“Kada ku daina yi wa baƙi alheri.”​—IBRAN. 13:​2, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 124, 79

1, 2. (a) Waɗanne ƙalubale ne baƙi da yawa suke fuskanta a yau? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Mene ne manzo Bulus ya tuna wa Kiristoci, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

SHEKARU 30 da suka shige, Osei [1] da ba Mashaidi ba ne a lokacin ya bar ƙasar Gana kuma ya tafi Turai. Ya ce: “Na lura cewa yawancin mutanen ƙasar ba su damu da ni ba. Ana sanyi sosai a wurin kuma ni ban saba da irin wannan sanyin ba. Na ji sanyin da ban taɓa ji a rayuwata ba sa’ad da na bar tashar jirgin sama kuma hakan ya sa na soma kuka.” Osei bai iya yaren ba. Don haka, ya yi fiye da shekara ɗaya yana neman aiki. Da yake ya yi nesa da ‘yan gidansu, hakan ya sa ya kaɗaita kuma ya soma kewar gida.

2 Idan ka sami kanka a irin wannan yanayin, yaya za ka so mutane su bi da kai? Duk da cewa ƙasarku ba ɗaya ba ce ko kuma launin fatarku ta bambanta, za ka yi farin ciki idan ‘yan’uwa suka marabce ka sosai sa’ad da ka je Majami’ar Mulki. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya umurci  Kiristoci cewa, ‘Kada su daina yi wa baƙi alheri.’ (Ibran. 13:​2, LMT) Saboda haka, bari mu tattauna waɗannan tambayoyin: Ta yaya Jehobah yake ɗaukan baƙi? Me ya sa muke bukatar mu canja ra’ayinmu game da baƙi? Sa’ad da waɗanda suka fito daga wata ƙasa suka zo gidanmu ko kuma ikilisiyarmu, ta yaya za mu iya taimaka musu su saki jiki?

YADDA JEHOBAH YAKE ƊAUKAN BAƘI

3, 4. Bisa ga abin da ke cikin littafin Fitowa 23:​9, yaya Allah yake so Isra’ilawa su riƙa bi da baƙi, kuma me ya sa?

3 Bayan Jehobah ya ceci mutanensa daga ƙasar Masar, ya ba su dokoki game da yadda za su riƙa bi da baƙin da suka bi su. (Fit. 12:​38, 49; 22:21) Jehobah ya tanadar wa baƙi abin da suke bukata duk da cewa su talakawa ne domin yana ƙaunarsu. Ɗaya daga cikin wannan tanadin shi ne za su iya yin kalar amfanin gona.​—⁠Lev. 19:​9, 10.

4 Maimakon Jehobah ya umurci Isra’ilawa su riƙa daraja baƙi kawai, ya gaya musu cewa su ji tausayin su. (Karanta Fitowa 23:⁠9.) Don sun taɓa zama baƙi, su san wahalar da ke tattare da hakan. Wataƙila kafin su zama bayi, mutanen Masar suna ƙin su don suna ganin cewa Isra’ilawan sun bambanta da su a launin fata ko kuma a addini. (Far. 43:32; 46:34; Fit. 1:​11-14) Isra’ilawa sun sha wahala sosai sa’ad da suke zaman baƙonci a ƙasar Masar. Duk da haka, Jehobah yana so su bi da baƙin da suke tare da su ‘kamar ɗan da aka haifa a wurinsu.’​—⁠Lev. 19:​33, 34.

5. Mene ne zai taimaka mana mu bi da baƙi yadda Jehobah yake so?

5 Har a yau muna da tabbaci cewa Jehobah ya damu da mutanen da suka fito daga wata ƙasa da suke halartan taro a ikilisiyarmu. (K. Sha. 10:​17-19; Mal. 3:​5, 6) Idan muka yi tunani game da ƙalubalen da suke fuskanta kamar bambancin da mutane suke nuna musu ko kuma rashin iya yaren ƙasar, hakan zai sa mu bi da su yadda yakamata kuma mu yi musu alheri.​—⁠1 Bit. 3:⁠8.

SHIN MUNA BUKATAR MU CANJA RA’AYINMU GAME DA BAƘI?

6, 7. Mene ne ya nuna cewa Kiristoci a ƙarni na farko sun koyi ƙin nuna bambanci a tsakaninsu?

6 Kiristoci a ƙarni na farko sun yi ƙoƙari wajen ƙin yin koyi da halin nuna bambanci da Yahudawa suke yi. A ranar Fentakos ta shekara ta 33, waɗanda suke zama a Urushalima sun nuna karimci ga mutanen da suka zama Kiristoci da suka zo daga ƙasashe dabam-dabam. (A. M. 2:​5, 44-47) Hakan ya nuna cewa waɗannan Kiristocin sun fahimci ma’anar furucin nan “karimci,” wato “yi wa baƙi alheri.”

