa a ƙungiyar Jehobah suna fuskantar irin jaraba da Yusufu ya fuskanta. Alal misali, abokan ajin Kim suna lalata sosai, kuma a kowane ƙarshen mako da suka yi lalata, sukan yi hirar abin da suka yi. Amma Kim ba ta irin wannan hirar. Da yake ba ta yin abin da sauran suke yi, takan ji kamar “ba mai sonta kuma ta kaɗaita.” Ƙari ga haka, tsararta sukan ɗauka cewa ita wawuya ce domin ba ta fita zance. Duk da haka, Kim ta san cewa matasa da yawa suna fuskantar jaraba sosai na yin jima’i. (2 Tim. 2:22) Abokan makarantarta sukan tambaye ta ko har ila ba ta taɓa kwana da namiji ba. Hakan yakan ba ta zarafin bayyana musu dalilin da ya sa ba ta yin lalata. Muna alfahari da matasa da suka ƙuduri aniyar guje wa matsin yin lalata, kuma Jehobah ma yana alfahari da su!

11 Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi a kan mutanen da ba sa kame kansu a batun lalata. Ya kuma nuna mana mugun sakamakon da ake samu ta yin hakan. Ya kamata duk wanda yake cikin irin yanayin da Kim ta fuskanta ya yi bimbini a kan wani saurayi marar wayo da aka yi maganarsa a littafin Misalai sura 7. Ƙari ga haka, ka yi tunanin abin da Amnon ya yi da kuma sakamakon halinsa. (2 Sam. 13:​1, 2, 10-15, 28-32) Iyaye suna iya taimaka wa yaransu su koyi kame kansu kuma su zama masu hikima a batun yin soyayya. Za su iya yin hakan ta wajen tattauna batun a lokacin da suke ibada ta iyali da kuma yin amfani da ayoyin da aka ambata.

12. (a) Ta yaya Yusufu ya kame kansa a lokacin da yake tare da ’yan’uwansa? (b) A waɗanne yanayi ne za mu kame kanmu?

12 Akwai kuma wani lokacin da Yusufu ya kafa mana misali a batun kame kai. Domin yana son ya san abin da yake cikin zuciyar ’yan’uwansa, Yusufu bai bayyana  musu ko wane ne shi ba sa’ad da suka zo sayan abinci a Masar. Kuma a lokacin da hakan ya dame shi sosai, sai ya je wani wuri ya yi kuka a ɓoye. (Far. 43:​30, 31; 45:1) Idan wani Kirista ko kuma abokinka ya yi wani abu da bai dace ba, ka kame kanka kamar Yusufu don hakan zai taimaka maka ka guji ɗaukan mataki da garaje. (Mis. 16:32; 17:27) Idan aka yi wa danginka yankan zumunci, kana bukatar ka kame kanka domin ka guji yin cuɗanya da shi. Hakan ba zai kasance maka da sauƙi ba, amma za mu yi farin ciki idan muka san cewa abin da muke yi ya jitu da misalin Allah da kuma shawarar da ya ba da.

13. Waɗanne darussa za mu iya koya daga labarin Sarki Dauda?

13 Littafi Mai Tsarki ya ba da misalin Sarki Dauda cewa mutum ne mai iko sosai amma bai kashe Saul da Shimei ba a lokacin da suka ɓata masa rai. (1 Sam. 26:​9-11; 2 Sam. 16:​5-10) Hakan ba ya nufin cewa Dauda ya kame kansa a kowane lokaci, kamar yadda muka ga daga zunubin da ya yi da Bath-sheba da matakin da ya ɗauka sa’ad da Nabal ya ƙi ba su abinci. (1 Sam. 25:​10-13; 2 Sam. 11:​2-4) Duk da haka, za mu koya darussa masu kyau daga Dauda. Na farko, ya kamata dattawa musamman su mai da hankali su riƙa kame kansu don kada su yi amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba. Na biyu, bai kamata kowannenmu ya saki jiki yana ganin cewa ba zai fuskanci jaraba ba.​—1 Kor. 10:12.

ABUBUWAN DA ZA KA IYA YI

14. Ka faɗi abin da ya faru da wani ɗan’uwa, kuma me ya sa halinmu yake da muhimmanci idan muna cikin irin wannan yanayin?

