BAYIN ALLAH a dā sun ba da hadaya kuma yin haka yana da muhimmanci sosai. Isra’ilawa sun ba da hadayar dabbobi, kuma an san Kiristoci da ba da “hadaya ta yabo.” Amma akwai wasu hadayu ma da ke faranta wa Allah rai. (Ibran. 13:​15, 16) Waɗannan hadayun suna sa mutane farin ciki kuma suna sa su samu albarka sosai, kamar yadda misalan da za mu gani suka nuna.

Wata baiwar Allah mai suna Hannatu tana so ta haihu, amma ba ta iya yin hakan ba. Sai ta yi wa Jehobah addu’a kuma ta yi alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta “ba da shi ga Ubangiji muddar ransa.” (1 Sam. 1:​10, 11) Da shigewar lokaci, Hannatu ta yi juna biyu kuma ta haifi ɗa, ta sa masa suna Sama’ila. Bayan da Hannatu ta yaye Sama’ila, sai ta kai shi mazauni don ta cika alkawarin da ta yi. Jehobah ya albarkaci Hannatu don abin da ta yi. Kuma ta ƙara haifan yara biyar, ban da haka ma, Sama’ila ya zama annabi da kuma marubucin wasu littattafai a Littafi Mai Tsarki.​—1 Sam. 2:21.

Kamar abin da Hannatu da Sama’ila suka yi, Kiristoci a yau suna da damar yin amfani da rayuwarsu don su yi wa Mahaliccinsu hidima. Ban da haka ma, Yesu ya yi alkawarin cewa za mu sami albarka sosai a duk wata sadaukarwa da muka yi a bautarmu ga Jehobah.​—Mar. 10:​28-30.

A ƙarni na farko, akwai wata mata mai suna Dokas da mutane suka san ta da “ayyukan nagarta da bayebayen” da take yi don ta taimaka ma wasu. Amma abin tausayi shi ne, “ta yi ciwo, ta mutu” kuma hakan ya sa ikilisiyar da take baƙin ciki sosai. Da ’yan’uwan suka ji cewa Bitrus yana yankinsu, sai suka kirawo shi. Babu shakka, sun yi farin ciki sosai da Bitrus ya zo ya ta da Dokas, kuma shi ne manzo na farko da ya ta da wani daga mutuwa. (A. M. 9:​36-41) Hakika, Allah bai manta da ayyukan da Dokas ta yi ba. (Ibran. 6:10) Kuma an rubuta labarin alherin da ta yi a Littafi Mai Tsarki don bayin Allah su yi koyi da halinta mai kyau.

Manzo Bulus ma ya kafa misali mai kyau na ba da lokacinsa da kuma taimaka wa mutane. Sa’ad da yake rubuta wa ’yan’uwan da ke Korinti wasiƙa ya ce: “Ni ma da farin ciki sarai na yarda in batar har kuwa a batar da ni sabili da rayukanku.” (2 Kor. 12:15) Bulus ya fahimci cewa yin sadaukarwa don wasu yana sa mutum farin ciki kuma yana sa Jehobah ya yi mana albarka. Ƙari ga haka, zai amince da shi.​—A. M. 20:​24, 35.

Babu shakka, idan muna amfani da lokacinmu don mu tallafa wa ƙungiyar Jehobah ko kuma taimaka wa ’yan’uwanmu, hakan yana faranta wa Jehobah rai. Ƙari ga abin da aka ambata, akwai wasu hanyoyin da za mu tallafa ma wa’azin da ake yi game da Mulkin Allah? E! Ban da ayyukan da muke yi, za mu iya nuna godiya ta wajen ba da gudummawa. Ana amfani da gudummawar ne don a tallafa wa ’yan’uwan da ke wa’azi a wata ƙasa da kuma wasu da ke hidima ta cikakken lokaci na musamman. Ban da haka ma, ana amfani da gudummawar don fassara littattafai da bidiyoyi da taimaka wa ’yan’uwa da bala’i ya auko musu. Ƙari ga haka, ana yin amfani da shi don a gina Majami’un Mulki da kuma kula da su. Muna bukatar mu kasance da tabbacin cewa “mai-alheri za ya sami albarka.” Ƙari ga haka, ba da gudummawa yana nuna cewa muna daraja Jehobah sosai.​—Mis. 3:9; 22:9.