7 Yayin da ikilisiyar take samun ci gaba, ‘yan’uwan sun soma samun matsala a tsakaninsu. Yahudawan da ke yaren Girka sun yi gunaguni cewa ba a kula da gwaurayensu. (A. M. 6:⁠1) Don su magance wannan matsalar, manzannin sun naɗa maza guda bakwai don su tabbatar cewa an biya bukatun kowa. Manzannin sun zaɓi mazan da suke da sunan Helenanci, wataƙila don su sa gwaurayen su saki jiki.​—⁠A. M. 6:​2-6.

8, 9. (a) Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu san ko muna nuna bambanci? (b) Mene ne ya wajaba mu daina yi? (1 Bit. 1:⁠22)

8 Gaskiyar ita ce, al’adarmu tana shafan mu sosai. (Rom. 12:⁠2) Wataƙila mun taɓa jin maƙwabtanmu ko abokan aikinmu ko ‘yan makarantarmu suna baƙar magana game da al’ada ko yaren ko kuma launin fatar wasu. Shin muna  barin waɗannan maganganun su shafi ra’ayinmu game da waɗanda suka fito daga wata ƙasa? Idan wani ya zagi ƙasarmu ko kuma al’adarmu fa? Ya ya za mu bi da batun?

9 Akwai lokacin da manzo Bitrus yake nuna wa waɗanda ba Yahudawa ba bambanci. Amma da shigewar lokaci, ya daina kasancewa da irin wannan halin. (A. M. 10:​28, 34, 35; Gal. 2:​11-14) Hakazalika, idan muka ga cewa muna nuna bambanci, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daina yin hakan. (Karanta 1 Bitrus 1:22.) Ko da daga wacce ƙasa ce muka fito, ya kamata mu tuna cewa mu ajizai ne kuma ba mu cancanci samun ceto ba. (Rom. 3:​9, 10, 21-24) Don haka, bai kamata mu riƙa ganin kamar mun fi wasu ba. (1 Kor. 4:⁠7) Muna bukatar mu kasance da irin ra’ayin manzo Bulus wanda ya gargaɗi ‘yan’uwansa shafaffu cewa, su “ba baƙi ba ne, . . . amma . . . na cikin iyalin Allah.” (Afis. 2:19) Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu daina nuna bambanci, hakan zai taimaka mana mu kasance da sabon hali.​—⁠Kol. 3:​10, 11.

YADDA ZA MU YI WA BAƘI ALHERI

10, 11. Ta yaya yadda Boaz ya bi da Ruth ya nuna yadda Jehobah yake ji game da baƙi?

10 Yadda Boaz ya bi da Ruth ‘yar Moab ya nuna yadda Jehobah yake ji game da baƙi. Sa’ad da Boaz ya zo don ya duba masu yi masa aiki a gona, ya lura da wata baƙuwa da take bin bayan masu girbi tana kala. Ko da yake tana da ‘yancin yin kala, ta nemi izini kafin ta yi hakan. Sa’ad da Boaz ya ji hakan, sai ya ƙyale ta ta yi kala a cikin dami-damin hatsin da aka girbe.​—⁠Karanta Ruth 2:​5-7, 15, 16.

11 Abin da ya faru daga baya ya nuna cewa Boaz ya damu da Ruth da kuma yanayin da take ciki a matsayinta na baƙuwa. Ya gaya mata ta kasance tare da sauran matan da ke gonarsa don kada mazan da suke yi masa girbi su wulakanta ta. Boaz ya tabbata cewa ta sami isashen abinci da kuma ruwa kamar na masu yi masa aiki. Ƙari ga haka, ya daraja wannan baƙuwar kuma ya ƙarfafa ta.​—⁠Ruth 2:​8-10, 13, 14.

12. Ta yaya nuna alheri zai shafi waɗanda suka zo daga wata ƙasa?

12 Ban da ƙaunar da Ruth ta nuna wa surkuwarta Naomi, abin da ya ƙara burge Boaz shi ne cewa ta soma bauta wa Jehobah. Boaz ya yi koyi da Jehobah ta wajen yi wa Ruth wadda ta zo ‘neman mafaka ƙarƙashin fukafukan Allah na Isra’ila’ alheri. (Ruth 2:​12, 20; Mis. 19:17) Hakazalika a yau, idan muna yi wa mutane alheri, hakan zai taimaka wa “dukan mutane” su koyi gaskiya kuma su ga cewa Jehobah yana ƙaunar su sosai.​—⁠1 Tim. 2:​3, 4.

Muna gaishe da sababbi sa’ad da suka halarci taro a Majami’ar Mulki? (Ka duba sakin layi na 13, 14)

13, 14. (a) Me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta wajen gai da baƙin da suka halarci taro a Majami’ar Mulki? (b) Mene ne zai taimaka maka ka ji daɗin tattaunawa da waɗanda suka fito daga wata ƙasa?

