“Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinku.”​—ROM. 12:2.

WAƘOƘI: 88, 45

1, 2. (a) Wace amsa ce Yesu ya ba Bitrus? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me ya sa Yesu ya ba da wannan amsar?

ABUBUWAN da mabiyan Yesu suka ji ya ba su mamaki sosai. Suna tunanin cewa Yesu zai mayar wa Isra’ilawa mulki, amma ya gaya musu cewa nan ba da daɗewa ba, zai sha wahala kuma ya mutu. Manzo Bitrus ya ce masa: “Allah ya sawwaƙe, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba.” Sai Yesu ya ce masa: “Ka rabu da ni, kai Shaiɗan! Kai mai sa tuntuɓe ne a gare ni, gama kana tunani kamar mutum ne, ba kamar Allah ba.”​—Mat. 16:​21-23; A. M. 1:6.

2 Abin da Yesu ya ce ya nuna mana bambancin da ke tsakanin bin ra’ayin Allah da kuma bin ra’ayin duniyar da Shaiɗan yake mulkinta. (1 Yoh. 5:19) Bitrus ya ƙarfafa Yesu ya kasance da irin halin son kai da mutanen duniya ke da shi. Amma Yesu ya nuna cewa ra’ayin Jehobah ya bambanta da na duniya. Ya san cewa Allah yana so ya kasance a shirye don wahalar da zai sha, ya kuma mutu. Ta amsar da Yesu ya ba Bitrus, ya nuna cewa ra’ayin Jehobah shi ne ya fi kyau.

3. Me ya sa yake da wuya mu kasance da ra’ayin Jehobah kuma mu guji bin ra’ayin mutanen duniya?

 3 Mu kuma fa? Shin muna bin ra’ayin Allah ne ko kuma ra’ayin mutanen duniya? Babu shakka a matsayinmu na Kiristoci, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu riƙa bin ra’ayin Allah. Amma tunaninmu ya jitu da na Jehobah kuwa? Muna bukatar mu saka ƙwazo don mu kasance da irin ra’ayin Jehobah, amma ba ma bukatar yin ƙwazo don kasancewa da ra’ayin mutanen duniya. Me ya sa? Domin ruhun nan da yake zuga zuciyar mutane na ko’ina. (Afis. 2:2) Ƙari ga haka, mutanen duniya suna ƙarfafa mu mu zama masu son kai, hakan yana iya sa mu kasance da ra’ayinsu. Hakika yana da wuya mu kasance da irin ra’ayin Jehobah, amma yana da sauƙi mu bi ra’ayin mutanen duniya.

4. (a) Mene ne zai faru idan muka bar duniyar Shaiɗan ta sarrafa tunaninmu? (b) Ta yaya wannan talifin zai taimaka mana?

4 Idan muka soma bin ra’ayin mutanen duniya, za mu zama masu son kai da kuma son samun ’yanci. (Mar. 7:​21, 22) Saboda haka, yana da muhimmanci mu kasance da ra’ayin Allah ba na mutanen duniya ba. Wannan talifin zai taimaka mana mu yi hakan. Za mu tattauna dalilan da suka sa muke bukatar mu riƙa bi da batutuwa yadda Jehobah yake yi. Za mu koyi abin da ya sa yin hakan ba taƙura ba ne, amma don amfaninmu ne. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu guji bin ra’ayin mutanen duniya. A talifi na gaba kuma, za mu tattauna yadda za mu kasance da ra’ayin Jehobah a wasu batutuwa.

RA’AYIN JEHOBAH YANA AMFANAR MU

5. Me ya sa wasu mutane ba sa son kowa ya gaya musu abin da za su yi?

5 Wasu mutane ba sa so kowa ya riƙa sarrafa tunaninsu. Suna iya cewa “Ni ke cin gashin kaina.” Wataƙila abin da suke nufi shi ne cewa su ne suke yi wa kansu zaɓi kuma ya dace su yi hakan. Ba sa son wasu su riƙa gaya musu abin da za su yi ko kuma a tilasta musu su yi koyi da wasu mutane. *

6. (a) Wane irin ’yanci ne Jehobah ya ba mu? (b) Shin wannan ’yanci yana da iyaka?

