“Ubangiji yana fansar ran bayinsa; a cikin masu-dogara gare shi ba za a kada ko ɗaya ba.”​—ZAB. 34:22.

WAƘOƘI: 8, 54

1. Yaya bayin Allah masu aminci suke yawan ji domin zunubin da suka gāda?

“KAITONA, ga ni mutum, abin tausayi!” (Rom. 7:24) Bayin Allah da yawa sun maimaita wannan furuci da manzo Bulus ya yi. Dukanmu muna shan wahala don zunubi da muka gada, kuma muna iya yin baƙin ciki sosai idan ayyukanmu ba su nuna cewa muna son mu faranta wa Jehobah rai ba. Wasu Kiristoci da suka yi zunubi mai tsanani sun ji cewa Allah ba zai taɓa gafarta musu ba.

2. (a) Ta yaya Zabura 34:22 ta nuna cewa bai kamata bayin Allah su riƙa baƙin ciki ainun don zunubinsu ba? (b) Mene ne za a bincika a wannan talifin? (Ka duba akwatin nan “ Darussa ko Abin da Wasu Labaran Littafi Mai Tsarki Suke Wakilta?”)

2 Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa waɗanda suka nemi mafaka a wurin Jehobah ba sa bukatar su yi baƙin ciki ainun don zunubin da suka yi. (Karanta Zabura 34:22.) Mene ne neman mafaka a wurin Jehobah ya ƙunsa? Waɗanne abubuwa ne za mu yi don Jehobah ya nuna mana jin ƙai kuma ya gafarta mana? Za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyi ta wurin bincika yadda aka tsara biranen mafaka a Isra’ila ta dā. Hakika, an kafa wannan tsarin sa’ad da ake bin Dokar  alkawari, wadda aka canja a ranar Fentakos na shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu. Amma Jehobah ne ya kafa wannan Dokar. Saboda haka, ta wurin tsara biranen mafaka, mun san ra’ayin Jehobah game da zunubi da masu zunubi da kuma tuba. Amma za mu fara tattauna abin da ya sa aka kafa waɗannan birane da kuma amfaninsu.

“KU SANYA BIRANEN MAFAKA”

3. Ta yaya Isra’ilawa suka bi da batun yin kisa?

3 Jehobah ba ya wasa da batun yin kisa a Isra’ila ta dā. Dangi na kusa na wanda aka kashe, wato mai ramako zai je ya kashe wanda ya yi kisan. (Lit. Lis. 35:19) Ɗaukan wannan matakin zai sa a rama ma wanda aka kashe ba gaira ba dalili. Yin hukunci nan da nan zai sa kada a ƙazantar da Ƙasar Alkawari, shi ya sa Jehobah ya ba da wannan umurni: “Ba za ku tozartar da ƙasa inda kuke zaune: gama [zubar da] jini yakan tozartar da ƙasa.”​—Lit. Lis. 35:​33, 34.

4. Ta yaya Isra’ilawa a dā suke bi da wanda ya kashe wani ba da gangan ba a Isra’ila?

4 Amma ta yaya Isra’ilawa suka bi da batun kisan kai da mutum ya yi ba da saninsa ba? Har ila mutumin yana da alhakin kashe mutum ko da ya yi hakan ba da saninsa ba. (Far. 9:5) Amma don a nuna masa jin ƙai, zai gudu daga wurin mai yin ramako zuwa ɗaya cikin biranen mafaka guda shida da ake da su. Babu wanda zai taɓa shi a cikin birnin, kuma zai zauna a ciki har sai babban firist ɗin ya mutu.​—Lit. Lis. 35:​15, 28.

5. Ta yaya shirin biranen mafaka ya taimaka mana mu fahimci Jehobah sosai?

5 Jehobah ne ya fito da wannan ra’ayin biranen mafaka, don ya ba Joshua umurni cewa: “Ka yi magana da ’ya’yan Isra’ila, ka ce, Ku sanya biranen mafaka.” An ɗauka waɗannan biranen a matsayin wurare masu tsarki. (Josh. 20:​1, 2, 7, 8) Tun da Jehobah ne ya keɓe waɗannan biranen don yin wani abu na musamman, muna iya tambaya: Ta yaya hakan ya taimaka mini in ga dalla-dalla cewa Jehobah mai jin ƙai ne? Kuma mene ne ya koya mana game da yadda za mu nemi mafaka a wurinsa?