14 Mene ne za ka yi don ka riƙa kame kanka? Ga wani misali, wani direba ya bugi motar Luigi ta baya. Duk da cewa direban ne yake da laifi, sai ya soma zagin Luigi kuma yana so su soma fada. Amma Luigi ya yi addu’a cewa Jehobah ya taimaka masa ya kame kansa, kuma ya yi ƙoƙari ya sa ɗayan direban ya yi shuru amma ya ƙi. Sai Luigi ya ɗauki lambar motar kuma ya tafi, amma direban yana ta zage-zage. Bayan mako ɗaya, Luigi ya koma ziyara a gidan wata mata kuma ya ga cewa wannan direban ne mijinta. Mutumin ya ji kunya sosai kuma ya nemi gafara don abin da ya yi. Sai direban ya ba da kuɗi don a gyara motar ɗan’uwan. Ƙari ga haka, mutumin ya zauna suka yi nazarin tare kuma ya ji daɗin abin da suka tattauna. Wannan abin da ya faru da Luigi ya sa ya fahimci cewa kame kai yana da muhimmanci. Da bai yi hakan ba, da yanayin zai yi muni sosai.​—Karanta 2 Korintiyawa 6:​3, 4.

Kame kanmu ko rashin yin hakan zai iya shafan hidimarmu (Ka duba sakin layi na 14)

15, 16. Ta yaya yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka da iyalinku ku riƙa kame kanku?

15 Yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai zai iya taimaka wa Kiristoci su riƙa kame kansu. Allah ya gaya wa Joshua: “Wannan littafin shari’a ba za ya rabu da bakinka ba, amma za ka riƙa bincikensa dare da rana, domin ka kiyaye ka aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki: gama da hakanan za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara.” (Josh. 1:8) Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka riƙa kame kanka?

16 Kamar yadda muka ambata ɗazu, Nassosi suna ɗauke da misalai da suka nuna amfani da kuma sakamakon ɗaukan wasu matakai. Jehobah ya sa an rubuta waɗannan labaran don mu koyi wasu darussa. (Rom. 15:4) Saboda haka, yana da kyau mu riƙa karanta su da yin bimbini a kansu da kuma nazarinsu. Ka  yi ƙoƙari ka fahimci yadda kai da iyalinka za ku yi amfani da su. Ka gaya wa Jehobah ya taimaka maka ka bi gargaɗin da ke cikin Kalmarsa. Idan ka ga cewa kana bukatar ka ƙara kame kanka, ka yi hakan. Ƙari ga haka, ka yi addu’a game da batun, kuma ka yi ƙoƙari ka kyautata halinka. (Yaƙ. 1:5) Hakika, yin bincike a littattafanmu zai taimaka maka ka ga bayanai da za su ƙara taimaka maka.

17. A waɗanne hanyoyi ne iyaye za su taimaka ma yaransu su riƙa kame kansu?

17 Ta yaya za ka taimaka ma yaranka su riƙa kame kansu? Iyaye sun san cewa yara suna bukatar su koyi yadda za su riƙa kame kansu. Kamar yadda yake da sauran halayen, ya kamata iyaye su kafa wa yaransu misali wajen kame kansu. (Afis. 6:4) Saboda haka, idan ka ga cewa yana yi wa yaranka wuya su kame kansu, ka tambayi kanka ko kana kafa musu misali mai kyau. Ka riƙa fita wa’azi da halartan taro da kuma yin ibada ta iyali a kai a kai, don yin waɗannan abubuwan za su taimaka musu sosai. Ban da haka ma, ba kome ba ne da yaranka suka roƙa za ka ba su! Don ba kome ba ne Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u, kuma ya yi hakan don su riƙa daraja ikonsa. Hakazalika, idan iyaye suna koyar da yaransu da kuma kafa musu misali mai kyau, yaran za su ko yi yadda za su riƙa kame kansu. Yana da muhimmanci sosai ka koya wa yaranka su riƙa daraja ikon Allah da kuma ƙa’idodinsa.​—Karanta Misalai 1:​5, 7, 8.

18. Me ya sa kake da tabbaci cewa abokan kirki za su sa ka samu albarka?

18 Hakika, ya kamata dukanmu mu zaɓi abokan kirki. Ka yi abota da waɗanda za su ƙarfafa ka ka zaɓi makasudai masu kyau kuma hakan zai sa ka guji faɗawa cikin matsala. (Mis. 13:20) Abokai da suke son bin ƙa’idodin Jehobah za su taimaka maka sosai, su sa ka yi koyi da halinsu na kame kai. Kuma halinka mai kyau zai ƙarfafa abokanka. Idan ka kame kanka, za ka riƙa jin daɗin rayuwa kuma ka faranta wa Jehobah rai har wasu su amfana.