6 Kasancewa da ra’ayin Jehobah ba ya nufin cewa ba za mu riƙa yi wa kanmu zaɓi ba. Littafin 2 Korintiyawa 3:17 ta ce: “A inda Ruhun Ubangiji yake kuwa a nan ’yanci yake.” Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓan yadda muke so halinmu ya kasance. Muna iya yin abubuwan da muke so da kuma irin aikin da muke so. Hakika, yadda Jehobah ya halicce mu ke nan. Amma hakan ba ya nufin cewa ’yancinmu ba shi da iyaka. (Karanta 1 Bitrus 2:16.) Idan ya zo ga batun zaɓan abu mai kyau da marar kyau, Jehobah yana so mu yi amfani da Kalmarsa don yin zaɓin da ya dace. Shin hakan taƙura ne ko kuma don amfanin kanmu?

7, 8. Me ya sa kasancewa da irin ra’ayin Jehobah ba taƙura ba ne? Ka ba da misali.

7 Ku yi la’akari da wannan misalin. Iyaye suna iya ƙoƙarinsu don su koya wa yaransu halaye masu kyau. Suna iya koya musu yadda za su riƙa faɗin gaskiya da yin ƙwazo a aiki da kuma sanin yakamata. Hakan ba taƙura ba ne, amma iyayen suna koya wa yara yadda za su yi nasara a rayuwa ne sa’ad da suka girma. A lokacin da yaran suka bar gida, su za su riƙa yi wa kansu zaɓi. Idan suka bi  abubuwan da iyayensu suka koya musu, za su riƙa yanke shawarwarin da ba za su yi da-na-sani ba. A maimakon haka, za su tsai da wa kansu shawarwari masu kyau kuma hakan zai taimaka masu su guji matsaloli.

8 Jehobah yana son mu yi rayuwa mai gamsarwa, kamar yadda iyaye nagari ke so. (Isha. 48:​17, 18) Saboda haka, ya koya mana ɗabi’a mai kyau da kuma yadda za mu riƙa sha’ani da mutane. Yana son mu kasance da irin ra’ayinsa kuma mu riƙa yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. Wannan ba taƙura ba ne. Amma, yana taimaka mana ne mu kasance da ra’ayin da ya dace. (Zab. 92:5; K. Mag. 2:​1-5; Isha. 55:9) Idan muka yi hakan, za mu riƙa yin abubuwan da muke so kuma mu riƙa yin zaɓin da zai sa mu farin ciki. (Zab. 1:​2, 3) Hakika, kasancewa da irin ra’ayin Jehobah zai amfane mu sosai!

RA’AYIN JEHOBAH YA FI KYAU

9, 10. Mene ne ya nuna cewa ra’ayin Jehobah ya fi na mutanen duniya kyau?

9 Ga wani dalili kuma da ya sa bayin Jehobah suke son kasancewa da irin ra’ayinsa. Ra’ayin Jehobah ya fi na mutanen duniya kyau. Mutanen duniya na iya ba da shawara game da halin da ya dace da yadda iyalai za su zauna lafiya. Ƙari ga haka, za su iya ba da shawara a kan yadda mutum zai yi nasara a aikinsa da dai sauransu. Amma da yawa daga cikin shawarwarin ba su jitu da ra’ayin Jehobah ba. Alal misali, suna yawan ƙarfafa mutane su zama masu son kai, kuma su riƙa yin lalata. Ƙari ga haka, a wasu lokuta suna ƙarfafa ma’aurata su rabu da juna ko kuma su kashe aurensu saboda dalilin da bai taka-karya-ya-ƙarya ba. Suna ganin cewa yin hakan zai sa su farin ciki. Irin waɗannan shawarwarin sun saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki. Waɗanne shawarwari ne za su amfane mu a yau, na mutanen duniya ne ko na Allah?

10 Yesu ya ce: “Ana gane hikimar Allah a ayyukanta.” (Mat. 11:19) Duk da cewa ana samun ci gaba sosai don yin amfani da na’urori, hakan bai magance matsalar da ke hana mutane farin ciki ba, kamar yaƙi da nuna bambanci da mugunta. Ƙari ga haka, mutanen duniya suna ganin yin lalata ya dace. Mutane da yawa sun yarda cewa waɗannan abubuwa suna ɓata iyali da jawo cututtuka iri-iri da kuma wasu matsaloli. Kiristocin da suke bin ra’ayin Jehobah suna farin ciki, suna da ƙoshin lafiya kuma suna zaman lafiya da ’yan’uwansu a faɗin duniya. (Isha. 2:4; A. M. 10:​34, 35; 1 Kor. 6:​9-11) Hakan ya nuna mana cewa ra’ayin Jehobah ya fi ra’ayin mutanen duniya kyau.