“ZA YA . . . BAYYANA DA’AWARSA A CIKIN KUNNUWAN DATIƁAN”

6, 7. (a) Ka bayyana aikin dattawa sa’ad da suke yi wa wanda ya kashe mutum ba da saninsa ba shari’a. (Ka duba hoton da ke shafi na 8.) (b) Me ya sa ya dace mai gudun hijira ya je wurin dattawa?

6 Idan mutum ya kashe wani ba da saninsa, zai “bayana da’awarsa a cikin kunnuwan datiɓan” a ƙofar birnin mafakar da ya je. Za a marabce shi sosai a wurin. (Josh. 20:4) Bayan wani lokaci, za a tura shi zuwa wurin dattawan birnin da ya yi kisan, kuma su yi shari’ar. (Karanta Littafin Lissafi 35:​24, 25.) Sai bayan sun ga ba shi da laifi ne za a mai da shi birnin mafakan.

7 Me ya sa zai je wurin dattawa? Don dattawan suna bukatar su sa ikilisiyar Isra’ila ta kasance da tsabta kuma a taimaka ma wanda ya kashe mutum ba da saninsa ya amfana daga jin kan Jehobah. Wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya rubuta cewa “kasada ce ga mutumin” idan ya ƙi zuwa wurin dattawa. Ya daɗa cewa: “Jininsa yana kansa, domin bai yi amfani da tanadin tsaro da Allah ya yi masa ba.” Za a taimaka ma wanda ya yi kisan ba da saninsa ba, amma shi ne zai nemi taimakon. Idan bai gudu zuwa cikin ɗaya daga cikin biranen da Jehobah ya keɓe ba, dangin wanda ya kashe zai kashe shi.

8, 9. Me ya sa Kirista da ya yi zunubi sosai zai nemi taimakon dattawa?

8 A yau, Kirista wanda ya yi zunubi yana bukatar ya nemi taimakon dattawa don ya farfaɗo. Me ya sa hakan yake da  muhimmanci? Na farko, don Jehobah ne ya ce dattawa su riƙa yin shari’ar masu zunubi, kamar yadda aka faɗa a cikin Kalmarsa. (Yaƙ. 5:​14-16) Na biyu, wannan shirin yana sa Allah ya ci gaba da ƙaunar wanda ya yi laifi da ya tuba kuma ya guji ci gaba da zunubin. (Gal. 6:1; Ibran. 12:11) Na uku, an ba dattawa umurni kuma an horar da su su ƙarfafa masu zunubi da suka tuba, don hakan zai sauƙaƙa baƙin ciki da alhakin da suke yi. Jehobah ya kira waɗannan dattawan “maɓoya daga iska.” (Isha. 32:​1, 2) Babu shakka, wannan shirin ya nuna cewa Allah mai jin ƙai ne!

9 Bayin Allah da yawa sun gano cewa mutum yana samun sauƙi idan ya nemi taimakon dattawa. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Daniel ya yi zunubi sosai, amma ya yi watanni da yawa yana jinkirin zuwa wurin dattawa. Ya ce: “Bayan wani dogon lokaci, na yi tunani cewa dattawa ba za su iya taimaka mini kuma ba. Duk da haka, ina damuwa cewa zan fuskanci sakamakon ayyukana. Kuma sa’ad da na yi addu’a ga Jehobah, sai na soma jin cewa ya kamata in soma kowace addu’a da neman gafara.” Daga baya, Daniel ya nemi taimakon dattawa. Sa’ad da ya yi tunanin abin da ya faru, ya ce: “A gaskiya, na ji tsoron zuwa wurin dattawa. Amma bayan da na yi hakan, sai na ji kamar na sauke babban kaya daga kaina. Yanzu ba abin da zai hana ni yin addu’a ga Jehobah.” Ba abin da ke damun Daniel a yau, kuma bai daɗe ba da aka naɗa shi bawa mai hidima a ikilisiya.

