MAHAIFIN John ya yi baftisma a wani ƙaramin gari mai suna Gujarat da ke Indiya shekara 60 da suka shige. John da mahaifiyarsa da kuma ’yan’uwansa maza da mata guda biyar masu ƙwazo ne a cocin Katolika. Kuma don haka, sun tsananta wa mahaifinsu don ya ƙi ya bi addininsu.

Wata rana, mahaifin John ya tura shi ya kai ma wani abokinsa a ikilisiyarsu wasiƙa. Amma kafin John ya kai wannan saƙon, ya ji ciwo sosai a yatsarsa da safen a lokacin da yake buɗe wani babban durum. Da yake yana so ya kai wannan saƙon da mahaifinsa ya ba shi, sai John ya ɗaure yatsarsa da tsumma kuma ya kai wasiƙar.

Da John ya isa gidan da zai ba da wasiƙar, matar mutumin kawai ya samu, kuma su Shaidu ne. Sa’ad da matar ta karɓi wasiƙar, sai ta lura cewa John ya ji rauni a yatsarsa, kuma ta so ta taimaka masa. Sai ta fito da akwatin magani, ta wanke ciwon ta saka magani ta ɗaure yatsar da bandeji kuma tana masa wa’azi. Ban da haka ma, ta ba shi shayi ya sha kuma suka ci gaba da hira game da Littafi Mai Tsarki.

Saboda alherin da ta yi masa, sai John ya soma son Shaidun Jehobah. Kuma ya yi mata tambayoyi guda biyu game ga imanin Shaidun Jehobah da suka bambanta da na cocin Katolika. Wato ya so ya san ko Yesu shi ne Allah da kuma ko wajibi ne Kiristoci su yi addu’a ga Maryamu. Da yake matar ta iya yarensu John wato Gujarati, sai ta nuna masa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batun kuma ta ba shi ƙasidar nan “This Good News of the Kingdom.”

Da John ya karanta ƙasidar, ya fahimci cewa abin da yake karantawa gaskiya ne. Sai ya je wurin firist ɗin su kuma ya yi masa tambayoyi guda biyun. Firist ɗin ya ji haushi sosai kuma ya hasala ya jefe shi da Littafi Mai Tsarki, ya ce: “Ka zama Shaiɗani! Ka nuna mini inda Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ba Allah ba ne. Kuma ka nuna mini inda ya ce kada mu bauta wa Maryamu. Ka nuna min in gani!” Abin da firist ɗin ya yi ya ba wa John mamaki sosai kuma ya ce masa, “Ba zan sake zuwa cocin Katolika ba.” Kuma bai ƙara yin hakan ba!

Bayan haka, sai John ya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu kuma ya soma bauta wa Jehobah. Ban da haka ma, mutane da yawa a iyalinsu ma sun soma bauta wa Jehobah. Bayan shekara 60, har yanzu John yana da taɓo don rauni da ya ji a yatsarsa. Kuma yana tunawa da irin alherin da aka nuna masa da ya sa ya soma bauta wa Jehobah.​—2 Kor. 6:​4, 6.