11. Ra’ayin wane ne Musa ya bi, kuma wane sakamako hakan ya kawo?

11 Bayin Jehobah a zamanin dā sun san cewa ra’ayinsa ne ya fi kyau. Alal misali, duk da cewa an “koya wa Musa dukan hikimar Masarawa,” ya roƙi Jehobah ya sa ‘zuciyarsa ta sami hikima.’ (A. M. 7:22; Zab. 90:12) Ban da haka ma, Musa ya roƙi Jehobah, ya ce: “Ka nuna mini hanyoyinka.” (Fit. 33:13) Da yake Musa ya yarda Jehobah ya sarrafa tunaninsa, Jehobah ya yi amfani da shi don ya cika nufinsa. Ƙari ga haka, ya daraja Musa ta wajen ambata sunansa a Littafi Mai Tsarki a matsayin mutum mai bangaskiya sosai.​—Ibran. 11:​24-27.

12. Wane ra’ayi ne Bulus ya bi don ya tsai da shawara mai kyau?

12 Manzo Bulus mutum ne mai ilimi sosai, kuma ya iya Ibrananci da Helenanci. (A. M. 5:34; 21:​37, 39; 22:​2, 3) Duk da haka sa’ad da ya zo ga batun yin zaɓi, ya guji bin ra’ayin mutanen duniya. A maimakon  haka, ya yi zaɓin da ya jitu da ƙa’idodin Allah. (Karanta Ayyukan Manzanni 17:2; 1 Korintiyawa 2:​6, 7, 13.) A sakamakon haka, ya yi nasara sosai a wa’azinsa kuma yana ɗokin samun ladan da zai dawwama.​—2 Tim. 4:8.

13. Wane ne yake da hakkin sa mu kasance da irin ra’ayin Jehobah?

13 Babu shakka, ra’ayin Jehobah ya fi na mutanen duniya kyau. Bin ƙa’idodinsa zai sa mu yi farin ciki kuma mu yi nasara. Amma Jehobah ba zai tilasta mana mu bi ra’ayinsa ba. “Bawan nan mai aminci, mai hikima” da kuma dattawa ba sa sarrafa tunaninmu. (Mat. 24:45; 2 Kor. 1:24) A maimakon haka, kowane Kirista ne yake da hakkin kasancewa da irin ra’ayin Allah. Ta yaya za mu yi hakan?

KADA KA YARDA DUNIYAR NAN TA RINJAYE KA

14, 15. (a) Me ya kamata mu riƙa yin tunani a kai don mu kasance da irin ra’ayin Jehobah? (b) Me ya sa muke bukatar mu guji tunanin mutanen duniya? Ka ba da misali.

14 Romawa 12:2 ta ce: “Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinku, amma ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.” Wannan ayar ta nuna mana cewa ko da mene ne yake sarrafa tunaninmu kafin mu soma bauta wa Jehobah, muna iya canja ra’ayinmu kuma mu kasance da ra’ayin da ya jitu da na Allah. Halayen da muka gāda daga iyayenmu da kuma abubuwan da muka shaida a rayuwa suna iya shafan tunaninmu. Duk da haka, muna iya canja ra’ayinmu. Irin wannan canjin ya dangana ga abubuwan da muke tunani a kansu. Idan muka yi tunani a kan ƙa’idodin Jehobah, za mu riƙa tabbatar wa kanmu cewa ra’ayin Jehobah ne ya dace. Ƙari ga haka, za mu so bin ra’ayinsa.

15 Idan muna so mu riƙa bin ra’ayin Jehobah muna bukatar mu ƙi barin ‘tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinmu.’ Mu guji yin tunanin da suka saɓa wa ƙa’idodin Allah. Muna iya kwatanta muhimmancin yin hakan da abinci. Mutumin da yake so ya kasance da ƙoshin lafiya yana bukatar ya riƙa cin lafiyayyen abinci. Amma ƙoƙarinsa zai zama a banza idan bai daina cin ruɓaɓɓen abinci ba. Hakazalika, ƙoƙarinmu na kasancewa da ra’ayin Jehobah zai zama a banza idan muna barin ra’ayin mutanen duniya ya riƙa sarrafa tunaninmu.

