Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ta Yaya Za Ka Saba da Sabuwar Ikilisiyar da Ka Je?

Ta Yaya Za Ka Saba da Sabuwar Ikilisiyar da Ka Je?

ALLEN * ya ce: “Na jin tsoron ƙaurowa zuwa wannan ikilisiyar don ban san ko zan sami abokai ko kuma ’yan’uwan za su amince da ni ba.” Allen yana so ya saba da sabuwar ikilisiyar da ya je da ke da nisan kusan mil 900 daga garinsu.

Wataƙila kai ma kana tsoron ƙaura zuwa wata ikilisiya dabam. Mene ne zai taimaka maka ka saba da wurin? Mene ne za ka yi idan yana maka wuya ka saba da sabuwar ikilisiyar? Ban da haka, ta yaya za ka taimaka ma sababbi da suke ƙaurowa ikilisiyarku?

TA YAYA ZA KA SABA KUMA KA AMFANA?

Alal misali, idan aka tuge itatuwa zuwa wani wuri, hakan yakan shafe su. Ana tuge yawancin jijiyoyin itacen muddin aka tuge shi daga ƙasa don ya kasance da sauƙi a dasa shi a wani wuri. Itacen yakan soma kafa sabbin jijiyoyi da zarar an sake dasa shi. Hakazalika, wataƙila kana fuskantar wasu matsaloli don ka ƙaura zuwa wata ikilisiya. A ikilisiyar da ka baro kana da ‘jijiyoyi,’ wato abokanka, kuma kana jin daɗin bautarka ga Jehobah a wurin. Yanzu kana bukatar ka nemi sababbin abokai a wannan sabuwar ikilisiyar. Mene ne zai taimaka maka ka yi hakan? Ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Bari mu bincika wasu a cikinsu.

Mutumin da yake karanta Kalmar Allah a kai a kai yana “kamar itacen da aka dasa a magudanan ruwaye, wanda yana ba da ’ya’yansa a cikin kwanakinsa; ganyensa ba ya yi yaushi ba; kuma cikin iyakar abin da yake yi za shi yi albarka.”​Zab. 1:​1-3.

Kamar yadda itace zai yi girma sosai kuma ya kasance lafiyayye idan yana samun ruwa sosai, wajibi ne Kirista ya riƙa karanta Kalmar Allah don ya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Saboda haka, ka ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki kullum, kuma ka riƙa halarta taro a kai a kai. Kuma kana yin ibada ta iyali da kuma nazari na kanka. Kana bukatar ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kamar yadda kake yi a ikilisiyarku ta dā.

“Mai-ban ruwa shi kansa za a yi masa ban ruwa.”​Mis. 11:25.

Za ka sami ƙarfafa kuma ka saba da sabuwar ikilisiyar idan kana fita wa’azi sosai. Wani dattijo mai suna Kevin ya ce: “Abin da ya fi taimaka min da matata shi ne da zarar muka iso sabuwar ikilisiyarmu sai muka soma hidimar majagaba na ɗan lokaci. Hakan ya sa muka san ’yan’uwa da majagaba da kuma yankin nan da nan.” Roger wanda ya ƙaura zuwa wuri mai nisan mil 1,000 daga wurin da yake zama ya ce: “Hanya mafi kyau don saba da wata ikilisiya ita ce fita wa’azi a kai a kai. Kuma ka sa dattawa su san cewa za ka so ka taimaka da yin wani aiki, wataƙila share Majami’ar Mulki ko ba da jawabi idan wani bai shirya ba ko kuma kai wani ɗan’uwa taro a motarka. Idan ’yan’uwa suka ga wani sabon zuwa mai ƙwazo sosai, za su so su zama abokansa nan da nan.”

“Ku buɗe zuciyarku.”​2 Kor. 6:13.

