Me ya sa Yesu ya hana yin rantsuwa?

BISA ga dokar da aka ba da ta hannun Musa, akwai wasu lokuta da Yahudawa za su iya yin rantsuwa. Amma a zamanin Yesu, yin rantsuwa ya zama gama gari, mutane suna yin rantsuwa a kome da suka faɗa. Kuma suna yin hakan ne don mutane su yarda da abin da suka faɗa. Amma Yesu ya yi musu kashedi sau biyu cewa hakan bai dace ba. Maimakon yin rantsuwa Yesu ya ce: “Bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a.”​—Mat. 5:​33-37; 23:​16-22.

Wani ƙamus mai suna Theological Dictionary of the New Testament ya ce littafin Talmud zai iya taimaka mana mu ga yadda Yahudawa suke yin rantsuwa a duk abin da suke faɗa. Abin da ya sa za mu iya fahimtar hakan shi ne don littafin Talmud ya bayyana dalla-dalla irin alkawarin da za a iya cika idan an yi rantsuwa a kansu da kuma wanda ba za a iya cikawa ba.

Ba Yesu kaɗai ba ne ya ce irin wannan rantsuwa ba ta dace ba. Alal misali, ɗan tarihin Yahudawa mai suna Flavius Josephus ya rubuta cewa akwai wata ƙungiyar Yahudawa da ba su amince da yin rantsuwa ba, don haka ba sa yi. Membobin wannan ƙungiyar sun yi imani cewa yin rantsuwa ya fi muni da yin ƙarya. A ganinsu idan mutum ya yi rantsuwa don wasu su yarda da abin da yake faɗa, to mutumin tamkar maƙaryaci ne. Ban da haka ma, littafin Sirak ko kuma Ecclesiasticus, (23:11) ya ce: “Duk mai yin rantsuwa a kai a kai yana ƙara wa kansa nauyi.” Kuma Yesu ma ya haramta yin rantsuwa a kan abubuwan da ba su da muhimmanci. Idan a kowane lokaci muna faɗin gaskiya ba ma bukatar mu riƙa rantsuwa don mutane su yarda da abin da muke faɗa.