16. Daga mene ne muke bukatar mu kāre kanmu?

16 Za mu iya guje wa ra’ayin mutanen duniya gabaki ɗaya? A’a, domin ba za mu iya ficewa daga duniya ba. (1 Kor. 5:​9, 10) Sa’ad da muke wa’azi, muna haɗuwa da mutanen da imaninsu bai jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Duk da cewa ba za mu iya guje wa ra’ayin mutanen duniya gabaki ɗaya ba, ba ma bukatar mu riƙa tunani a kansu. Kamar Yesu, muna bukatar mu ƙi duk wani ra’ayin da bai dace ba da Shaiɗan yake so mu kasance da shi. Ƙari ga haka, muna bukatar mu guji abubuwan da za su iya sa mu kasance da ra’ayin da bai dace ba.​—Karanta Karin Magana 4:23.

17. A waɗanne hanyoyi ne muke bukatar mu guji tunanin mutanen duniya?

17 Alal misali, muna bukatar mu yi hattara da irin mutanen da muke abota da su. Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi cewa idan muna yin abokantaka da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah, za mu soma tunani yadda suke yi. (K. Mag. 13:20; 1 Kor. 15:​12, 32, 33) Ƙari ga haka,  muna bukatar mu mai da hankali ga irin nishaɗin ba muke yi. Idan muka guji fina-finan da ke ɗaukaka koyarwar juyin halitta da mugunta da kuma lalata, za mu iya guje wa ra’ayin da ya saɓa wa ƙa’idodin Allah.​—2 Kor. 10:5.

Kuna taimaka wa yaranku su guji yin nishaɗin da bai dace ba kuwa? (Ka duba sakin layi na 18, 19)

18, 19. (a) Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali musamman ga ra’ayin da ake so a cusa mana da wayo? (b) Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu yi wa kanmu, kuma me ya sa?

18 Muna bukatar mu san ra’ayin mutanen duniya da ake neman a cusa mana da wayo kuma mu guje su. Alal misali a labarai, ana iya ba da rahoto a hanyar da za ta ɗaukaka ra’ayin wasu ’yan siyasa. Wasu rahotannin kuma suna iya ɗaukaka ra’ayoyin da mutanen duniya ke so. Wasu fina-finai da littattafai suna ɗaukaka son kai kuma suna nuna wa mutane cewa hakan abu ne da ya dace. Irin wannan ra’ayin bai jitu da abin da ke Littafi Mai Tsarki ba. Domin Kalmar Allah ta ce iyalai za su yi farin ciki idan suna ƙaunar Jehobah fiye da kome. (Mat. 22:​36-39) Ƙari ga haka, wasu fina-finai da yara suke kallo da kuma littattafan suke karantawa na iya sa su soma tunanin cewa halin banza ba laifi ba ne.

19 Hakan bai haramta yin nishaɗin da ya dace ba. Muna bukatar mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Zan gane ra’ayin mutanen duniya ko da da wayo ake so a cusa mini shi? Ina kāre kaina da kuma yarana daga shirye-shiryen telibijin da kuma littattafan da ke ɗaukaka ra’ayin da bai dace ba? Ina taimaka wa yarana su kasance da ra’ayin Jehobah?’ Idan muka fahimci bambanci da ke tsakanin ra’ayin Jehobah da na mutanen duniya, hakan zai taimaka mana mu guji barin ‘tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinmu.’

WANE NE YAKE SARRAFA KA A YAU?

20. Yaya za mu sani ko waye ne yake sarrafa tunaninmu?

20 Muna bukatar mu tuna cewa a wurare biyu ne za mu iya samun bayanai, wato a wurin Jehobah ko kuma duniyar da Shaiɗan yake mulkinta. Wane ne yake sarrafa tunaninmu? Amsar ta dangana ga wurin da muke samun bayanai. Idan muka amince da ra’ayin mutanen duniya, ra’ayin ne zai riƙa sarrafa tunaninmu, kuma hakan zai sa mu soma yin tunani da kuma ayyukan da suke yi. Shi ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali ga irin abubuwan da muke tunani a kai da kallo da karantawa da kuma saurarawa.

21. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Kamar yadda aka ambata ɗazu, idan muna so mu kasance da irin ra’ayin Jehobah, ba guje wa ra’ayin mutanen duniya kawai muke bukatar mu yi ba. Muna bukatar mu riƙa yin bimbini a kan ra’ayoyin Jehobah don mu ma mu kasance da irin ra’ayinsa. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu yi hakan.

^ sakin layi na 5 Ra’ayin wasu yana shafan mutumin da yake ganin yana da ’yanci. A wace hanya ce ra’ayin wasu yake shafan mu? Hakan yana iya faruwa sa’ad da muke tunani game da yadda rayuwa ta soma, da kuma a lokacin da muke zaɓan tufafin da za mu saka. Amma muna iya zaɓan ra’ayin wanda za mu riƙa bi.