13 Sa’ad da waɗanda suka fito daga wata ƙasa suka halarci taro a Majami’ar Mulki, ya kamata mu gaishe su sosai. Ta hakan muna yi musu alheri. A yawancin lokaci, waɗannan baƙi suna jin kunya kuma suna zama su kaɗai. Wataƙila don yadda aka rene su ko kuma al’adarsu, suna iya ganin kamar wasu mutane daga wata ƙasa sun fi su. Don haka, ya kamata mu riƙa gai da su kuma mu nuna cewa mun damu da su. Idan kuna da JW Language app a naku yaren, kuna iya amfani da shi don ku koya yadda ake gaisuwa a yarensu.​—⁠Karanta Filibiyawa 2:​3, 4.

 14 Wataƙila ba ka jin daɗin yin magana da waɗanda suka fito daga wata ƙasa. Don ka daina ji hakan, kana iya gaya musu wani abu game da kanka. Kafin ka sani, za ka lura cewa babu wani bambanci tsakaninku. Ka riƙa tunawa cewa kowace al’ada tana da inda ta kasa da kuma inda ta yi fice.

KU TAIMAKA MUSU SU SAKI JIKI

15. Mene ne zai taimaka mana mu fahimci waɗanda ba su saba da al’adar wata ƙasa ba?

15 Don ka taimaka wa wasu su saki jiki a cikin ikilisiya, ka yi wa kanka wannan tambayar, ‘Idan na je wata ƙasa, yaya zan so mutanen wurin su bi da ni?’ (Mat. 7:12) Ku yi haƙuri da baƙi don ba su saba da ƙasar ba. Da farko ba za mu iya fahimtar yadda suke ji da kuma dalilin da ya sa suke yin wasu abubuwa ba. Amma maimakon mu yi tunani cewa ya kamata su bi al’adarmu, zai dace mu amince da su yadda suke.​—⁠Karanta Romawa 15:⁠7.

16, 17. (a) Mene ne za mu yi don mu kusaci waɗanda al’adarsu dabam ne da namu? (b) Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu taimaka wa baƙin da suke ikilisiyarmu?

16 Idan muka san al’adar ƙasar wasu, hakan zai taimaka mana mu riƙa tattaunawa da su cikin kwanciyar hankali. Za mu iya keɓe lokaci sa’ad da muke ibada ta iyali don mu yi bincike game da ƙasar mutanen da ba mu saba da su ba a cikin ikilisiya ko kuma a yankinmu. Wata hanya kuma da za mu iya kusantar baƙin da suka zo ƙasarmu ita ce ta wurin gayyatar su gidanmu. Tun da Jehobah “ya buɗe kofar bangaskiya ga al’ummai,” ya kamata mu ma mu riƙa marabtar baƙi “waɗanda suke ‘yan’uwanmu cikin Almasihu.” ​—⁠A. M. 14:27; Gal. 6:​10, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana; Ayu. 31:⁠32.

Muna gayyatar waɗanda suka zo daga wata ƙasa gidanmu kuwa? (Ka duba sakin layi na 16, 17)

17 Idan muka ba da lokacinmu wajen tattaunawa da waɗanda suka fito daga wata ƙasa, za mu fahimci ƙoƙarin da  suke yi don su saba da al’adar ƙasarmu. Za mu ga cewa suna bukatar taimako don su iya yaren. Ƙari ga haka, za mu iya haɗa su da waɗanda za su taimaka musu su sami masauki ko kuma aiki. Yin irin waɗannan abubuwan zai taimaka wa ‘yan’uwanmu sosai.​—⁠Mis. 3:⁠27.

18. Wane misali mai kyau ne baƙi za su iya yin koyi da shi a yau?

18 Hakika, waɗanda suka zo wata ƙasa suna so su yi iya ƙoƙarinsu don su saba da al’adar ƙasar. Ruth ta kafa misali mai kyau game da hakan. Da farko, ta daraja al’adar ƙasar ta wajen neman izini kafin ta yi kala. (Ruth 2:⁠7) Duk da cewa tana da ‘yancin yin kala, ba ta ɗauka cewa abin da mutane ya kamata su yi mata ba ke nan. Na biyu, ta yi godiya don alherin da aka nuna mata. (Ruth 2:13) Idan baƙi suka nuna irin wannan halin, mutanen ƙasar da kuma ‘yan’uwa a cikin ikilisiya za su daraja su sosai.

19. Mene ne dalilin da ya sa ya kamata mu marabci baƙin da suka zo ƙasarmu?

19 Abin farin ciki ne cewa Jehobah ya ba wa mutane daga ƙasashe dabam-dabam damar jin wa’azi game da Mulkinsa. Wataƙila waɗannan baƙin ba su sami damar yin nazarin Littafi Mai Tsarki ko kuma tarayya da Shaidun Jehobah ba a ƙasarsu. Amma yanzu da suka soma tarayya da mu, ya kamata mu taimaka musu su saki jiki. Ko da ba mu da kuɗi ko kuma ba za mu iya taimaka musu a kowane yanayi ba, muna yin koyi da Jehobah sa’ad da muka yi musu alheri. A matsayinmu na “masu-koyi da Allah,” bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu marabci baƙin da suka zo ƙasarmu.​—⁠Afis. 5:​1, 2.

^ [1] (sakin layi na 1) An canja sunan.