Ku riƙa ƙaunar dukan ’yan’uwa ko daga ina suka fito. Bayan Melissa da iyalinta suka ƙaura zuwa wata ikilisiya, sai suka mai da hankali ga neman abokai. Ta ce: “Mukan yi cuɗanya da ’yan’uwa a Majami’ar Mulki kafin a soma taro da kuma bayan an gama  taro. Hakan yakan ba mu lokacin tattaunawa sosai.” Ƙari ga haka, wannan ya taimaka wa dukansu su san sunayen ’yan’uwan da sauri. Ban da haka ma, suna nuna wa ’yan’uwan karimci, kuma wannan ya ƙarfafa dangantakarsu. Ta daɗa cewa: “Mun karɓi lambar wayarsu su kuma suka karɓi namu, don mu riƙa kiran juna kuma muna aikin ikilisiya tare.”

Kana iya soma yin magana da mutanen da ba ka saba da su ba ta yin wasu abubuwa da ba su taka ƙara sun karya ba idan kana tsoron tattaunawa da mutane. Alal misali, ka riƙa murmushi ko da ba ka son yin hakan. Yin murmushi zai sa wasu su zo wurinka. Ballantana ma “fuska mai fara’a takan sa ka yi murna.” (Mis. 15:​30, Littafi Mai Tsarki.) Rachel wadda ta ƙaura da nesa daga wurin da ta girma ta ce: “Ni mai jin kunya ce sosai, a wasu lokatai nakan tilasta wa kaina in yi magana da ’yan’uwa a sabuwar ikilisiyar da na koma. Nakan nemi wanda ya zauna shi kaɗai a Majami’ar Mulki kuma in yi masa hira. Wataƙila wannan mutumin ma mai jin kunya ne yadda nake ji.” Ka kafa makasudin tattaunawa da wani sabon zuwa a taronku kafin a tashi daga taro da kuma bayan hakan.

A wani lokaci kuma, kana iya yin farin cikin haɗuwa da mutane a ’yan makonni na ƙaurowa zuwa ikilisiyar. Amma da shigewar lokaci, za ka saba da ’yan’uwan. A wannan lokacin, kana bukatar ka ci gaba da neman sabbin abokai.

Itatuwan da aka tuge sukan yi yaushi, amma da zarar an dasa su sukan soma kafa sabbin jijiyoyi

ZAI ƊAUKI LOKACI KAFIN KA SABA

Wasu itatuwa suna ɗaukan lokaci sosai kafin su kafu idan aka dasa su. Hakazalika, ba dukan mutane ba ne suke sabawa da sabuwar ikilisiya a lokaci ɗaya. Idan ka daɗe da zuwa wata ikilisiya kuma har ila kana fama don ka saba da ikilisiyar, za ka sami taimako idan ka bi waɗannan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki:

“Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.”​Gal. 6:9.

Kafin ka saba zai ɗauki lokaci fiye da yadda kake tsammani. Alal misali, masu wa’azi da yawa a ƙasar waje da suka je makarantar Gilead sukan yi shekaru da yawa a ƙasar da suke hidima kafin su kai ziyara ƙasarsu. Yin hakan yana taimaka musu su ƙulla dangantaka da ’yan’uwa da ke ƙasar da suke hidima kuma su saba da al’adarsu.

Alejandro da ya ƙaura sau da yawa ya san cewa yakan ɗauki lokaci kafin mutum ya saba da wurin da ya koma da zama. Ya ce: “Bayan da muka ƙaura, sai matata ta ce, ‘Dukan abokai na suna ikilisiyarmu ta dā!” Sai ya tuna mata cewa, haka ne ta faɗa bayan sun ƙaura shekara biyu da ta shige. Amma a cikin waɗannan shekarun, sai ta soma abokantaka da wasu, kuma suka zama abokai na kud da kud.

“Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanin dā suka fi na yanzu? Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.”​M. Wa. 7:10.