ZAI “GUDU ZUWA ƊAYAN BIRANEN NAN”

10. Wane mataki mai kyau ne wanda ya yi kisa zai ɗauka don a nuna masa jin ƙai?

10 Wanda ya kashe mutum ba da saninsa ba zai ɗauki mataki don a nuna masa jin ƙai. Zai gudu zuwa birnin mafaka da ya fi kusa. (Karanta Joshua 20:4.) Mutumin ba zai ci musun yin hakan ba don za a kashe shi idan bai isa birnin mafaka nan da nan kuma ya ci gaba da zama a wurin ba. Kuma hakan yana nufin cewa zai yi hasarar wasu abubuwa. Zai bar aikin da yake yi a dā da gidansa, kuma ba zai riƙa yawo yadda ya ga dama ba har sai babban firist  ɗin ya rasu. * (Lit. Lis. 35:25) Amma yin waɗannan abubuwan sun dace, don idan ya ci gaba da zama a birnin da ya yi kisan, ba zai ga munin laifin da ya yi ba, kuma za a iya kashe shi.

11. Waɗanne ayyuka ne za su nuna cewa Kirista da ya tuba yana godiya don yadda Allah yake nuna mana jin ƙai?

11 Wajibi ne waɗanda suka yi zunubi da suka tuba a yau su ɗauki wani mataki don su amfana daga jin kan Allah. Dole ne mu guji yin zunubi gabaki ɗaya. Zai dace mu daina wani zunubi da wasu abubuwan da muke gani ba wani abu ba ne da za su iya sa mu yi zunubai masu tsanani. An hure manzo Bulus ya faɗi ayyukan Kiristoci da suka tuba a Koranti. Ya ce: “Ɓacin zuciya da aka yi muku irin da Allah ke sa, duba irin ƙaifin hankali da ya aika a wurinku, i, duba, wace irin ƙariyar kai, i, wane irin haushi, i, wane irin tsoro, i, wane irin bege, i, wace irin himma, i, wace irin ɗaukar fansa.” (2 Kor. 7:​10, 11) Yin iya ƙoƙarinmu don mu daina wani zunubi yana nuna wa Jehobah cewa mun damu da yanayinmu, kuma ba ma jin cewa zai gafarta mana haka kawai ba tare da mun ɗauki wani mataki ba.

12. Mene ne Kirista yake bukatar ya daina idan yana son Allah ya ci gaba da nuna masa jin ƙai?

12 Waɗanne abubuwa ne ya kamata Kirista ya daina don Allah ya ci gaba da nuna masa jin ƙai? Wajibi ne ya daina wasu abubuwan da yake so idan za su sa ya yi zunubi. (Mat. 18:​8, 9) Idan wasu abokanka suna sa ka yi abubuwan da ba sa faranta wa Jehobah rai, zai dace ka daina tarayya da su. Idan kana fama da shan giya, shin kana shirye ka guji yanayi da zai sa ka shan giya da yawa? Idan kana fama da sha’awar yin lalata, shin kana guje wa fina-finai da dandalin intane ko kuma ayyuka da za su sa ka soma wannan banzan tunanin? Ka tuna cewa za mu amfana idan muka yi duk wata sadaukarwa da za ta taimaka mana mu riƙe amincinmu ga Jehobah. Ganin cewa Jehobah ya yashe mu ne zai fi sa mu baƙin ciki a rayuwa. Ƙari ga haka, za mu samu gamsuwa sosai idan muna samun ‘madawwamin alherinsa.’​—Isha. 54:​7, 8.

“ZA SU ZAMA MUKU MAFAKA”

13. Ka bayyana abin da ya sa wanda ya yi kisa zai samu kwanciyar hankali kuma ya yi farin ciki a birnin mafaka.

13 Babu abin da zai sami wanda ya yi kisan muddin yana cikin birnin mafakan. Jehobah ya ce game da waɗannan biranen: “Za su zama muku mafaka.” (Josh. 20:​2, 3) Jehobah ba ya bukatar a sake yi ma wanda ya yi kisan shari’a a kan wannan batun, ko kuma a ƙyale mai ramako ya shiga cikin birnin ya kashe shi. Saboda haka, wanda ya yi kisa ba zai ji tsoro cewa za a kawo masa hari ba. Amma, yayin da yake cikin birnin ba abin da zai same shi don Jehobah yana kāre shi. Ba wai yana zaman fursuna ne a birnin mafakan ba. Don a cikin birnin an ba shi damar yin aiki kuma zai iya taimaka ma wasu. Ban da haka ma, zai bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Hakika, zai yi farin ciki kuma ya samu kwanciyar hankali!

Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta maka zunubanka (Ka duba sakin layi na 14-16)

14. Wane tabbaci ne Kirista da ya tuba yake da shi?

14 Wasu mutanen Allah da suka yi zunubi sosai amma sun tuba har ila suna gani suna cikin fursuna don abin da suka yi. Ƙari ga haka, suna jin cewa Jehobah zai riƙa yi musu kallon masu zunubi har abada. Idan kana jin hakan, ka kasance da tabbaci cewa kana da kwanciyar hankali don Jehobah ya riga ya gafarta maka. Daniel da aka ambata ɗazu ya ce hakan gaskiya ne, don bayan da dattawa suka yi masa gyara kuma suka taimaka masa, sai ya ce: “Sai na ji na sami kwanciyar  hankali kuma. Bayan an yi shari’ar, ba na ganin ina da alhaki kuma. Da zarar Jehobah ya gafarta maka, yana share zunubin. Kuma kamar yadda Jehobah ya faɗa, yakan ɗauki zunubinka kuma ya ajiye shi da nesa. Ba za ka ƙara ganinsa ba.” Muddin wanda ya yi kisa yana cikin birnin mafaka, ba zai ƙara jin tsoron mai ramako ba. Hakazalika, muddin Jehobah ya gafarta mana zunubinmu, ba ma bukatar mu ji tsoron cewa zai ta da batun wata rana ko kuma ya yi mana shari’a a kan batun.​—Karanta Zabura 103:​8-12.

15, 16. Ta yaya matsayin Yesu na Mai Fansa da Babban Firist ya sa ka kasance da tabbaci cewa Allah zai nuna maka jin ƙai?

15 Muna da dalili mai kyau na kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai nuna mana jin ƙai fiye da yadda ya nuna wa Isra’ilawa. Bayan da Bulus ya nuna baƙin cikinsa don ba ya yin nufin Jehobah yadda yake so, sai ya ce: “Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Rom. 7:25) Hakika, duk da yadda Bulus ya yi fama da zunubi da kuma abin da ya yi a dā, ko da yake ya tuba, Bulus yana da tabbaci cewa Allah zai gafarta masa ta wurin Yesu. Da yake Yesu ne ya fanshe mu daga zunubi, ya share zunubanmu kuma ya sa mu kasance da kwanciyar hankali. (Ibran. 9:​13, 14) Ƙari ga haka, tun da shi ne Babban Firist, “yana da iko ya yiwo ceto ba iyaka domin waɗanda ke kusantuwa ga Allah ta wurinsa, da shi ke kullum a raye yake domin yin roƙo sabili da su.” (Ibran. 7:​24, 25) Idan aikin babban firist shi ne ya sa Isra’ilawa su kasance da tabbaci cewa za a gafarta musu zunubansu, ya kamata ayyukan Yesu Babban Firist su tabbatar mana cewa za “a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.”​—Ibran. 4:​15, 16, Littafi Mai Tsarki.

16 Saboda haka, don ka sami mafaka a wurin Jehobah, wajibi ne ka kasance da bangaskiya ga hadayar Yesu. Kada ka riƙa faɗa da baki kawai cewa fansar ta taimaka wa mutane da yawa. Maimakon haka, ka kasance da bangaskiya cewa ka amfana ta wurin fansar. (Gal. 2:​20, 21) Ƙari ga haka, ka ba da gaskiya cewa ta wurin fansa ce ake gafarta maka zunubanka. Kuma ka gaskata cewa ta wurin fansa ce za ka sami rai madawwami. Hadayar da Yesu ya ba da ce kyautar da Jehobah ya ba ka.

17. Me ya sa kake so ka sami mafaka a wurin Jehobah?

17 Biranen mafaka na Isra’ila ta dā sun nuna cewa Jehobah mai jin ƙai ne. Ta wurin yin tanadin waɗannan biranen, Allah ya nuna cewa rai yana da muhimmanci a gare shi kuma sun nuna yadda dattawa suke taimaka mana. Ƙari ga haka, mun koyi yadda mutum zai tuba da gaske da kuma dalilin da ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai gafarta mana zunubanmu. Shin kana neman mafaka a wurin Jehobah? A wurinsa ne za ka sami kwanciyar hankali! (Zab. 91:​1, 2) A talifi na gaba, za mu bincika yadda biranen mafaka za su iya taimaka mana mu bi misalin Jehobah na nuna adalci da kuma jin ƙai.

^ sakin layi na 10 Wani littafin bincike na Yahudawa ya ce iyalin wanda ya yi kisan sukan bi shi zuwa birnin mafakan.