Ka daina kwatanta sabuwar ikilisiyarka da wanda kake a dā. Alal misali, wataƙila ’yan’uwan da suke sabuwar ikilisiyar ba sa yawan yin magana ko kuma masu surutu ne sosai, kai kuma ba ka saba da hakan ba. Don haka, zai dace ka mai da hankali ga abubuwa da suke yi masu kyau kamar yadda kai ma za ka so su riƙa mai da hankali ga halayenka masu kyau. Idan wasu ’yan’uwa suka koma wata ikilisiya, halin da suke nunawa yakan sa su tambayi kansu, ‘Shin da gaske ina ƙaunar ’yan’uwan da ke faɗin duniya?’​—1 Bit. 2:17.

 “Ku roƙa, za a ba ku.”​Luk 11:9.

Ka ci gaba da yin addu’a ga Jehobah ya taimaka maka. Wani dattijo mai suna David ya ce: “Kada ka ce za ka iya jimre kowane irin abu, Jehobah ne yake taimaka mana, don haka, ka yi masa addu’a game da batun.” Rachel wadda aka ambata ɗazu ta ce: “A duk lokacin da ni da mijina muka ga cewa ’yan’uwa a ikilisiya ba su damu da mu ba, muna addu’a ga Jehobah kuma mu roƙe shi ya taimaka mana mu san ko abin da muke yi ne yake sa ’yan’uwan suka guje mu. Bayan haka, sai mu nemi lokaci don mu riƙa hira ko ziyartar ’yan’uwanmu.”

Iyaye, idan yana yi wa yaranku wuya su saba da ’yan’uwan ikilisiyar da kuka koma, ku yi addu’a tare da su game da batun. Kuma kuna iya taimaka musu su sami abokai ta wurin gayyatar ’yan’uwa don ku shaƙata.

KA TAIMAKA WA SABABBI SU SĀKE JIKI

Mene ne za ka yi don ka taimaka ma waɗanda suka ƙauro ikilisiyarku? Ka yi ƙoƙari ka zama abokinsu. Don ka iya yin hakan, ka yi tunanin me za ka so a yi maka idan kai sabo ne a ikilisiyarku, sai ka yi musu hakan. (Mat. 7:12) Kana iya gayyatar waɗanda suka komo ikilisiyarku don ku yi ibada ta iyali tare ko kuma don ku kalli shirinmu a Tashar JW da ake yi kowane wata. Ban da haka ma, za ka iya gaya musu cewa za ka so ku fita wa’azi tare. Kuma idan ka gayyace su don ku ci abinci tare, ba za su taɓa mantawa da wannan gayyatar ba. Ban da abin da aka ambata, mene ne za ka iya yi don ka taimaka wa sababbi a ikilisiyarku?

Wani mai suna Carlos ya ce: “Wata ’yar’uwa ta nuna mana wuraren da ake sayar da abubuwa da araha, kuma hakan ya taimaka mana sosai.” ’Yan’uwan da suka zo daga wurin da yanayin ya bambanta da naku, za su ji daɗi idan kuka nuna musu irin kayan da kuke sakawa a a lokacin sanyi ko zafi ko kuma idan ana yawan yin ruwan sama. Ban da haka ma, za ka iya taimaka musu su iya yin wa’azi sosai a wurin, idan kuka gaya musu labarin garin ko kuma idan kuka bayyana musu abin da mutanen wurin suka yi imani da shi.

IDAN MUKA YI ƘOƘARI, ZA MU YI NASARA

Allen, wanda aka ambata ɗazu ya yi shekara ɗaya yanzu a ikilisiyar da ya koma. Ya ce: “Na yi ƙoƙari sosai don in san ’yan’uwan da ke ikilisiyar. Kuma yanzu sun zama kamar iyalina, hakan yana sa ni farin ciki.” Allen ya fahimci cewa komawa wata ikilisiya bai sa ya yi rashin abokansa ba, amma ya sami wasu sababbin abokai da za su ci gaba da abokantaka muddar ransu.

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunayen.